Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Muna nan muna bincike kan sabuwar cutar da ta bulla a Zamfara - Gwamnati
Gwamnatin jihar Zamfara ta ce tana bin dukkan matakan da suka kamata, domin gano da kuma dakile yaduwar wata cuta da ta bulla, wadda ba a kai ga tantance ko wacce iri ce ba.
Gwamnatin jihar ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
Mai magana da yawun gwamnan jihar ta Zamfara Sulaiman Bala Idris,ya shaida wa BBC cewa, yanzu gwamnati na son a fahimci cewa wacce irin cuta ce? da kuma fara killace wadanda suka kamu da cutar saboda gudun yaduwarta.
Ya ce,”Idan mutane suka ga wata bakuwar cuta wadda ba a santa ba ya kamata su je asibiti domin a gwada jinin mutum aga wacce iri ce, domin idan mutane ba su je asibiti ba, ba za a iya sanin abin da ke faruwa bah ar sai cutar ta yadu.”
Wasu rahotanni sun ce akalla mutane da dama ne suka kamu da wannan cuta, to amma gwamnatin jihar ta musanta adadin tana mai cewa sai na kammala bincike sannan za a gano ko mutum nawa ne suka kamu da cutar da kuma wadanda suka mutu sakamakonta.
Sulaiman Bala Idris, ya ce a yanzu hukumomin lafiya na nan na sun dukufa domin gano wacce irin cuta ce sannan kuma a samar da maganinta.
Kazalika gwamnati ta kuma dauki matakin killace wadanda suka kamu da cutar don dakile yaduwarta.