Shin ‘yan majalisa sun dawo rakiyar gwamnatin Tinubu ne?

Majalisar dokokin Najeriya

Asalin hoton, NASS

    • Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
  • Lokacin karatu: Minti 3

A cikin makon nan ne majalisar wakilan Najeriya ta yi kira ga gwamnatin ƙasar ta gaggauta janye ƙarin farashin mai da na tukunyar gas.

Tun bayan da kamfanin NNPCL ya sanar da ƙarin farashin mai, sau biyu a cikin wata guda, al'amura suka ƙara dagulewa a Najeriya tare da jefa ƴanƙasar cikin wani yanayi na wahala da tsadar rayuwa.

Ƙarin na kimanin kaso 15 ya zo ne bayan bayanai da suka nuna NNPCL ya zare hannunsa daga dillancin fetur tsakanin matatar mai ta Ɗangote da 'yankasuwa.

A yanzu dai ana sayar da man fetur ne a kan sama da naira 1,000 a sassan Najeriya yayin da kowane kilo na iskar gas kuma ake sayar da shi kan naira 1,500.

A ƙudirin da ya gabatar wanda ya samu goyon bayan ƴanmajalisa 111, mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar, Aliyu Madaki, ya ce suna fargabar ƙarin na ƙara sanya al'umma cikin ƙangin talauci da kuma barazana ga samun ayyukan yi.

Wannan dai na zuwa ne yayin da Bankin Duniya ke gargaɗin cewa ƙara farashin man fetur a Najeriya na iya mayar da hannun agogo baya game da tasirin cire tallafin mai a ƙasar.

Shin me wannan kira na majalisar wakilan Najeriya ke nufi? Wace gudunmawa hakan zai bayar wajen rage wa talaka raɗaɗi?

Kan haka ne BBC ta tattauna da masana masu sharhi kan al'amuran yau da kullum domin jin abin da suka fahimta game da kiran na majalisar.

Me kiran ƴan majalisar ke nufi?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Farfesa Abubakar Kari masanin kimiyyar siyasa kuma malami a jami'ar Abuja ya shaida wa BBC cewa kiran na ƴanmajalisar na kan gaɓa kuma ya yi daidai da ra'ayin galibin al'ummar ƙasar.

A cewarsa, kiran nasu na nuna irin damuwar da suka yi da halin da ƴan ƙasar suke ciki ganin cewa al'umma na cikin matsi da uƙuba na yawan ƙara kuɗin mai da ake yi a Najeriya.

"Abin da yake faruwa shi ne al'umma za su dawo daga rakiyarsu, suna jin tsoron su kansu suna cikin haɗari idan ba su fito sun yi irin wannan ba." in ji Farfesa Kari.

Masanin ya ƙara da cewa a dimokraɗiyyance "wannan kira nasu zai zamo wani babban matsi da gwamnati za ta samu."

"Ko ba ta aiwatar da kiran nasu ba to dole ne gwamnati za ta san cewa wakilai da sauran jama'a suna nuna damuwa." kamar yadda ya ce.

Ya kuma ƙara da cewar idan har gwamnati da gaske take ya kamata a ce gwamnati ta yi wani abu game da kira-kirayen da ake yi na sassauta wa al'umma da kuma gyara manufofinta da ke jefa al'umma cikin wani mummunan yanayi.

Ya ce halin da ake ciki a Najeriya, abu ne da ya shafi kowa da kowa shi ya sa "masu faɗa a ji da ƙungiyoyi da shugabanni da sarakuna suke fitowa suke yi wa gwamnati hannunka mai sanda."

A cewarsa, suna haka ne domin nuna wa gwamnati buƙatar ta yi wani abu domin sauƙaƙa wa jama'a.

Masanin ya ce kiraye-kirayen ba wai suna nuna sun dawo daga rakiyar gwamnati bane illa dai suna nuna "matuƙar damuwa da ɓacin rai kan yadda al'amura suka taɓarɓare."

Ana yawan zargin ƴanmajalisar da rashin yin kataɓus "ko ma sun sa ido abubuwa sun lalace a ƙasa duk da suna da damar yin hakan ba sa yi."

"Idan tafiyar ta ci gaba a haka musamman Tinubu da muƙarrabansa suka ƙi amfani da kiran ƴanmajalisar, babu mamaki sannu a hankali a raba gari da aƙalla wasu daga cikinsu." in ji masanin.

Yaushe farashin mai zai daina hauhawa?

"Ba a taɓa yin haka ba a duniya kuma ba za a fara daga Najeriya ba. Farashi ba zai daina tashi ba. Da ma shi cire tallafi ya gaji haka domin yanzu farashin zai dogara ne ga yadda kasuwa ta kama musamman ma farashin dala." In ji Dakta Ahmed Adamu, malami a jami'ar Nile University kuma masanin harkar makamashi a Abuja Najeriya.

Dakta Ahmed ya ƙara da cewa "duk kuwa da cewa yanzu gwamnati za ta rinƙa sayar wa da Ɗangote ɗanyen man a naira to amma ita kanta naira ɗin ai sai an canza dalar saboda darajar naira ta dogara ne ga dalar Amurka.

Saboda haka darajar naira ce abin dubawa. Idan naira ta karye to farashin mai dole ne ya tashi.

''Sannan akwai batun dakon man da kuma kai shi wuri mai nisa. Duka waɗannan abubuwan dubawa ne da za su iya haddasa hawa da saukar farashin na mai,'' in ji masanin.