Wannan cin zarafin ne ga ƴan faransa - Lloris

Tsohon kyaftin ɗin Faransa Hugo Lloris ya bayyana waƙar da wasu ƴan wasan tawagar Argentina suka rera da cewa wani lamari ne na ci zarafi ga Faransawa, amma yana fatan ƴan wasan da abin ya shafa zu koyi darasi daga kuskuren da suka yi.

Ɗan wasan tsakiya na Chelsea Enzo Fernandez na fuskantar tahuma daga kulob ɗin na Premier bayan ya wallafa wani bidiyo a shafukan sada zumunta wanda hukumar ƙwallon ƙafa ta Faransa ta ce yana ɗauke da kalaman da ke nuna ƙyama da kuma wariyar launin fata.

Ita ma Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya Fifa ta na gudanar da bincike kan bidiyon, inda ƴan wasan Argentina da dama da ke murnar nasarar da suka samu kan Colombia da ci 1-0 a wasan ƙarshe na gasar Copa America - suka fara rera wata waƙa inda suke shaguɓe ga baƙaƙen fatar da ke wasa a tawagar ƙwallon ƙafar Faransa.

Lloris, wanda shi ne ɗan wasan da ya fi bugawa Faransa wasa kuma kyaftin dinsu a lokacin da suka lashe gasar cin kofin duniya ta 2018, ya bayyana kaɗuwarsa kan halin na ƴan wasan Argentina.

Ya ce: “Ba ka son ji ko ganin irin wannan lamarin a harkar ƙwallon ƙafa, dukkanmu mun yi adawa da kowace irin wariya, musamman wariyar launin fata.

"Ni dai ina fatan kuskure ne, dukkanmu muna yin kuskure wani lokaci kuma da fatan za su dauki darasi daga wannan lamarin."

Tsohon kyaftin ɗin Tottenham, Lloris, mai shekara 37, ya rattaba hannu a kulob ɗin Los Angeles FC da ke fafatawa a gasar Major League Soccer ta Amurka a watan Disamba kuma ya kasance a Amurka yayin da Argentina ta lashe kofin Copa America a birnin Miami.