Ƴar Afghanistan da aka yi wa auren wuri ta lashe gasar motsa jikin zama ƙarti

Roya Karimi in her gym, looking at camera
Bayanan hoto, Roya ta tattauna da sashen Afghanistan na BBC daga gidanta da kuma wurin motsa jiki kan jajircewarta na wayar da kai kan halin da matan Afghanistan ke ciki.
    • Marubuci, Mahjooba Nowrouzi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Afghan
  • Lokacin karatu: Minti 6

A baya Roya Karimi ta kasance wadda aka yi wa auren wuri a Afghanistan, kuma ta haihu tana da shekara 15 a duniya, amma a yanzu ta zama daya daga cikin shahararrun masu motsa jiki don zama ƙarti a Turai.

A yanzu da ta shiga gasar masu motsa jiki don zama ƙarti ta duniya, rayuwarta ta kasance abin nuni ga yadda za a iya yaƙar tsauraran al'adu, ta kuma sake gina kanta, tare da zama abin koyi ga matan da ke fuskantar matsi da takura.

Roya ta gudu daga Afghanistan shekaru 14 da su ka gabata tare da mahaifiyarta da ɗanta, suka nemi mafaka a Norway.

Duk da sabuwar rayuwarta ta kai ta ga samun nasarori kamar shiga gasar masu motsa jiki domin zama ƙarti ta duniya lokacin tana da shekara 30, har yanzu Roya na damuwa game da ƴancin sauran matan da suka rage a ƙasar.

Ta fi damuwa ne game da takunkuman da aka sanya wa matan Afghanistan tun bayan da ƴan Taliban suka dawo mulki a 2021.

''Duk lokacin da na je wurin motsa jiki, sai in tuno cewa akwai wani lokaci da nake Afghanistan da ba ni da damar motsa jikina,'' Roya ta shaida wa sashen Afghanistan na BBC.

"Na yi sa'ar fita daga cikin wannan yanayin, amma har yanzu ana tauye wa mata da yawa ƴancinsu a matsayin su na bil'adama, kamar ilimi. Lamarin ba shi da daɗi kuma ya na karya zuciya.''

Roya na magana ne kan haramta wa ƴanmatan da suka kai shekara 12 zuwa makaranta da gwamnatin Taliban ta yi.

Roya Karimi's son NAME (left), Roya holding a trophy while wearing a sparky outfit, and her husband, Kamal Jalaluddin
Bayanan hoto, Roya Karimi da maigidanta Kamal Jalaluddin bayan ta lashe gasar masu motsa jiki domin zama ƙarti mai suna 'NAME IT'

Labarin nuna turjiya

Roya na ganin bayar da labarin turjiyar, shi kanshi wata gwagwarmaya ce.

"A halin da muke ciki yanzu, an rufe wa yara mata ƴan Afghanistan bakunansu zuwa matakin da ba sa ma iya zuwa makaranta. Ba za su iya fita gida ba ba tare da rakiyar namiji ba, ballanta na ma a zo maganar daukar mataki wa kansu, ko su samu yancin yin tunani, ko bayyana ra'ayinsu, ko yin soyayya ko kuma ma yin rayuwa."

Ƴan Taliban ɗin sun sanya tsauraran takunkumai kan mata da ƴanmata, bayan karɓe iko daga gwamnatin da ke da goyon bayan ƙasashen yamma bayan sojojin Amurka sun janye ana tsaka da rikici a 2021.

''Ina fatan ganin ranar da mata ƴan Afghanistan za su yi rayuwa ba tare da fargaba ba, su kuma cimma burukansu,'' in ji Roya.

Women with faces covered sit on the floor and study scriptures
Bayanan hoto, Mata a Afghanisatan na iya karatun addini a islamiyoyi, amma ƴan Taliban ɗin sun hana matan zuwa makaranta domin koyon sauran darussa idan sun kai shekara 12.

Tafiya zuwa Norway

Roya ta bayyana cewa 'ba ta son wannan rayuwar'' tun ma kafin Taliban su dawo kan mulki a ƙasar.

Hukuncin da ta yanke na barin Afghanistan, tare da barin mijinta, zai zama cike da kasada da barazana ga matan da ke Afghanisatan idan za su yi hakan.

A Norway, Roya ta tsinci kanta a wani wuri da ke da banbanci sosai da inda ta fito.

Dole sai da ta yi ƙokarin sauya rayuwarta, ta nemi aiki domin tallafa wa kanta da iyalinta, ta kuma koyi yaren ƙasar.

Ya kasance abu mai wahala gare ta yin duka waɗanan abubuwa a tare a lokacin da ta fara, amma jajircewarta ya kai ta ga nasara.

Roya ta karanci ilimin jinya kuma ta yi aiki a wani asibiti da ke Oslo, babban birnin ƙasar.

Koyon motsa jiki domin zama ƙarti

Roya Karimi sitting in an exercise machine
Bayanan hoto, Roya ta soma koyon motsa jiki domin zama ƙarti shekaru 14 da su ka gabata.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Fara koyon motsa jiki domin zama ƙarti shi ne babban abin da ya sauya rayuwar Roya.

Zuwa wuraren motsa jiki ba wai kawai domin motsa jikinta ba ne, yin hakan ya zama wata hanya ta sake ƙarfafa wa kanta gwiwa da kuma sake gina kanta.

Bayan aikin da ta ke yi a matsayin ma'aikaciyar jinya, Roya ta ci gaba da karatu a fannin horaswa kan lafiya da cin abinci mai gina jiki, har ta samu shaidar digiri a harkar motsa jiki.

A yanzu Roya da mijinta na biyu sun kasance ma'aurata na farko masu motsa jiki domin zama ƙarti daga Afghanistan, wani abu da ke nuna jajircewa da kuma sauyi.

A shekarar da ta gabata, Roya ta yanke hukuncin barin aikin jinya tare da shiga duniyar motsa jiki gadan-gadan. Wani mataki mai muhimmanci da ya sauya akalar rayuwarta.

Sai dai ta ce ba sauya aiki ba ne abin da ya fi zama kalubale a gare ta, sauya rayuwarta zuwa rayuwa ta ƴanci bayan matsi da takurar da ta fuskanta a Afghanistan ne babban kalubalen.

"Babban kalubalenmu shi ne rabuwa da iyakoki da tsare-tsaren da wasu suka gindaya mana, dokokin da aka sanya mana da sunan al'ada ko addini, '' in ji ta.

Baya ga ayyukanta na motsa jiki, Roya ta kuma ƙulla wata alaƙa da mata ƴan Afghanistan da ke ciki ko wajen ƙasar ta hanyar shafukan sada zumunta.

Tana tattaunawa da su kan lafiyar jikinsu, da ƙarfafa ƙwarin gwiwarsu da kuma sake gina kansu.

Roya ta yi amannar cewa a duk lokacin da wata mace ƴar Afghanistan ta yi nasara kan wani abu, ba kawai nasarar kanta ba ne, wani mataki ne na sauya matsayin mata a cikin alumma.

Hanyar kai wa ga shiga gasar ta duniya

Roya na shirin fafatawa a cikin gasar masu motsa jiki domin zama ƙarti ta duniya da za a soma ranar 27 ga watan Nuwamba.

Ta samu ɗaukaka ne sosai bayan ta lashe lambar zinare a gasar motsa jiki ta Stoperiet ta wannan shekarar.

Ba kamar sauran fannoni ba da ke mayar da hankali kan kaurin jiki, fannin da ta lashe ya na mayar da hankali ne kan kaurin jiki, da fata mai kyau da kuma lafiyar jiki.

Bayan wannan nasarar, Roya ta kuma lashe gasar Norway Classic ta 2025. Wannan gasa ita ce gasar motsa jiki domin zama ƙarti mafi muhimmanci a arewacin Turai.

Nasarar ce ta kai ta ga samun matsayi a gasar ta Turai, wani mataki mai muhimmanci da ya kai rayuwarta a Kabul da yaƙi ya ɗaiɗaita zuwa idon duniya.

Hakazalika nasarar ta samar mata gurbi a gasar ta duniya.

Goyon bayan da maigidanta ya ba ta

Roya Karimi holding her trophy while her husband, Kamal Jalaluddin, gives her a kiss on the cheek
Bayanan hoto, Maigidan Roya, Kamal Jalaluddin, ya na sumbatarta a kumatu bayan ta lashe lambar zinare

Roya ta haɗu da mijinta na biyu mai suna Kamal Jalaluddin a Norway.

Shi ma ɗan Afghanistan ne, kuma ya na da tarihi mai tsawo a fannin motsa jiki, hakazalika shi ne babban mai goya wa Roya baya.

"Ganin Roya a kan dandamali shi ne cikar burin da muka gina tare, in ji Kamal.

Roya na matukar jin dadin goyon bayan da ya ke ba ta ta kowane fanni: ''Kafin in hadu da Kamal, ina abubuwan motsa jiki, amma ba a mataki na ƙwarewa ba.

''Goyon bayansa ne ya ba ni ƙwarin gwiwar zaɓen bin wannan hanyar. Ina da yaƙinin cewa idan namiji ya goya wa mace baya, za ta iya yin abubuwa masu ban mamaki.''

Roya Karimi looks adoringly towards her husband Kamal Jalaluddin, who is smiling

Duk da nasarorin da ta samu, ƴan'uwan Roya a Afghanistan sun daina goya mata baya. Sai dai a cewar ta ''Na zaɓi kaina da kuma yin aiki domin samun makoma mai kyau.''

Shafukan sada zumuntarta na cike da masu suka, a wasu lokutan har da barazanar kisa.

Sai dai ta yi watsi da sukar da ake yi mata : ''Mutane kawai su na gani na ne da kayan da na ke sawa. Amma a can ciki, na sha wahala na gwamman shekaru na kuma jajirce. Nasarorin da na samu ba su zo cikin sauƙi ba.''

Roya Karimi in a kitchen, looking at camera