Nottingham Forest ba za ta sayar da Anderson ba, Chelsea ta sake tuntuɓar Maignan

Lokacin karatu: Minti 2

Nottingham Forest ta kuduri aniyar ci gaba da rike dan wasan Ingila, Elliot Anderson, mai shekara 23, kuma za ta yi watsi da duk wani tayi da za a yi masa a kasuwar sayar da 'yan wasa a watan Janairu.(Mail),

Manchester United na cikin kungiyoyin da ke zawarcin Anderson kuma kungiyar ta Old Trafford na son ta kara yawan 'yan wasan baya da kuma na tsakiya.(ESPN),

Tottenham na sha'awar daukan dan wasan kasar Sifaniya Samu Aghehowa daga Porto, yayin da Arsenal da Chelsea su ma suke zawarcin dan wasan mai shekara 2. (Caught Offside)

Crystal Palace na son ta sayi dan wasan Newcastle United Joe Willock, mai shekara 26 a watan Janairu. Ana iya shawo kan Magpies su siyar da shi saboda suna son su sayi dan wasan AZ Alkmaar da kuma Netherlands Kees Smit mai shekara 19. (Telegraph ),

West Ham ce ke kan gaba a jerin kungiyoyin da ke son daukar Promise David daga Union Saint-Gilloise a watan Janairu, Wolves da Leeds suma suna zawarcin dan wasan na Canada mai shekara 24. (Teamtalk),

Chelsea ta sake tuntubar wakilan Mike Maignan bayan da ta samu labarin cewa golan na Faransa mai shekara 30 ba ya da niyyar tsawaita kwantiraginsa da AC Milan a bazara mai zuwa.(Sky Sport)

Watakila Chelsea ta sallami golan Denmark Filip Jorgensen, mai shekara 23, domin samun damar daukar Maignan ko wani mai tsaron gida.(Football Insider),

Wakilin dan wasan Brazil Estevao Willian ya ce an yi wa Barcelona tayin dan wasan mai shekara 18 kafin ya koma Chelsea amma yanayin kudin kungiyar ta Sifaniya ya sa ba za su iya siyanshi ba.(Cadena Ser, via Talksport),

Ana danganta dan wasan Atletico Madrid Julian Alvarez, mai shekara 25, da kungiyoyi da dama amma shugaban kungiyar ta La Liga, Enrique Cerezo, ya ce dan wasan na Argentina yana son ya ci gaba da taka leda a kungiyar ta Sifaniya.(Mundo Deportivo).