Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barcelona ta fara zawarcin Guehi, Garcia na iya barin Real Madrid
Barcelona na sanya ido kan ɗan wasan bayan Crystal Palace Marc Guehi, mai shekara 25, duk da cewa har yanzu Liverpool ce kan gaba wajen zawarcin ɗan wasan na Ingila. (Cadena SER).
Brighton na son ɗaukar aron ɗan wasan gaban Real Madrid Gonzalo Garcia mai shekara 21 a watan Janairu, yayin da Leeds da Sunderland suma suka shiga zawarcinsa. (Mail).
Manchester United ta bi sahun Borussia Dortmund wajen zawarcin ɗan wasan gaban Sweden Kevin Filling mai shekara 16 daga AIK Stockholm. (Florian Plettenberg).
Liverpool ce ke kan gaba wajen neman ɗan wasan gaban Bournemouth da Ghana Antoine Semenyo, mai shekara 25, amma Tottenham ma ta matsa ƙaimi kan ɗan wasan. (Teamtalk).
Kocin Manchester United Ruben Amorim ya nuna sh'awar ɗaukar Semenyo amma zai yi wuya ƙungiyar ta iya biyan farashin fam miliyan 65 da Bournemouth ta ƙaƙaba masa a watan Janairu. (Athletic).
AC Milan na zawarcin ɗan wasan Jamus Niclas Fullkrug, mai shekara 32, wanda aka ce zai iya barin West Ham a watan Janairu. (Corriere dello Sport).
West Ham da Everton da Roma suna zawarcin ɗan wasan Manchester United Joshua Zirkzee, yayin da da ɗan wasan na Netherlands, mai shekara 24, ke fama da rashin tagomashi a Old Trafford. (The I).
Ɗan wasan gaban Senegal Nicolas Jackson, mai shekara 24, zai ci gaba da zaman aro a Bayern Munich har ƙarshen kakar wasa ta bana maimakon komawa ƙungiyarsa Chelsea a watan Janairu. (Football Insider).
Sabon kwantiragin da aka bai wa kocin Fulham Marco Silva na tsawon shekara uku ne, inda tsohon kwantiragin ɗan ƙasar Portugal ɗin a Craven Cottage zai ƙare a ƙarshen kakar wasa ta bana. (Sky Sports).
Tsohon kociyan tawagar matasa a Liverpool Vitor Matos ne ke kan gaba a jerin waɗanda za su iya zama kocin Swansea, bayan da ya taka rawar gani a ƙungiyar Maritimo ta Portugal a kakar wasa ta bana. (Talksport).
An dakatar da tattaunawa tsakanin Manchester United da Kobbie Mainoo kan sabon kwantaragi yayin da ɗan wasan tsakiyar Ingila mai shekara 20 ke son komawa Napoli a matsayin aro a watan Janairu. (Calciomercato).
Manchester United ta ki amincewa da tayin da Chelsea ta yi mata na miƙa ma ta ɗan wasan tsakiyar Belgium Romeo Lavia, mai shekara 21, ko kuma ɗan wasan gaban Faransa Christopher Nkunku, mai shekara 28, a wani ɓangare na yarjejeniyar da ta sa ɗan wasan Argentina Alejandro Garnacho mai shekara 21 ya koma Blues. (ESPN).