Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Adeyemi ya fi son Arsenal kan Man Utd, Lewandowski yayi watsi da tayin Fenerbahce
Ɗan wasan Borussia Dortmund da Jamus Karim Adeyemi na son komawa Arsenal maimakon Manchester United, da ke harin ɗaukar ɗan wasan mai shekaru 22. (Mirror)
A wani yanayi na rashin zaɓi, an sananr da ɗan wasan Manchester United Jadon Sancho, zai bar ƙungiyar ya koma Borussia Dortmund, tare da haƙura da albashinda ake biyansa na£300,000 duk mako. (Mirror)
Fenerbahce na son ɗaukar ɗan wasan gaban Poland Robert Lewandowski daga Barcelona, sai dai ya yi watsi da tayin nasu. (AS - in Spanish)
Wolves na son ɗaukar mai tsaron ragar Lazio Christos Mandas a watan Janeru mai zuwa, yayin da ake sa ran siyar da shi kan fam miliyan 12. (GiveMeSport)
Eintracht Frankfurt na ƙoƙarin ɗaukar ɗan wasan Brentford Vitaly Janelt, sai dai Bees na tattaunawa da ɗan wasan don ganin ya tsawaita zamansa har zuwa ƙarashen kakar wassanin. (Teamtalk)
Sunderland za ta bayar da ɗan wasan Najeriya Ahmed Abdullahi aro, a watan Janeru. (Northern Echo - subscription required)
Manchester United na dab da ɗaukar ɗan wasan Ajax Jorthy Moki, duk da cewar Tottenham da Newcastle na zawarcin ɗan wasan. (Caughtoffside)
Babu tabbacin Arsenal za ta ci gaba da zawarcin ɗan wasan Bournemouth Antoine Semenyo, a kakar siyen ƴan wasan a watan Janeru. (Football.London)
Ɗan wasan Newcastle William Osula, mai shekaru 22, zai so koma Eintracht Frankfur a watan Janeru, da suka nuna sha'awar ɗaukarsa matsayin ɗan wasan aro a kakar wasannin.(Bild via FussballTransfers - in German)
Real Madrid sun cimma yarjejeniyar tsawaita kwantaragin ɗan wasan Brazil Vinicius Jr, har zuwa bayan kwantaraginsa ta ƙare a 2027. (AS via Tribuna - in Spanish)