Abu tara game da mutumin da ya sauya fasalin fina-finai a duniya

Daga Thom Poole

.

Asalin hoton, Getty Images

Jean-Luc Godard, wanda ya mutu yana da shekaru 91 na daga cikin mutanen da suka kafa tarihi a duniyar gidan kallo.

Dan kasar Faransa da Switzerland din ya fita a idon duniya ne a karshen shekarar 1950, inda ya zama gaba-gaba a harkar fina-finai a Faransa mai suna New Wave, inda ya ba da umurni a gwamman fina-finai tsawon sama da shekaru 50.

Ga abubuwa tara da muka sani game da shi.

1. Ya sauya harkar fim da yarinya da bindiga

Abin da kake nema ka shirya fim, a cewar Godard shi ne ''yarinya da bindiga''.

Ya kuma tabbatar da hakan a fim din da ya shirya a 1960 mai suna Breathless.

Yarinyar da ta fito a shirin Patricia, na tare da wani dan ta'adda Michel, wanda ake nema ruwa a jallo saboda kashe wani dan sanda.

Ta yaudare shi inda yan sanda suka samu nasarar harbe shi.

Fim din 'Breathless' ya yi kama da shirin ta'addanci, to amma mafi yawan ayyukan Godard na nuna al'ada da kuma yadda ake amfani da hoto don a gidan kallo.

Ya kuma iya amgani da kasafin kudin da bai taka kara ya karya ba tare da samar da riba mai yawan gaske.

Kusan shekaru 60 kenan, har yanzu ana ganin tasirin Godard a harkar shirya fina-finai.

2. Ya fito da tsarin yanka hoto

Wani abu da aka fahimta a shirin Breathless shi ne iya amfani da hoto.

Yanka hoto na da muhimmanci sosai a harkar fim, kuma abinda Godard ya kware kenan, wanda haka ya sa fim din nasa na Breathless ya fita daban a lokacin.

.

Asalin hoton, Breathless

Bayanan hoto, Jump-cuts in Breathless: Godard edited within shots, causing the image to leap forward in time and space

Ta hakan ya janyo hankalin mai kallo, musamman wurin bayyana damuwar Michel.

3. Ya sauya fasalin rubuta labari

Akwai kuma wasu fasahohin da yake dasu. An shirya fim din Breathless ne kai tsaye, ta amfani da kyamarar hannu, inda Godard yake rubuta labari a ranar, ya karanta wa ma'aikatansa su kuma kwaikwayi hakan nan take.

Hakan ya sha bamban da abinda aka saba gani, inda za a yi amfani da kayan aiki masu tsada da kashe kudi sosai wurin tara ma'aikata.

.

Asalin hoton, Getty Images

Basirar da Godard ya yi amfani da ita a shirinsa na Breathless ya sa ya fita daban, kuma ya yi hakan a fina-finansa da dama, inda za ka ga taurarin fim dinsa za su zo inda ake shirya fim amma ba su san kalaman da za su fada ba sai a wurin.

4. Yana matukar son gidan kallo

Godard mutum ne mai sha'awar son gidan kallo wato silma.

Kafin ya zama darakta ko kuma mai shirya fina-finai, yana zuwa gidan kallo don kallon fina-finai. Mutum ne da ake shedi cewa zai iya kallon fim daya sau da yawa a rana daya.

Kamar sauran masana harkar fim a lokacin, ya kan yi fashin baki, ta hakan ya rika bayyana yadda yake tunanin gidan kallo da wasan kwaikwayo su kasance, kafin ya fara bayyana hakan a zahiri.

5. Ya rika fito da sabbin shirye-shirye

Fim din Breathless kadai ya isa ya tabbatar da gogewar Godard harkar shirya fina-finai, to amma bai tsaya a nan ba.

Shafin IMDB ya zayyana sama da ayyuka 100, da suka hada da gajeru da dogayen fina-finai har ma da masu dogon zango.

Amma shekarar 1960 ce aka fi kallon fina-finansa. A 1961 kuma shirinsa na 'A Woman Is a Woman', sai kuma 'Alphaville' a 1965.

Akwai kuma wasan barkwancinsa na 'Weekend' da ya fito da Emil Bronte a 1967.

Jean-Luc Godard and Brigitte Bardot in a car

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Godard and Brigitte Bardot (R), who was the lead in his 1963 film Le Mépris (Contempt)

Bayan shirin 'Weekend' ne ya tsunduma harkar siyasa, a matsayin mai ra'ayin kawo sauyi irin na Marxists, inda ya fara shirya fina-finai masu kwaikwayar irin wadannan akidoji a 1972, kamar fim din All's Well.

Shekaru da dama bayan haka ya yi fina finan da ke magana kan tarihi, har ma ya yi wanda ke magana kan tarihin ita kanta sinima ko gidan kallo.

Sai a 2014, a lokacin da yake cikin shekarunsa na 80, ya saki wani samfurin fasahar 3D mai suna Goodbye to Language.

6. Ya samu tallace-tallace

Irin karbuwar da ya samu a wurin masu kallo ta sa Godard ya samu tallace tallace daga yan kasuwa. Baya ga shirya fina-finai, Godard mutum ne mai karance-karance sosai.

Ya kuma hada kai da sanannun marubuta a lokacin kamar marubucin kasar Jamus Bertolt Brecht.

Fina-finan Godard da dama na amfani da salon Brecht ne, kamar shirinsa na La Chinoise a 1967.

7. Ya rika kwaikwayar dabi'unsa

A mafi yawan ayyukansa, Godard ya kan sa taurarinsa kwikwayar wasu daga cikin dabi'u ko wasu akidu da ya gamsu da su.

A shirinsa na Le Mepris a 1963, tauraron fim din Michel Piccoli ya fito a matsayin wani marubuci dan kasar Faransa, kuma mai shirya fina-finai, inda a ciki ma ya zama darakta a wani fim mai suna 'Adaptation of Ulysses.

Fim din ya nuna rashin jituwa tsakanin kasuwanci da fasaha, da kuma matsalar rayuwar aure, da ta yi kama da irin wadda Godard ya fuskanta tsakanin shi da Anna Karina, wadda ta ja shirye shiryensa da dama.

Jean-Luc Godard with Anne Wiazemsky

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Godard with Anne Wiazemsky, his former wife and star of several of his films

Taurari a shirye shiryensa su kan nuna halayensa, inda ta kai ga ya yi shiri kacokan kan tarihin rayuwarsa JLG/JLG- Self-Potrait.

Sai kuma 2018 da ya yi shirye-shirye dauke da muryarsa masu taken 'The Image Book'.

Mai sharhi kan fina-finai dan kasar Amurka Roger Ebert, ya bayyana Godard a matsayi mai shirya fina-finai a duniyarsa, kuma a cewars fina-finan Godard na da kayatarwa da kuma takaici.

8. Yana da wuyar sha'ani

An san Godard a matsayin mutum da ke da wuyar sha'ani a matsayinsa na dan adam da kuma yadda yake gudanar da aikinsa.

Aure auren da ya yi guda biyu, farko da Anna Karina da kuma Anne Wiazemsky duka sun zo da matsala, wani abu da ya nuna a fina-finansa.

Akwai lokacin da ya daki mai shirya fina-finai Iain Quarrier, kan rashin jituwa bayan fitar shirinsa 'Sympathy for the Devil' a 1968 bayan nuna shirin a London.

Rock group the Rolling Stones during the filming of Sympathy For the Devi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, The filming of Sympathy For the Devil, also known as One Plus One

Ya kuma taba babban rikici da abokinsa wanda shima darakta ne a New Wave, wato Francoise Truffaut.

A 1973, Godard ya taba rubuta wa Truffaut wasika yana sukar fim dinsa Day For Night, kuma Truffaut ya rubuta masa martani marar dadi. Tun daga lokacin basu taba shiryawa ba.

Sai dai ya yadda da hadin gwuiwa, lura da nasarorin da ya samu bayan hada kai da Karina da kuma Wiazemsky.

Ya kuma kulla kawance da Jean-Pierre Gorin da Raoul Coutard, wanda ya bayyan Godard a matsayin 'mai wuyar sha'ani amma kuma mutum mai fasaha'.

Tun daga shekarun 1970, bai taba kulle kawancen da ya yi tasirin wanda ya kulla da abokiyar rayuwarsa ba, wato mai shirya fina-finai yar kasar Switzerland Anne-Marie Mieville.

9. Ya zama allon kwaikwayo

Ayyukan Godard da ke kwaikwayar rayuwarsa ko ta wasu, ko ma na siyasa, sun yi matukar tasiri.

Manyan Daraktoci a Amurka kamar Quentin Tarantino da Bernando Bertolucci a Italiya, kazalika Abbas Kiarostami na kasar Iran da dukansu sun kwaikwayi salon yadda Godard ke shirya fina-finai.

Fina-finan Godard hudu da suka yi zarra har sunansu ya fito a jerin fina-finai 50 mafi shahara na Sight and Sound sun hada da Breathless, da Le Mepris, da Pierrot le Fou da kuma Histoire du cinema.