Zaɓaɓɓun hotuna masu ƙayatarwa na wannan mako daga faɗin nahiyar Afirka da ma wasu wuraren.
Asalin hoton, HASSAN ALI ELMI / AFP
Bayanan hoto, Shukri Osman Muse, mai shekara 25 ta shirya tsaf domin hawa doki a birnin Mogadishu na ƙasar Somaliya. Tana bayyana kanta a matsayin "mace ta farko mai sukuwar dawaki" a ƙasar, kuma ta ce "ta shafe lokaci mai tsawo na rayuwarta tana mafarkin hakan.
Asalin hoton, ANDREA SOLERO / EPA
Bayanan hoto, Washegari, Sabrina Simader ƴar Kenya tana shan kwana a wata gangarar dusar ƙanƙara a gasar cin kofin duniya ta zamiyar ƙanƙara ta FIS Alpine a ƙasar Italiya.
Asalin hoton, CEM OZDEL / GETTY IMAGES
Bayanan hoto, A Dakar, babban birnin Senegal, ƴan kokawa na fafatawa a wasan da suka yi wa laƙabi da 'laamb.
Asalin hoton, YUICHI YAMAZAKI / AFP
Bayanan hoto, Ƴar wasan Tenis ta ƙasar Tunisiya, Ons Jabeur na ƙoƙarin mayar da ƙwallon da abokiyar karawarta Emma Navaro ta Amurka ta cillo, a gasar Australia Open, ranar Asabar.
Asalin hoton, DOAA ADEL / GETTY IMAGES
Bayanan hoto, Duk a ranar ta Asabar, an fara sayar da fitillun yin ado gabanin zuwan watan Ramadan, a birnin Alƙahira na ƙasar Masar.
Asalin hoton, AMANUEL SILESHI / AFP
Bayanan hoto, A ranar Lahadi, manyan shehunnan addinin Kiristanci na orthodox suna yin addu'a a ƙasar Habasha, lokacin da ake yin bikin Timkat...
Asalin hoton, AMID FARAHI / AFP
Bayanan hoto, Timkat lokaci ne na tunawa da lokacin da Yesu Almasihu ya jiƙa jikinsa da ruwa a matsayin alamar mayar da hankali wurin bauta, kuma wannan na daga cikin bukukuwa masu tsarki na mabiya addinin kirista a ƙasar ta Habasha.
Asalin hoton, GERALD ANDERSON / GETTY IMAGES
Bayanan hoto, Yara na karatu da wutar kyandir ranar Juma'a a unguwar Mathare, wata unguwar marasa galihu a Nairobi, babban birnin ƙasar Kenya.
Asalin hoton, TAIWO ARIFAYAN / REUTERS
Bayanan hoto, Ranar Juma'a, wata mata na gittawa ta wani bango da aka yi wa zane-zane a birnin Legas na Najeriya.
Asalin hoton, JOHAN RYNNERS / GETTY IMAGES
Bayanan hoto, Wani tsuntsu na kalaci da tsutsa a Bela Bela na ƙasar Afirka ta Kudu, a ranar Alhamis.
Asalin hoton, SAMEER AL-DOUMY / AFP
Bayanan hoto, Ranar Laraba, wasu maza da suka yi ƙaura daga ƙasar Sudan ta Kudu sun kunna wuta domin jin ɗumi saboda tsananin sanyi da ake sulalawa a arewacin ƙasar Faransa.
Asalin hoton, JEROME FAVRE / EPA
Bayanan hoto, Ranar Juma'a a ƙasar Senegal, wata mata mai suna Bineta Dieng na nuna hoton ƴarta mai shekara 19 a duniya wadda ta yi balaguro domin tafiya cirani ta ƙasar Sifaniya a cikin kwalekwale tare da wasu matasa da dama, shekaru biyu da suka gabata, waɗanda har yanzu ba a ji ɗuriyarsu ba. Ta ce "Babu ɗaya daga cikinsu da ya rayu".
Asalin hoton, ISABEL INFANTES / REUTERS
Bayanan hoto, Ranar Asabar a birnin Landan na ƙasar Birtaniya, wata mata ta jawo hankalin al'umma kan buƙatar al'ummar Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo na ganin an kawo ƙarshen yaƙin Gaza.
Asalin hoton, MEHMET ASLAN / GETTY IMAGES
Bayanan hoto, Wani ɗan ƙabilar Masai na ƙoƙarin kunna wuta da karmamin ciyawa a yankin Arusha na ƙasar Tanzaniya, ranar Alhamis.
Asalin hoton, ABDEL MAJID BZIOUAT / AFP
Bayanan hoto, Mutane na zagayawa a kan tsaunukan Atlas na ƙasar Morocco, ranar Lahadi.
Asalin hoton, YANICK FOLLY / AFP
Bayanan hoto, Sai kuma wannan hoton, inda a ranar Juma'a wasu ƴammata ke ɗauke da darukan ruwa a Lome, babban birnin ƙasar Togo.