Man United za ta yi gwanjon 'yan wasa 12, PSG za ta taya Osimhen

Harry Maguire

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An taba yi wa Harry Maguire barazanar kai masa harin bam a farkon 2022

Manchester United za ta nemi sayar da manyan 'yan wasanta kusan 12 a bazaran nan ciki har da dan bayan Ingila Harry Maguire, da mai tsaron ragar Sifaniya David de Gea, da dan gaban Faransa Anthony Martial. (Mirror)

Red Devils din na duba yuwuwar sayen golan Valencia da Georgia Giorgi Mamardashvili, mai shekara 22 wanda aka yi wa farashi kusan fam miliyan 45, domin ya maye gurbin De Gea. (Givemesport)

Arsenal na sa ido a kan halin da Mason Mount ke ciki a Chelsea kuma da alamu za ta yi gogayya da Liverpool a kan dan wasanb na tsakiya na Ingila a bazara. (Goal)

Haka kuma Gunners din sun tura masu farautar 'yan wasa domin su yi nazari a kan dan wasan tsakiya na Sifaniya Martin Zubimendi, da dan bayan Faransa Robin le Normand, wadanda dukkanninsu suna taka leda ne a Real Sociedad. (Daily Mail)

Paris St-Germain na shirin taya dan gaban Napoli Victor Osimhen fam miliyan 133, kuma da alama za ta shiga gaban Chelsea wajen zawarcin dan Najeriyar mai shekara 24. (Football Insider)

Dan gaban Brazil Roberto Firmino, ya amince ya tafi Barcelona idan kwantiraginsa ya kare a Liverpool a bazara. (Daily Mail)

Mashawartan dan wasan tsakiya na Chelsea da Croatia Mateo Kovacic sun je domin tattaunawa da Manchester City a kan musayar dan wasan wanda ke dab da shiga shekarar karshe ta kwantiraginsa. (Sport Klub)

Liverpool da Tottenham za su kokarin daukan dan bayan Faransa Evan Ndicka mai shekara 23 idan kwantiraginsa da Eintracht Frankfurt ya kare a bazara. (Football Insider)

A shirye Liverpool take ta bar dana gabanta Fabio Carvalho dan Portugal ya tafi wata kungiyar aro a kaka mai zuwa bayan ya yi mata wasa 632 a wannan shekara. (90min)

Aston Villa da Newcastle da Liverpool da kuma Tottenham sun tura masu nemo musu 'yan wasa kallon karawar da za a yi ta wasan dab da na kusa da karshe na gasar kofin Europa tsakanin Sporting Lisbon da Juventus na ranar Alhamis inda za su sanya ido a kan 'yan wasan da suka hada da Adrien Rabiot na Faransa da Marcus Edwards na Sporting dan Ingila da kuma dan wasan tsakiya dan Portugal Pedro Goncalves. (90min)

Marcos Alonso ba shi da niyyar barin Barcelona duk da sha'awarsa da Inter Milan ke yi. (Mundo Deportivo)

Wata kungiyar Saudiyya ta nemi Luka Modric, ya koma cikinta a kaka mai zuwa inda za ta rinka ba shi ninki biyu na albashinsa. (AS )