Pochettino ya tattauna da Chelsea, Barcelona na shirin dawo da Messi

Mauricio Pochettino

Asalin hoton, Getty Images

Tsohon kociyan Paris St-Germain da Tottenham Mauricio Pochettino, ya tattauna da Chelsea a kan karbar aikin horad da kungiyar. (Mirror)

Kungiyar ta Stamford Bridge tana kuma shirin sayar da wasu 'yan wasanta masu yawa kafin ranar 30 ga watan Yuni domin gudun saba ka'idojin kashe kudi. (Evening Standard)

Mai tsaron ragar Manchester United David de Gea, na dab da cimma sabuwar yarjejeniyar ci gaba da zama a Old Trafford. (Forbes)

Haka kuma United din ce a gaba-gaba wajen neman sayen matashin dan wasan gaba na Atalanta da Denmark Rasmus Hojlund mai shekara 20 (Mirror)

Barcelona na kammala tayin da za ta gabatar wa Paris St-Germain domin sake dauko Lionel Messi. (Mundo Deportivo)

Aston Villa ta sabunta bukatarta ta son dan wasan tsakiya na Arsenal da Ingila Emile Smith Rowe. (talkSPORT)

Villarreal na shirin gabatar wa dan bayanta dan Sifaniya Pau Torres sabon kwantiragi amma kuma Aston Villa plotting na neman zawarcinsa a bazaran nan. (Football Insider)

Manchester City na son sayen dan wasan tsakiya na Chelsea da Croatia Mateo Kovacic, a bazara duk da haka kuma tana son ci gaba da kokarin dauko matashin tauraron Borussia Dortmund da Ingila Jude Bellingham.(Givemesport)

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai kuma Paris St-Germain din watakila ta sayi dan wasan tsakiya na Nice da Faransa Khephren Thuram, mai shekara 22, ko kuma dan wasan tsakiya na Lens da Ivory Coast Seko Fofana mai shekara 27 a madadin Bellingham. (CaughtOffside)

Crystal Palace, Wolves, Burnley da Sheffield United dukkanninsu na son sayen dan bayan Jamhuriyar Ireland Matt Doherty, a bazara bayan rashin taka rawar gani da ya yi a Atletico Madrid. (90min)

A shirye Newcastle take ta sayar da Allan Saint-Maximin dean Faransa domin ta samu kudin cefane a bazara. (talkSPORT)

Haka kuma yawancin masu hannun jari a kungiyar ta Newcastle na tattaunawa kan maganar sayen KV Oostende ta Belgium a matsayin karin kungiyarsu. (Athletic)

Manchester United, Newcastle, Wolves, Arsenal, West Ham da Crystal Palace na sa ido a kan dan bayan Bayern Munich na Morocco Noussair Mazraoui. (90min)

Dan bayan Ingila Chris Smalling, ya kusa kammala tattaunawa da Roma kan kwantiragin ci gaba da zama a kungiyar har zuwa watan Yuni na 2025. (Fabrizio Romano)