Arsenal ta kara wancakalal da damar lashe Premier League

Premier League

Asalin hoton, Getty Images

Arsenal ta sha da kyar da gumin goshi a Emirates a hannun Southampton a gasar Premier League wasan mako na 32 ranar Juma'a.

Gunners ta tashi 3-3 da Southampton, wacce take ta karshe a teburi, wadda ta ci 3-1 daga baya Arsenal ta farke biyu.

Karo na uku a jere da Arsenal ta raba maki a Premier League a shirin da take na lashe kofin bana a karon farko bayan kusan shekara 20.

Arsenal ta tashi 2-2 a gidan Liverpool, sannan ta kara wani 2-2 da West Ham, yanzu ta kuma yi 3-3 da Southampton.

Gunners ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da tazarar maki biyar tsakaninta da Manchester City ta biyu.

City mai kwantan wasan Premier biyu za ta karbi bakuncin Arsenal a Etihad a fafatawar mako na 32 ranar Laraba.

Sai dai ranar Asabar 22 ga watan Afirilu, City za ta kara da Sheffield United a FA Cup karawar daf da karshe a Wembley.

Dakika 28 da fara wasa Southampton ta ci kwallo ta hannun Carlos Alcaraz, bayan da Aaron Ramsdale ya yi kuskure.

Karo na biyu da aka ci Gunners cikin kan-kanin lokaci a Premier League a bana, bayan Philip Billing da ya zura kwallo a dakika tara a fafatawa da Bournemouth.

Theo Walcott ne ya ci wa Southampton kwallo na biyu, wanda ya zura raga a tsohuwar kungiyarsa, daga baya Gabriel Martinelli ya farke daya.

Duje Caleta-Car ne ya kara na uku da Southampton ta yi fatan hada maki uku da cin kwallo 3-1.

Nan da nan Gunners ta kara sa matsi ta kara zare daya ta hannun Martin Odegaard saura minti biyu lokaci ya cika, sai Bukayo Saka ya farke na uku daf da za a tashi daga karawar.

Har yanzu Southampton tana ta karshen teburin Premier League.

Southampton da Arsenal sun tashi 1-1 a wasan farko a kakar nan a babbar gasar tamaula ta Ingila ranar Lahadi 23 ga watan Oktoban 2023.