Tuchel ya zama sabon kocin Ingila

A

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

An naɗa Thomas Tuchel a matsayin sabon kocin Ingila. Kwantiraginsa za ta fara ne daga 1 ga watan Janairun 2025.

Ɗan ƙasar Jamus mai shekara 51, ya zama mutum na uku da zai jagoranci Ingila wanda ba ɗan ƙasar ba, bayan Sven-Goran Eriksson da Fabio Capello.

Gareth Southgate ya yi murabus a watan Yuli bayan shan kashi da Ingila ta yi a hannun Sifaniya a wasan karshe na Gasar Euro 2024.

Lee Carsley, wanda aka naɗa a matsayin kocin riƙon kwarya a watan Agusta, zai ci gaba da riko a wasannin Gasar Nations League da Ingila za ta yi da ƙasashen Greece da kuma Jamhuriyar Ireland a wata mai zuwa.

Tuchel, wanda ya bar Bayern Munich a karshen kakar wasanni da ta gabata, ya ce: "Ina alfahari da wannan dama da aka ba ni na jagorantar tawagra Ingila.

"Na daɗe da son irin salon wasa da ake yi a ƙasar nan, kuma tuni na fara jin daɗin matsayi da na samu," in ji Tuchel.

Ya jagoranci Chelsea tsakanin Janairun 2021 zuwa Satumbar 2022 - Ya lashe Champions League da Fifa Club World Cup da Uefa Super Cup gabanin a kore shi.

Nasarorin Tuchel

Champions League daya

FIFA Club World Cup daya

German Champion daya

French Champion biyu

German Cup daya

UEFA Super Cup daya

French Cup daya

French League Cup daya

French Super Cup biyu