Fitattun jaruman Bollywood 5 da suka mutu a 2025

Dharmendra

Asalin hoton, Dinodia

    • Marubuci, Aisha Shariff Baffa
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi Media Broadcast Journalist
  • Lokacin karatu: Minti 5

Masana'antar finafinan Indiya ta Bollywood ta yi rashin wasu fitattun jarumanta maza da mata a shekarar 2025.

Wasu daga cikinsu tarihin Bollywood ba zai taba cika ba tare da ambaton sunayensu ba saboda irin rawar da suka taka.

Dharmendra

Dharmendra

Asalin hoton, Getty Images

An haife Dharam Singh Deol a ranar 8 ga watan Disambar 1935.

Jarumi ne kuma mai shirya finafinai ne sannan kuma dan siyasa ne.

Kodayake an fi saninsa a finafinai na Bollywood musamman na Hindi.

Ana masa kallon daya daga cikin jaruman Indiya da suka samu nasara a tarihin rayuwarsu da kuma taka muhimmiyar rawa a finafinan Indiya.

A tsawon shekaru 65 da ya yi a fagen finafinai na Indiya, Dharmendra, ya yi finafinai sama da 300, sannan kuma yawancin finafinansa sun yi tashe da fice sosai.

Dharmendra, ya fara fitowa a fim ne a shekarar 1960 inda ya fito a fim din Dil Bhi Tera Hum Bhi Tere. Daga nan ne kuma ya ci gaba da fitowa a finafinai da dama.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Daga cikin finafinansa da suka fi fice akwai Seeta aur Geeta da Jugnu da Yadoon ki Baraat da Sholay da Charas da The Burning Train da Dharam Veer da Ghazab da Hukumat da Chupke Chupke da dai sauransu.

Dharmendra, ya auri mata biyu, matarsa ta farko ita ce Prakash Kaur a lokacin yana da shekara 19.

Sun haifi 'ya'ya hudu, maza biyu mata biyu. Mazan sune Sunny Deol da Booby Deol. Kuma su ma sannu ne a Bollwood.

Matarsa ta biyu ita ce Hema Malini, wadda sun fito a finafinai da dama tare, kuma a wani kaulin an ce sai da suka musulunta suka auri juna, saboda a addinin Hindu ba a auren mata biyu, ga shi kuma suna son juna, sai suka ga to ai addinin musulunci ya bayar da damar a auri mata fiye da guda.

Shi ne suka yi auri suka kuma samu 'ya'ya biyu mata, wato Esha Deol da Ahana Deol. Esha Deol ma jaruma ce a finafinan na Bollywood.

Dharmendra, ya mutu a ranar 24 ga watan Nuwambar 2024, yana da shekara 89, wato yana dab da cika shekaru 90 da haihuwa ke nan.

Satish Shah

Satish Shah

Asalin hoton, NDTV Movies

An haife shi a Mumbai, Maharashtra a ranar 25 ga watan Yunin 1951.

Ya yi karatu a makarantar fim inda ya samu kwarewa a bangaren fitowa a finafinai.

Satish Shah ya shahara wajen fitowa a rawar jarumi mai barkwanci.

Ya fara fitowa a finafinai ne a shekarar 1976, kuma ya yi finafinai da dama cikinsu akwai Jaane Bhi Do Yaaro, Main Hoon Na, Kal Ho Naa Ho, Fanaa, Om Shanti Om, Dilwale Dhulhaniya Le Jayenge, Kaho Naa Pyar Hai da Bhoothnath da Ra One da kuma wanda ba a kai ga sakinsu ba kamar Ikkis.

Baya ga finafinai na Bollywood, Satish Shah ya fito a finafinai masu dogon zango kamar Yeh Jo Hai Zindagi da Sarabahi vs Sarabahi da Ghar Jamai da dai sauransu.

Ya auri Madhu Shah a 1982, amma kuma ba su samu haihuwa ba har ya mutu.

Ya mutu a ranar 25 ga watan Octoban 2025, yana da shekara 74 a duniya.

Govardhan Asrani

Asrani

Asalin hoton, Asrani/Facebook

An haife shi a ranar 1 ga watan Janairun 1941.

An fi saninsa da suna Asrani. Jarumi ne sannan kuma mai bayar da umarni ne a fim.

Ya shafe shekaru fiye da 50 a masana'antar Bollywood inda kuma ya fito a finafinai na Hindi da Gujarati sama da 350.

Asrani ya taka rawar babban jarumi da mai taimakawa jarumi da kuma mai barkwanci.

Daga daga cikin rawar da ya taka da ta fito da shi aka san shi sosai ita ce ta dansanda a fim Sholay wato Jailor.

Asrani ya yi finafinai tare da Rajesh Khanna har guda 25 a tsakanin shekarun 1972 da 1991 kamar Bawarchi da Ghar Parivaar da dai sauransu.

Sauran finafinan da ya yi fice sun hadar da Garam Masala da Chupke Chupke da All The Best da The Burning Train da Zamaane Ko Dhikana Hai da Ek Duje Ke Liye da Sargam da Namak Haram da Mili da kuma Himmatuwala da dai sauransu.

Ya auri matarsa Manju Bansal, amma kuma ba su samu haihuwa ba.

Asrani dattijo ne mutumin kirki. Ya mutu a ranar 16 ga watan Oktoba sakamakon matsalar numfashi, yana kuma da shekaru 84 a duniya.

Shefali Jariwala

Shefali

Asalin hoton, NDTV Movies

An haifi Shefali a ranar 15 ga watan Disambar, 1982 a Ahmedabad, Gujarat.

Ta karanci bangaren injiniya. Iyayenta ma'aikata ne dukkansu.

Shefali jaruma ce a finafinan Indiya da kuma mai tallata kayan kawa. Haka kuma ta kan fito a wakoki tare da ainihin mawakan kamar misali wakar Kaanta Laga da ta yi fice, abin da ya sa har ake kiranta da suna Kanta Laga Girl.

Ta fito a fim din Mujhse Shaadi Karoge da kuma fil din Baby Come Naa.

Shefali ta kara fice ne bayan ta fito a shirin nan na Big Boss 13.

Shefali ta auri mijinta na farko Harmeet Singh, wanda mawaki ne a shekarar 2004 inda suka rabu a 2009.

Sannan ta auri mijinta na biyu Parag Tyagi a 2014. Ta mutu a ranar 27 ga watan Yunin 2025 sakamakon bugun zuciya, kuma tana da shekaru 42 a duniya.

Manoj Kumar

Manoj Kumar

Asalin hoton, Getty Images

Harikrishan Giri Goswami, wanda aka fi sani da Manoj Kumar, an haife shi a ranar 24 ga watan Yulin 1937.

Jarumi ne sannan kuma mai bayar da umarni ne kuma marubucin finafinai ne sannan yana rubuta waka da kuma tace finafinai.

Ana daukarsa a matsayin daya daga cikin gwaraza da suka cimma burinsu a finafinan Indiya.

Ya shafe shekaru fiye da 40 yana fim, sannan kuma ya fito a finafinai 55.

Ya samu lambobin yabo da dama hatta gwamnatin Indiya ta karrama shi da lambar yabo.

Fim dinsa na farko ya yi fice bayan wadanda ya fito a matsayin jarumi mai taimawa babban jarumi shi ne Kaanch Ki Gudiya a 1961.

Daga nan ne likkafa ta yi gaba ya ci gaba da fitowa a matsayin babban jarumi a finafinai.

Ya fito a finafinai kamar Kranti da Shaheed da Himalay ki God Mein da Gumnaam da Do Badan da kuma Dus Numbri, wanda wakar cikin fim din ta yi tashe sosai.

Baya ga finafinai, Manoj Kumar ya yi siyasa. Ya auri Shashi Goswani, sannan suna 'ya'ya biyu Kunal da Vishal Goswami.Ya mutu sakamakon ciwon zuciya, a ranar 4 ga watan Aprilun 2025 yana da shekaru 87 da haihuwa.

Gwamnatin Indiya ta bayar da umarnin inda aka yi masa jana'zar ban girma.