Me ya sa mutane ke yawan farkawa daga barci a tsakiyar dare?

Lokacin karatu: Minti 3

''Karfe ɗaya na dare kana cikin barci; karfe biyu karnuka na kuka; karfe uku kuma ana ta jin abubuwa." Wannan abu ne da mutane da dama suka ce sun ji tun lokacin yaranta. Wannan ya sa tsakiyar dare da misalin karfe uku take cike da tsoro wanda ba a cika fahimta ba.

Mutanen da suka balaga da dama su ma sun ce suna yawan farkawa da tsakiyar dare misalin karfe uku ba tare da sun san dalilin haka ba.

Dakta Greg Murray, darektan wata cibiyar lafiyar kwakwalwa a Australiya, wanda ya kware kan samar da waraka kan tunani mai kyau, ya ce farkawa da misalin karfe uku na dare kuma a kasa komawa barci tare da yin tunani daban-daban, abu ne da ɗan'adam ke fuskanta sau ɗaya daga lokaci zuwa lokaci, sai dai ya ce hakan zai zama matsala idan hakan ya koma ɗabi'ar mutum.

Farkawa tsakanin karfe 3 zuwa 4 na asubahi abu ne da ya yawaita tsakanin kashi ɗaya cikin uku na Amurkawa, kuma alkaluman sun ƙaruwa lokacin annobar korona sakamakon gajiya da ta ƙaru cikin mutane.

Sai dai, Dakta Murray ya ce gajiya ba ita ce ke janyo ake yawan farkawa da daddare ba.

"Muna yawan farkawa sau da dama da dare, mun fi yawan farkawa lokacin da dare ya raba. Muna yawan manta irin waɗannan farkawa," a cewar Dakta Murray.

"Amma abubuwa da dama kamar gajiya na iya janyo a cika yawan farkawa idan dare ya raba."

Irin abubuwan da mutum ke aikatawa a kowace rana, kamar tsara abubuwan da zai yi, kallon labarai daban-daban a kafofin yaɗa labaru da kuma shafukan intanet, har ma da rashin hanyar shigar iska cikin ɗaki, su ma suna janyo a riƙa farkawa da tsakiyar dare.

Stephanie Romiszewski, wata mai ba da shawara kan yadda za a iya barci a asibitin Sleepyhead a birnin Landan, ta ba da shawarar cewa: "ka tashi a daidai lokacin da ka tsara kowace rana kuma kar ka kwanta har sai ka ji barci. Bayan ɗan wani lokaci, za ka fuskanci alamun sauyi. Za ka tsinci kanka kana farkawa a daidai lokacin da ka tsara a kullu-yaumin, kuma hakan zai zama abin da za ka riƙa yi."

Romiszewski ta kuma bayar da shawarar cewa, "A riƙa yawan motsa jiki, a shaƙi rana da safe, sannan a ware lokaci yadda ya kamata. Akwai buƙatar mu koyawa kwakwalenmu cewa muna da dama ɗaya ta yin barci, kuma shi ne da daddare, ba can dare ba, kamar yadda yawancin mutane suke yi a birane."

Wani dalilin da ya sa muke farkawa da misalin karfe uku zuwa huɗu shi ne, yawancin mutane na kwanciya da misalin karfe 11 na dare ko kuma 12, sannan su tashi da karsashi da safe da misali karfe 7 ko 8 na safe, abin da ke nufin tsakiyar lokacin barcin shi ne karfe 3 zuwa huɗu.

Dr. Aneesa Das, mataimakiyar darekta a wani shiri kan samun barci a jami'ar jihar Ohio da ke Amurka, ta ce, "yanayin barci da daddare na zagayawa na lokaci, musamman ta hanyar mafarki ko kuma yawaita ketta ido da kuma barci mai nauyi. Mutum zai iya farkawa a kowane irin nau'in barci."

"Dalilin da ya sa kuke farkawa a lokaci ɗaya shi ne saboda kuna kwanciya barci a lokaci iri ɗaya a kowace rana," a cewar Das. "Da zarar asubahi ta kusa, a lokacin ne kuma barci yake kasancewa ba ya nauyi."

Wani farfesa a jami'ar Baylor a Amurka, Dakta Michael K. Scullin, ya ƙara da cewa akwai yiwuwar cewa abin da ya sa mutane ke farkawa da misalin karfe 3 na dare shi ne saboda mugun mafarki. "Masana kimiyya sun amince cewa a tsawon shekaru 100 rashin gama wani aiki ko ma kammala shi zai iya sanya kwakwalwa a farke," in ji shi.

Sai dai Romiszewski ta ba da shawarar cewa idan farkawar da mutum yake yi da misalin karfe 3 zuwa 4 ya kasance har na tsawon watanni uku, ya kamata mutum ya ga likita nan take, saboda hakan zai iya zama ɗabi'ar da ba za a iya shawo kanta da sauki ba, ko da an magance abin da ya janyo ta - kamar gajiya da sauransu.