Yahudawa ƴan kama-wuri-zauna sun ƙwallafa rai a kan filin Gaza

Shin wane ne ba zai so samun gida a bakin teku ba? Ga wasu 'yan Isra'ila masu tsattsauran ra'ayi, babban burinsu zaman gabar teku a yanzu, da kuma wani sashen Gaza.

An tambayi Daniella Weiss, dattijuwa 'yar shekara 78, da ta haifar da wani shirin fafutukar kama-wuri-zauna na Isra'ila, wadda ta ce tuni tana da lissafin iyalai 500 da suka shirya tarewa ko yau aka ba su dama a Gaza.

"Ina da abokai da kawaye a Tel Aviv," in ji ta, "suna shaida min, 'Kada ki manta ki ajiye min fuloti a kusa da gabar tekun Gaza,' saboda da tana kyawun gani, bakin teku ne mai kayatarwa, da yashi mai launin ruwan zinare".

Ta fada musu cewa tuni an kakkama fulotan da ke gabar teku.

Misis Danielle Weiss, jagorar wata kungiyar 'yan kama-wuri-zauna da ake kira Nachala.

Tsawon gomman shekaru, ta kaddamar da matsugunnan Yahudawa a Gabar Yamma da Kogin Jordan da Gabashin Kudus da ke karkashin mamaya kan yankunan Falatsinawa da Isra'ila ta kwace a yakin Gabas ta Tsakiya a 1967.

Wasu a cikin kungiyar 'yan kama-wuri-zauna din sun yi ta buri ko kuma mafarkin sake komawa Gaza tun cikin shekara ta 2005, lokacin da Isra'ila ta ba da umarni ita da kanta na ficewa daga yankin. Sojoji suka ruguza matsugunnai 21 na Yahudawa tare da kwashe 'yan kama-wuri-zauna kimanin 9,000.

Da yawan 'yan kama-wuri-zauna na ganin dukkan wannan al'amari a matsayin cin amana daga gwamnati.

Zaben jin ra'ayin jama'a na nuna cewa mafi yawan 'yan Isra'ila ba sa goyon bayan sake kafa matsugunnan 'yan kama-wuri-zauna a Gaza,kuma ba manufar gwamnati ba ce yin hakan, sai dai tun bayan da Hamas ta kai hare-haren ranar 7 ga watan Oktoba, masu wancan ra'ayi suna ci gaba da tattauna shi a fili.

Misis Danielle Weiss cikin alfahari ta nuna mini wata taswira ta Gabar Yamma da digo-digo na ruwan goro da ke nuna matsugunan Yahudawa. Digo-digo ya mamaye duk sassan taswirar, inda matsugunnan suka babbake fatan Falasdinawa na gina kasarsu.

Akwai Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna kimanin 700,000 a wadannan wurare yanzu kuma adadin 'yan kama-wuri-zauna din cikin sauri yana karuwa.

Mafi rinjayen kasashen duniya na kallon matsugunnan Yahudawan a matsayin haramtattu a karkashin dokokin duniya, ciki har da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. Isra'ila tana da ja a kan haka.

Mun gamu da Daniella a gidanta da ke Kedumim, matsugunin Gabar Yamma, inda gidaje masu jan rufin kwano suka mamaye saman tuddai da kwarin yankin. Ba ta cika zama wuri daya ba duk da bandejin da aka sanya mata a hannu.

Burinta ga makomar Gaza - a yanzu gida ga Falasdinawa miliyan biyu da dubu dari uku, wadanda da yawansu suna fama da yunwa shi ne ya kasance Yahudawa ne.

"Larabawan Gaza ba za su zauna a Zirin Gaza ba," in ji ta. "Wane ne zai zauna? Yahudawa."

Ta yi ikirarin cewa Falasdinawa ne kansu ke son barin Gaza kuma kamata ya yi sauran kasashe su karbe su - ko da yake a doguwar tattaunawar da aka yi da ita, ba ta cika ambatar "Falasdinawa" ba.

"Duniya tana da fadi," in ji ta. "Afirka tana da girma. Kanada tana da girma. Duniya za ta iya karbar al'ummar Gaza. Ta yaya za mu yi hakan? Muna karfafa gwiwar hakan. Falasdinawa a Gaza, mutanen kirkin cikinsu, za a bar su, ban ce a yi dole ba, na ce ana iya bari saboda suna so, su tafi."

Babu wata shaida cewa Falasdinawa suna son barin kasarsu - ko da yake da yawansu mai yiwuwa suna da burin su kubutar na wani dan lokaci, don tsira da rayukansu. Ga mafi yawan Falasdinawa, babu wata hanya ta fita.

Iyakokin yankin suna karkashin tsattsaurar kulawar Isra'ila da Masar, kuma babu wata kasar duniya da ta yi musu tayin ba su mafaka.

Na gabatar mata cewa kalamanta sun yi kama da na wani shirin kakkabe wata al'umma daga kasarsu. Ba ta musanta hakan ba.

"Kana iya kiran hakan da kakkabe al'umma daga kasa. Amma na fada na maimaita, Larabawa ba sa son zama a Gaza, Larabawa masu lafiyayyen hankali ba sa son zama a Gaza. Idan ka so kana iya kiran hakan da kakkabe wata al'umma daga wani wuri, idan ka so kana iya kiran hakan wariyar launin fata, kai ne ka zabi hakan. Ni kuma na zabi hanyar kare kasar Isra'ila. "