Ƙasar da ba a auren mace sai ta nuna shaidar budurcinta

A Iran, adana budurci kafin aure na da muhimmanci sosai ga galibin 'yan mata da iyayensu.

A wasu lokutan maza na bukatar a ba su shaidar da ke tabbatar da budurcin mace - al'adar da hukumar lafiya ta WHO ke cewa akwai rashin dacewa da tauye hakki.

Amma a shekarun baya, ana ta samun karuwar mutanen da ke gangamin adawa da hakan.

"Kin yaudareni na aureki saboda kin rasa budurcinki. Babu wanda zai aureki da an san gaskiya."

Wadannan su ne kalmomin mijin Maryam bayan saduwa da ita a daren farko na aurensu.

Ta yi kokarin tabbatar ma sa da cewa, duk da cewa ba ta fitar da jini ba lokacin saduwa, ba ta taba saduwa da wani ba kafin aurenta ba.

Amma bai yarda da kalamanta ba, da bukatar ta gabatar masa da shaidar budurcinta.

Wannan ba fitaccen abu ba ne a Iran. Bayan baiko, mata da yawa na zuwa wajen likita domin a yi musu gwajin tabbatar da cewa ba su taba kwanciya da namiji ba.

Sai dai, a cewar bayanan WHO, gwajin budurci ba shi da tushe a kimiyance.

Takardar shaidar budurcin Maryam ya nuna cewa tantanin budurcinta na budewa. Hakan na nufin ba zata zubar da jini ba idan ta sadu da namiji.

"An zubar mun da ƙima. Ban aikata wani abin rashin gaskiya ba, amma mijina kullum yana cikin zagina," a cewarta.

"Ba zan iya daukar zaginsa ba na gaji, don haka sai na sha wasu ƙwayoyi domin kashe kaina."

Amma an yi gaggawar kai ta asibiti, kuma ta rayu.

"Ba zan taba mantawa da ranaku masu bakin ciki ba. Sai da na zabge ƙiba da kusan kilo 20 a wannan lokacin."

Ƙaruwar jan hankalin kawo ƙarshen dabi'ar

Labarin Maryam shi ne gaskiyar abin da ke faruwa ga mata da dama a Iran.

Kasancewa da budurcinki kafin aure na da muhimmanci sosai ga galibin 'yan mata da danginsu.

Abu ne da ake darajawa sosai a al'adu masu tsauri.

Amma a 'yan kwanakin nan, abubuwa sun soma sauyawa.

Mata da Maza a sassan duniya nata gangami domin kawo karshen dabi'ar gwajin budurci.

A Nuwambar bara, an shigar da korafe-korafe dubu 25 a wata guda ta shafin intanet.

Wannan shi ne karo na farko da ake fitowa karara ana kalubalantar gwajin budurci tsakanin wasu mutane a Iran.

"Cin mutuncin sirri da keta hakk ne," a cewar Neda.

A lokacin da take daliba yar shekara 17 a Tehran, ta rasa budurcinta bayan saduwa da saurayinta.

"Na tsorata. Na shiga damuwa kan abin da zai biyo baya idan iyayena suka samu labari."

Sai Neda ta ƙudiri aniyar gyara tantanin budurcinta.

A zahiri, wannan tsari ba haramtacce ba ne - amma yana da illa a al'umma don haka ba kowanne asibiti ke yarda da yin wannan aikin ba.

Don haka sai Neda ta nemi irin asibitocin nan masu zaman kansu da za su yi mata wannan aiki cikin sirri - duk da barazanar da ke tattare da yin haka.

"Na kashe duk kudadena na asusun ajiya. Na sayar da komfutata, wayata da sarkokin zinare na," a cewarta.

Tana bukatar sanya hannu a wasu takardu domin daukar alhakin duk wani abin da zai iya biyo baya.

Wata likitar jinya ce ta yi aikin. An shafe kusan mintuna 40 ana aikin.

Amma Neda na bukatar makonni kafin ta warke.

"Ina cikin azababben ciwo. Na kasa motsa kafafuwa," a cewarta.

"Na kasance cikin yanayi na kadaici. Amma fargabar kar iyayena su gano abin da na aikata ya cigaba da karfafa mun gwiwar jure azabar."

A karshe, duk azabar da Neda ta sha ya tashi a banza.

Bayan shekara guda, sai ta gamu da wani da yake son aurenta. Amma da suka sadu, ba ta fitar da jini ba. Aikin da ta yi bai yi nasara ba.

"Saurayina ya zargeni da kokarin yaudararsa domin ya aure ni. Ya ce ni makaryaciya ce don koma sai ya rabu da ni."

Matsin lamba daga iyaye

Duk da dakile batun gwajin budurci da WHO tayi kan hujojin rashin tushe a kimiyance, ana cigaba da aiwatar da wannan dabi'a a kasashe da dama, ciki akwai Indonsiya da Iraki da Turkiyya.

Cibiyar kiwon lafiya ta Iran ta jaddada cewa tana aiwatar da wannan gwaji na budurci ne kadai idan aka tsinci kai cikin wani yanayi - kamar batun shari'ar kotu da zargin fyade.

Sai dai, galibin masu zuwa neman shaidar budurci suna kasancewa masoya da ke kokarin aure.

Don haka suna zuwa asibitoci masu zaman kansu - da iyayensu mata ke rakiya.

Wata likitar mata ko ma'aikaciyar jinya tana gudanar da gwaji da bada takardar shaida.

Wannan ya kunshi cikakken sunan mace, na mahaifinta, da lambobinta shaidar 'yar kasa da hotuna a wasu lokutan.

Takardar na bada bayanai kan matakin tsantsanin budurcinta, dauke da bayanai kamar haka: "Wannan yarinyar gwaji ya tabbatar da budurcinta."

Tsakanin iyalai masu tsauri, dole sai mutum biyu sun sanya hannu a matsayin shaidu kan takardar asibitin - galibin lokuta iyaye mata.

Dakta Fariba ta shafe shekara da shekaru tana bada irin wannan shaidar takardar.

Ta yarda da cewa hakan akwai cin mutunci, amma kuma tana ganin kamar tana taimaka wa mata ne.

"Suna cikin matsi ne sosai daga danginsu. A galibin lokuta na kan yi wa masu shirin zama ma'aurata karya.

"Idan sun kwana tare kuma suna son aure, sai na ce a gaban iyayensu cewa budurcin macen lafiya yake."

Amma ga maza da dama, auren mace da budurcinta na da muhimmanci.

"Idan mace ta rasa budurcinta kafin aure, ba abar yarda ba ce. Tana iya bin maza da aurenta," a cewar wani injiniyar wuta mai shekara 34, Shiraz.

Ya ce ya sadu da 'yan mata 10. "Na kasa jurewa," a cewarsa.

Ali ya yarda da cewa akwai tasiri mai girma tsakanin Iraniyawa, amma bai ga dalilin kaurace wa al'adu ba.

"Al'adu na nuna cewa maza sun fi mata 'yan ci."

Ra'ayin Ali abu ne da mutane da dama suka shaida, musamman a kauyuka, inda mutane ke da tsatsauran ra'ayi.

Fata na gaba

Shekara hudu bayan kokarin kashe kanta da zama da mijin da ke cin zarafinta, Maryam a karshe ta samu takardar saki ta hanyar kotu.

Makonnin da suka gabata ta zama bazawara.

"Abu ne mai wahala na iya amincewa da wani namji kuma," a cewarta. "Bana tunanin aure a nan gaba."

Tare da wasu dubban mata, ita ma ta sanya hannu kan korafin da aka shigar ta intanet kan kawo karshen shaidar budurci kafin aure.

Duk da cewa ba ta sa ran ganin sauyi ba a yanzu, ba ta nuna a zamaninta amma dai ta hango wata rana mata za su daina fuskantar bambanci a kasarta.

"Ina da tabacci hakan zai faru wata rana. Ina fatan nan gaba babu macen da zata fuskanci wahalar da na gani a rayuwa."

An sauya sunayen duk mutanen da aka tattauna da su domin ba su kariya.

Idan kuma wani bangare na wannan labari ya taba shafarki ko kina son tsokaci kan wannan makala don Allah a ziyarci shafin taimako na BBC.