Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An jahilci manufar samar da ƴansandan jihohi a Najeriya - Uba Sani
Gwamnan jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya Sanata Uba Sani ya ce wasu sun jahilci manufar samar da ƴansandar jiha da ake cecekuce akai a ƙasar.
A makon nan ne Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya amince da a duba yiwuwar kafa rundunar ƴansandan jihohi a ƙasar a matsayin wani mataki na shawo kan matsalar tsaro da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.
Shugaban ya amince da haka ne bayan ganawa da ya yi da gwamnonin jihohin ƙasar 36, inda Tinubu ya buƙaci gwamnonin su fara tsara yadda za a aiwatar da shirin.
Cikin tattaunawarsa da BBC kan batun, gwamnan na jihar Kaduna ya ce yawan ƴansandan da ake da su a ƙasar nan bai kai yadda za su iya kare al'umma ba.
Ya ƙara da cewa babu wani gwamna a jiharsa da yake iya bai wa kwamishinan ƴansanda umarni.
Gwamnan Kaduna daya daga cikin masu fama da kalubalen yanbindiga masu satar mutane domin kuɗin fansa ya ce akwai ƙarancin ƴansanda a Najeriya, kuma samar da ƴansandan jihohi zai taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar matsalar tsaro da ta addabi Najeriya.
Ya ce rashin samun cikakken iko ga gwamnoni kan jami'an tsaro ne ya tilasta wa wasu jihohin daukar matakin kafa rundunonin tsaro na ƴan sa-kai.
"Kundin tsarin mulki bai ba su dama su riƙe manyan makamai ba, su kuma ƴan ta'addar da ake fama da su suna riƙe da manyan makamai ciki har da irin wadanda za su iya kashe mutum hamsin lokaci guda, mu kuma bamu iya ba ƴan sa-kai manyan makamai irin wadannan domin su kare al'umma."
Gwamnan ya ce babu wani abu da yake da mahimmanci wanda ya wuce tsaro a Najeriya.
Ya ce ƙudurin da ya taɓa gabatarwa a majalisa bai ce gwamnatin jiha ce za ta dauki gabadaya nauyin ƴansandan da ake son samarwa ba, "domin su ma suna ƙarƙashin shugaban ƙsa ne amman ana kiransu ƴnsandan jiha."
"Ba gwamnatin jihohi ne za su dauki nauyin ƴansandan jiha ba, a 'a suma duk za su kasance ƙarƙashin shugaban ƙasa ne," in ji shi
Ya ce idan aka dauko ɗansanda daga wata jiha aka kai wani wuri, bai san yanayin mutanen wajen ba to ba zai saki jiki ba, amman ɗansandar jiha ya yankinsa zai tsaya ya kare wurin saboda ya san yanayin abin da ke faruwa a wurin
"Duk wani gwamna da shugaban ƙasa sun san cewa idan ba a magance matsalar tsaro ba duk abin da aka saka a gaba ko harkar ilimi ko lafiya ko noma ba za a yi nasara ba, saboda ga makarantu nan da dama an rufe su saboda rashin tsaro."
Sha'anin tsaro ya taɓarɓare a faɗin ƙasar inda a kowace rana ake tashi da sabon labarin sace-sacen mutane don neman kuɗin fansa da matsalolin ƴan fashin daji.
Masanan na ganin cewa a maimakon kafa ƴansandan jihohi, kamata ya yi hukumomi su mayar da hankali wajen bai wa ƴansandan da ake da su a ƙasa ƙarin horon da ya dace.