Ranakun hutu da na bukukuwa a Najeriya cikin shekarar 2026

Bikin sallar Idi a garin Bauchi da ke Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bikin sallar Idi a garin Bauchi da ke Najeriya
Lokacin karatu: Minti 3

An yi hutun sabuwar shekarar 2026, ranar farko da ake yin hutu a kowace shekara a Najeriya, amma akwai ranakun hutu da yawa da za su taho a cikin shekarar.

Hutun bukukuwan addini da na makaranta da kuma na gwamnati ne suka fi yawa a kowace shekara.

BBC ta duba jerin ranakun hutu da ƴan Najeriya za su samu a shekarar 2026 wadda ta kama.

Ranakun da gwamnati za ta bayar da hutu

1 ga watan Janairu

Wannan ce ranar bikin shigowar sabuwar shekara wadda gwamnati ta bayar da hutu a Alhamis ɗin makon da ya gabata.

20 ga watan Maris

Zai iya yiwuwa Ƙaramar Sallah (Eid El-Fitr) ta faɗo ranar Juma'a.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai wannan ranar za ta iya sauyawa kasancewar ganin jinjirin wata ne ke tabbatar da ranar da za a hau sallah, saboda haka wannan hutun zai iya matsawa.

3 ga watan Afrilu

Good Friday da kuma Easter Sunday ranaku ne da mabiya addinin Kirista ke amfani da su wajen tunawa da gicciye Yesu Almasihu da kuma mutuwarsa. A wannan shekara ta 2026 Godd Friday za ta fado ne a ranar 3 ga watan Afrilu, Easter Sunday kuma 5 ga watan Afrilu yayin da Easter Monday za ta fada ranar 6 ga watan Afrilu.

1 ga watan Mayu

Alhamis 1 ga watan Mayu za ta zama ranar ma'aikata a Najeriya kuma rana ce ta hutu. Rana ce ta hutu da raƙashewa ga ma'aikata domin jinjina wa kansu kan gudumawar da suke bayarwa.

27 ga watan Mayu

Wannan shekarar za a iya samun bukukuwa biyu a ranar 27 ga watan Mayu, sai dai ɗaya zai iya canzawa.

Za a iya bayar da hutun 27 da 28 ga watan Mayu sanadiyyar bikin babbar sallah, to amma hakan zai iya canzawa sanadiyyar ganin wata.

Daya bikin shi ne na ranar yara.

12 ga watan Yuni

Juma'a 12 ga watan Yuni ne ranar Dimokuraɗiyyya. Gwamnati za ta ayyana hutu a wannan rana domin tunawa da mulkin dimokuraɗiyya da kuma yadda aka samu ɗorewar mulkin dimokuradiyya tun daga shekarar 1999.

26 ga watan Agusta

Ita ce Laraba, kuma za ta iya zama ranar hutu domin bikin Maulidin Annabi Muhammadu (SAW).

1 ga watan Oktoba

Wannan ita ce ranar bikin tunawa da samun ƴancin kan Najeriya.

25 ga watan Disamba

Juma'a 25 ga watan Disamba za ta kasance ranar Kirsimeti domin bikin ranar haihuwar Yesu Almasihu.

26 ga watan Disamba

Asabar, za ta kasance ranar bayar da kyaututtuka ta mabiya addinin Kirista, wadda ake kira Boxing Day.

31 ga watan Disamba

Wannan ce ranar jajibirin 2027. Duk da cewa ba ranar hutu ba ce a Najeriya amma duk da haka wasu na yin bukukuwa a ranar.