Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waɗanne babura aka haramta wa hada-hada a Kano?
Tun bayan sanar da cigaba da ɗabbaƙa dokar haramta zirga-zirgar babura a birnin Kano da gwamnatin jihar Kano ta yi a koƙarinta na daƙile matsalar tsaro da wasu sassan jihar ke fuskanta, al'ummar birnin suka shiga ruɗani dangane da irin baburan da dokar ta shafa.
Bayanai sun nuna cewa a ranar Talata ne wata rundunar haɗin gwiwa ta ƴansanda da jami'an hukumar KAROTA a jihar suka ƙaddamar da wani samame inda suka rinƙa kama duk mai babur ɗin da aka gan shi da goyo.
Hakan ya sa jama'a yin tambayoyi cewa shin waɗanne babura ne aka haramta wa zirga-zirga a birnin?
Me dokar hana acaɓa a Kano ta ce?
Dokar wadda aka yi ta a shekarar 2013 mai suna dokar Hana Hawa Babur da Taƙaita Abubuwa masu alaƙa da hakan, wato "Motorcycling and Related Matters Regulation Law", tana da sassa bakwai.
Masana harkar shari'a sun ce dokar ba ta da rikitarwa kasancewar an yi ta ne kacokan kan al'amuran sana'ar acaɓa.
Barista Abba Hikima ya yi fashin baƙi dangane da sassan dokar.
- Sashe na ɗaya: Wannan sashen doka shi ne wanda ya faɗi sunan dokar.
- Sashe na biyu: Shi kuma sashe na biyu na dokar ya ce "acaɓa" shi ne kasuwanci ko kuma hada-hada na ɗaukar fasinjoji a kan babur domin biyan kuɗi.
- Sashe na uku: Wannan sashe ya ce daga lokacin da aka fara aiki da wannan doka, wato ranar 7 ga watan 2 na 2013 aka ce haramun ne mutum ya ɗauki fasinja domin biyan kuɗi, wato acaba a ƙananan hukumomin cikin birni guda 8 wato Kano Municipal da Gwale, da Dala da Nassarawa da Kumbotso da Fagge da Tarauni da Ungogo.
- Sashe na huɗu shi kuma ya ce duk inda ba waɗannan ƙananan hukumomi ba duk wanda zai yi acaɓa sai ya je wurin Mai Unguwa da ƴansanda domin samun lasisi inda zai biya naira 500 a ba shi katin shaida."
- Sashe na biyar: Sai dai kuma sashen ya ƙara da cewa gwamna yana da dama ya sauya dokar a wuraren da ba a hana acaɓar ba ta hanyar "umarnin gwamna".
- Sashe na shida: A ƙarshe sashen ya ce duk wanda aka kama da laifi za a ci tarar sa naira 10,000 ko zaman gidan yari na wata shida ko kuma a a hada masu duka biyu.
- Sashe na bakwai: Sashe na ƙarshe na wannan doka ya ce duk wanda aka kama ya yi laifi za a yi masa hukunci a kotun majistare ko kotun Shari'ar Musulunci.
Ko matakin da KAROTA ta ɗauka na kan ƙa'ida?
Sai dai kuma barista Abba Hikima ya ce yayin da gwamnati ke da haƙƙin kare dukiyoyi da rayukan al'ummar jihar Kano, ya kamata dole kuma gwamnatin ta lura da haƙƙoƙin al'umma.
"Abin da ƴan KAROTA suka yi dangane da kama baburan mutane ba daidai ba ne. Mun samu kira daga ƴan'uwa da abokai cewa an kama su saboda suna tuƙa babur duk da cewa ba acaɓa suke yi ba."
"Doka fa cewa ta yi acaɓa kawai aka hana. Duk wanda ba ɗan acaɓa ba bai shiga cikin wannan hani ba," in ji Barista Abba Hikima.
Hukumar KAROTA ba ta ce komai dangane da tuhume-tuhumen da ake yi mata.
Sai dai masana na ganin cewa hukumar ta KAROTA ba za ta aiwatar da irin wannan abu ba, ba tare da umarnin gwamnati ba ko kuma ƙoƙarin tabbatar da an bi doka da odar da gwamnati ta saka.
Abin da muke nufi da hana acaɓa - Gwamnatin Kano
Kwamishinan shari'a na jihar Kano, Abdulkareem Kabiru Maude ya shaida wa BBC cewa "abin da dokar take nufi shi ne acaɓa kawai aka hana wato wanda zai ɗauki mutu daga nan ya kai nan domin karɓar kuɗi."
Kwamishinan ya yi ƙarin bayani cewa wannan doka ba ta shafi duk wani mai babur ɗin da ba na haya ba ne saɓanin abin da bayanai suka nuna cewa wata runduna ta musamman a Kanon ta fara kama duk wanda aka gani da babur.