Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yaushe ɗan'adam ya fara alaƙa da mage?
- Marubuci, Helen Briggs
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Environment correspondent
- Lokacin karatu: Minti 4
A tsari irin na rayuwar maguna, sukan ɗauki lokaci mai tsawo kafin tantance wanda za su yi mu'amala da shi.
Bayanai na binciken kimiyya sun nuna cewa alaƙar mage da bil'adama ta fara ne daga baya-baya, kuma a wuri na daban, ba kamar yadda aka yi tunani ba a baya.
Nazarin da masana kufai suka yi kan wasu ƙasusuwa ya nuna cewa maguna sun fara shaƙuwa da ɗan'adam ne dubban shekaru da suka gabata a arewacin Afirka.
"Yanzu suna a ko'ina, muna haɗa finafinai da su da kuma sanya hotunansu a ko ina a intanet," in ji Farfesa Greger Larson na jami'ar Oxford da ke Birtaniya.
"Wannan alaƙa da muke da ita da maguna ta faro ne kimanin shekara 3,500 zuwa 4,000 da suka gabata, ba 10,000 da aka yi tsammani ba."
Dukkanin magunan da muke gani a yanzu sun samo asali ne daga nau'i ɗaya – magen daji ta Afirka.
Yadda suka baro daji tare da ƙulla alaƙa da ɗan'adam abu ne da ya daɗe yana bai wa masana kimiyya wahala.
Domin warware wannan abin da ya shige duhu, masu bincike sun yi nazarin ƙwayar halittar gado daga ƙasusuwan maguna da aka samu a kufayin da aka yi nazari a kansu a faɗin ƙasashen Turai da arewacin Afirka da kuma Anatolia.
Sun yi nazari kan ƙwayoyin halittar magunan ta hanyar lura da shekarunsu, sannan suka kwatanta su da ƙwayoyin halittar magunan wannan zamani.
Sabbin bayanan da aka tattara sun nuna cewa alaƙar mage da ɗan'adam ta fara ne a yankin arewacin Afirka ƴan ɗaruruwan shekaru bayan ɗan'adam ya fara noman abincin da yake ci.
"A maimakon ƙulla alaƙa ta farko a inda ɗan'adam ya fara zama da kuma yin noma, bayanan sun nuna cewa alaƙar ta faro ne da mutanen Misira," in ji Farfesa Larson.
Wannan ya yi daidai da ilimin da ɗan'adam ke da shi na cewa Misira yanki ne da ke girmama maguna, inda har suka riƙa alkinta su bayan mutuwa domin gangar jikinsu ya daɗe bai lalace ba.
Bayan maguna sun fara alaƙa da mutane, sai suka bazu a duniya a matsayin kyautar girmamawa ko kuma waɗanda ke a jiragen ruwa sannan kuma aka riƙa amfani da su a matsayin masu magance yaɗuwar ɓeraye.
Maguna sun isa yankin Turai ne shekaru 2,000 da suka gabata, baya sosai idan aka kwatanta da yadda aka yi tsammani a baya.
Sun karaɗe ƙasashen Turai zuwa cikin Birtaniya tare da Romawa, sannan suka nausa gabas har zuwa China.
A yanzu ana samun maguna a kowane yanki na duniya baya ga Antarctica.
Wani sabon abu kuma shi ne an gano cewa magunan daji sun daɗe suna alaƙa da mutanen China kafin isowar magunan gida.
Magunan dajin su ne irin su damisar Leopard da kuma ƴan'uwanta masu roɗi-roɗin fata, waɗanda suka riƙa rayuwa kusa da mutane a China tun shekara 3,500 da suka gabata.
Alaƙar bil'adama da damisar Leopard a China ta kasance irin ta babu ruwan kowa da kowa, ban cutar da kai ba, kai ma kada ka cutar da ni, in ji Farfesa Shu-Jin Luo ta jami'ar Peking da ke birnin Beijing a kasar China.
"Damisar leopard sun riƙa amfana da zaman da suke yi a kusa da bil'adama, su kuma mutane ba su damu da su ba, har ma sun riƙa maraba da su saboda suna maganin ɓeraye," in ji ta.
Al'umma ba su ɗauko damisar leopard sun kawo gida ba, sun bar su ne suna ci gaba da rayuwarsu a cikin dazukan nahiyar Asia.
Sai dai wani abu shi ne a baya-bayan nan an riƙa haɗa barbarar yanyawa tsakanin damisar leopard da magunan gida domin samar da magunan Bengal, waɗanda ake yi wa kallon sabbin nau'in mage a cikin shekarun 1980.