Wace rawa Donald Trump ya taka wajen kawo zaman lafiya a Gaza?

...

Asalin hoton, EPA/Shutterstock

    • Marubuci, Jeremy Bowen
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, International editor
  • Lokacin karatu: Minti 6

Ziyarar gaggawar da Donald Trump ya kai Isra'ila da Masar tabbas ta samu nasara.

Duk wanda ya saurari jawabansa a Urushalima da Sharm el-Sheikh zai ga mutum mai jin daɗin mulkinsa, yayin da ake tafa masa a majalisar Isra'ila, sannan a Masar yana jin daɗin ganin shugabanni da dama na duniya sun halarta.

Wani tsohon ɗan diflomasiyya da ke wurin ya ce Trump kamar yana kallon shugabannin ƙasashen wurin a matsayin cikon wuri ne kawai a cikin abin da ya tsara.

Saƙon Trump a Sharm el-Sheikh shi ne cewa ya kawo babban sauyi a tarihin duniya. Ya ce:

"Abin da nake yi tun lokacin da na fara aiki shi ne ƙulla yarjejeniyoyi. Mafi girman yarjejeniyoyi sukan faru da kansu ne, haka abin ya faru a nan. Wataƙila wannan yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da aka cimma ita ce mafi girma a cikin duk yarjejeniyoyin da na taɓa yi."

Masu sa ido sun fahimci cewa daga jawabansa, kamar aikin ya kammala. Amma ba haka ba ne.

Babu shakka Trump na da hakkin a yabe shi wajen cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni da aka yi tsakanin Gaza da Isra'ila.

Amma kuma ƙasashen Qatar da Turkiyya da Masar ne suka yi amfani da tasirinsu wajen tilasta wa Hamas ta amince.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wannan ya sa aikin ya zama na haɗin gwiwa, rawar da Trump ya taka wajen tsagaita wutar na da muhimmanci, amma ba lalle bane ta ɓa tabbatar da zaman lafiya.

Da ba don matsin lambar da ya yi wa Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ba, domin ya amince da sharuɗɗan da a da ya ƙi amincewa da su, da ba a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

Abin da ya kamata mu gane shi ne: wannan yarjejeniya tsagaita wuta ce da musayar fursunoni, ba yarjejeniyar zaman lafiya ba, kuma ba ma farkon tattaunawar zaman lafiya bane.

Mataki na gaba a cikin shirin Trump mai matakai 20 shi ne a samar da yarjejeniyar da za ta cike giɓin tsarin da ya bayyana cewa za a ƙwace makamai a Gaza, a tabbatar da tsaro, sannan a kafa kwamitin da zai ƙunshi Falasɗinawa don tafiyar da mulki.

Wannan kwamiti zai riƙa bayar da rahoto ga "Board of Peace" wanda Shugaba Trump zai jagoranta.

Akwai aiki mai yawa da ya rage a yi kafin hakan ya tabbata.

Yarjejeniyar Gaza ba ita za ta tabbatar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya ba wacce har yanzu ba a kai ga cimma ta ba.

Donald Trump da Benjamin Netanyahu

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Netanyahu ya kira Trump a matsayin "aboki mafi girma" da Isra'ila ta taɓa samu a Fadar White House.

Abu mafi muhimmanci kuma shi ne, babu wata hujja da ke nuna akwai niyyar siyasa ta gaske don ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya.

Yawancin yaƙe-yaƙe suna kawowa ƙarshe ne idan ɓangarorin da ke faɗa sun gaji, sannan suka yarda su zauna su sasanta. Yaƙin Gaza ya zama irin waɗannan, idan har abin da Trump ya ce gaskiya ne wanda ke cewa yaƙin ya kawo ƙarshe.

Hanya ta biyu da ake kawo ƙarshen yaƙi ita ce ta cikakkiyar nasara, wacce ta ke bai wa waɗanda suka ci nasarar damar tsara makomar gaba.

Mafi kyawun misali shi ne yadda Jamus ta mika wuya ba tare da sharaɗi ba a shekarar 1945 bayan Yaƙin Duniya na Biyu.

Kafin 9 ga Satumba, lokacin da Netanyahu ya ba da umarnin kai harin makami mai linzami kan Qatar, har yanzu yana da niyyar murƙushe abokan gaban Isra'ila gaba ɗaya,saboda Isra'ila ta zama mai ikon tsara makomar Gaza.

Wannan hari da Isra'ila ta kai kan Qatar ya fusata Trump ƙwarai.

Qatar tana daga cikin manyan abokan Amurka kuma ita ce ke da babbar sansanin sojin Amurka a Gabas ta Tsakiya.

Haka kuma, wuri ne da ɗansa ke gudanar da harkokin kasuwanci masu fa'ida.

Trump ya yi watsi da hujjar Netanyahu cewa manufar harin ita ce shugabannin Hamas, ba Qatar ba.

A wurin Trump, buƙatun Amurka sun fi na Isra'ila muhimmanci.

Bayanan bidiyo, Yadda kamara ta tsaro ta ɗauki lokacin da Israila ta kai wa shugabannin Hamas hari a Doha

Trump ya koma Washington DC, kuma jakadu sun ce Amurkawa sun fahimci cewa daidaita cikakkun bayanan yarjejeniyar da ake kokarin cimmawa abu ne mai matuƙar muhimmanci, amma hakan ba zai faru cikin gaggawa ba. Matsalar ita ce, watakila lokaci bai ishe su ba.

A mafi yawan lokuta, akan saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta tun a farkonta. Waɗanda kuma ba a samu saɓawa ba yawanci suna kasance ne waɗanda aka tsara bisa ƙa'ida mai ƙarfi tsakanin ɓangarorin da ke yaƙi da juna da suka yanke shawarar cewa hanya mafi kyau ita ce su tabbatar da cewa yarjejeniyar ta yi aiki.

Amma wannan tsagaita wutar ta Gaza ba ta da tushe mai ƙarfi. Bayan awa 24 da Isra'ilawa da Falasɗinawa suka yi murna da dawowar fursunoni, matsaloli suka fara bayyana.

Hamas ta dawo da gawarwakin Isra'ilawa bakwai kacal daga cikin 28 da aka kashe, tana cewa yana da wuya a gano kaburburensu saboda rushewar Gaza. Isra'ila ta nuna gajiyarta, ta kuma rage taimakon da ke shiga Gaza da rabin adadi, tare da rufe iyakar Rafah da Masar.

Ministan kuɗi mai tsattsauran ra'ayi na Isra'ila, Bezalel Smotrich, ya ce: "Matsin soji ne kaɗai ke dawo da fursunoni."

Dakarun sojin Isra'ila (IDF) har yanzu suna riƙe da kusan kashi 53 na yankin Gaza.

A ranar Talata, sun kashe Falasɗinawa da suka ce suna kusantar dakarunsu. Hukumar ceto ta Falasɗinawa ta shaida wa BBC cewa mutum bakwai ne suka mutu a wasu hare-hare biyu.

Ana ganin IDF tana ci gaba da bin dokokin da ta yi amfani da su kafin tsagaita wuta inda sojoji ke yin harbin gargaɗi idan Falasɗinawa suka kusanci layin farko, sannan su yi harbi don kisa idan suka ƙetare na biyu. Matsalar ita ce, Falasɗinawa ba su san inda waɗannan layuka suke ba.

A gefe guda kuma, Hamas tana sake nuna ƙarfinta.

Mayaƙanta masu ɗauke da makamai sun koma tituna, suna kai hari kan ƙungiyoyin da suke adawa da su, ciki har da waɗanda IDF ke karewa.

An yaɗa bidiyon yadda Hamas ke kashe mutanen da take zargi da haɗin kai da Isra'ila, domin tsoratar da masu adawa da kuma nuna cewa har yanzu tana da iko duk da hare-haren Isra'ila.

Falasɗinawa a birnin Gaza

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kusan duka gine-ginen Gaza sun ruguje saboda hare-hare.

Sashi na 15 na shirin Trump na tsagaita wuta a Gaza ya ce Amurka "za ta yi aiki tare da abokan hulɗa na Larabawa da na duniya don ƙirƙirar wani rukunin Ƙarƙashin Tsaro na ƙasashen duniya (ISF) na ɗan lokaci wanda za a tura nan take a Gaza."

Amma ba za a iya tara da tura irin wannan rundunar ba idan ba a tabbatar da tsagaita wuta ba.

Ƙasashen da za su iya ba da sojoji ba za su tura su don amfani da ƙarfi wajen kwace makaman Hamas ba idan tsagaita wutar ba ta da tushe.

Hamas ta nuna alamar cewa za ta iya miƙa wasu manyan makamai, amma ba za ta bari a ƙwace mata makamai gaba ɗaya ba.

Netanyahu ya yi barazanar cewa idan ba wanda zai aiwatar da aikin, Isra'ila za ta kammala shi da kanta. Ya ce dole a cire makaman Hamas, "ta hanyar sauƙi ko ta hanyar wuya."

Trump ya bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da shi ya kawo za ta kawo ƙarshen dogon rikicin da aka yi tsakanin Larabawa da Yahudawa a ƙasar dake tsakanin Kogin Jordan da Bahar Rum.

Har ila yau ya ce za ta haifar da zaman lafiya a fadin Gabas ta Tsakiya.

Idan yana da gaskiya cewa an riga an kammala aikin kawo zaman lafiya, yana yaudarar kansa ne. Samun zaman lafiya yana buƙatar mayar da hankali na dogon lokaci da aikace-aikacen diflomasiyya mai wahala, da shawarwarin ɓangarorin biyu cewa lokaci ya yi su yarda su sadaukar saboda tabbatar da zaman lafiya.

Shugabannin Amurka na baya sun na su sha yin imanin cewa za su iya kawo zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Trump zai gane cewa saboda shugaban ƙasa komin ƙarfinsa ya ce a samar da zaman lafiya, hakan ta faru.