Su wane ne mayaƙan Dughmush da ke ƙalubalantar Hamas a Gaza?

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Rushdi Abualouf
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Gaza correspondent in Istanbul
- Lokacin karatu: Minti 3
Hamas ta yi wa dakarunta sama da 7,000 kiranye domin ƙoƙarin samun iko da wasu yankunan Gaza da sojojin Isra'ila suka janye, kamar yadda kafofin watsa labarai na yankin suka bayyana.
Ƙungiyar ta kuma naɗa gwamnoni biyar da suke da ƙwarewar soji, daga ciki har da waɗanda suka taɓa jagorantar wasu sassan ƙungiyar.
Rahotanni sun ce ƙungiyar ta yi kiranyen ne ta hanyar tura saƙonnin kar ta kwana da ma kiran waya domin "daƙile masu taimakon Isra'ila wajen mamaye Gaza," sannan aka buƙaci mayaƙan su koma ba tare da ɓata lokaci ba.
An ce tuni mayaƙan na Hamas suka fara bazuwa zuwa sassan zirin, wasu sanye da kayan soja, wasu da shiga ta fararen kaya. Sai dai sashen hulɗa da jama'a na Hamas ya ƙaryata tura "mayaƙa zuwa titunan zirin."
An fara shiga fargaba ne bayan mayaƙan Dughmush sun harbe ƴan Hamas biyu a garin Sabra da ke birnin Gaza. Ɗaya daga cikin waɗanda aka harbe ɗin, ɗa ne ga babban kwamandan Hamas Imad Aqel, wanda yanzu yake jagorantar sashen tattara bayanan sirrin ƙungiyar.
An tsinci gawarsu ne a titin birnin, lamarin da ya haifar da fargabar Hamas za ta iya mayar da martani, wanda zai iya haifar da tashin-tashina.
Kwatsam daga bisani mayaƙan na Hamas suka mamaye wani yanki da ke tattare da mayaƙan Dughmush sama da 300 da manyan makamansu.
Daga baya Hamas ta kai hari, inda ta kashe wani ɗan Dughmush ɗaya, sannan ta yi yi garkuwa da wasu guda 30.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dama dai an yi hasashen Hamas za ta sake shiri a daidai lokacin da ake tattaunawa kan mulkin Gaza bayan yaƙin.
Wannan lamarin zai kawo tangarɗa kan zagaye na biyu na aiwatar da yarjejeniyar Trump, wadda a ciki aka ce dole Hamas ta ajiye makami.
Jami'an Hamas na ƙasashen waje sun ƙi cewa komai kan tura mayaƙa titunan Gaza, amma sun ce, "ba za mu bar Gaza a hannun ɓarayi ba, da ma ƴanbindiga da suke samun goyon bayan Isra'ila kuma suke goyon bayan mamayar Isra'ila a Gaza.
"Makaman suna da amfani ne wajenmu domin daƙile mamayar Gaza, kuma za su ci gaba da amfani matuƙar aka ci gaba da yunƙurin mamayar."
Wani tsohon soja da ya yi aiki da gwamnatin Falasɗinawa a Gaza ya ce yana fargabar Zirin zai sake shiga wani sabon yaƙin.
"Hamas ba ta canza ba. Har yanzu tana tunanin makami da hargitsi ne kaɗai hanyar tabbatar da ƙungiyar," in ji shi a tattaunawarsa da BBC.
"Makamai sun yi yawa a Gaza. An sace dubban makamai da alburusan Hamas a lokacin da ake yaƙi, sannan wasu ƙungiyoyin sun samu tallafin makamai daga Isra'ila."
Khalil Abu Shammala masanin harkokin haƙƙin ɗan'adam da yake zaune a Gaza, ya ce za a jira a gani ko Hamas za ta bar mulkin Gaza a hannun kwamitin ne ko kuma za ta kawo tsaiko kan aiwatar da yarjejeniyar.
"Lallai ƴan Gaza da yawa suna cikin fargabar rikicin cikin gida na iya ƙazancewa saboda abubuwan da ke wakana," in ji shi.
"Ina da yaƙinin cewa lallai idan Hamas ta ci gaba da nacewa sai ta kasance tana da hannu a tsaron Gaza, za ta lalata yarjejeniyar da aka tsara, kuma za ta sake jefa Gaza cikin wata wahalar," in ji shi.











