Ƙasashen da ba su da sojoji a duniya

Vatican ta dogara ne da dakarun Swiss Guard

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Vatican ta dogara ne da dakarun Swiss Guard
    • Marubuci, Walid Badran
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC
  • Lokacin karatu: Minti 6

A jawabinsa ga Majalisar Ɗinkin Duniya, Shugaban Falasɗinu, Mahmoud Abbas ya ce, "ba mu damu da kafa rundunar soji a Falasɗinu ba," inda ya yi kira ga sashen da ke riƙe da makamai a yankin da su ajiye makamansu, sannan ya nanata cewa Hamas ba ta da rawar da za ta taka a gwamnatin ƙasar.

Duk ma dai yadda aka kalla jawabin na shugaban Falasɗinun, samun ƙasashe a duniya da ba su da wata rundunar soji ba sabon abu ba ne.

Duk da cewa rundunar soji na cikin abubuwan da ke nuna ƴancin ƙasa, kuma abu ne mai muhimmanci wajen kare ƙasa da ƴancinta, akwai ƙasashen da ba su da sojoji.

Shin waɗanne ƙasashe ne haka?

Turai

A turai, babbar ƙasar da take zama ba tare da sojoji ba ita ce Iceland duk da cewa mamba ce kuma ɗaya daga cikin ƙasashen da aka ƙirƙiri NATO da su.

Tun bayan samun ƴancinta daga Denmark a 1944, ƙasar ta Iceland tana dogaro ne da wasu tsirarun ƴansanda domin samar da tsaron cikin gida, da kuma dagewa wajen ƙarfafa ƙungiyar tsaron haɗin kai ta NATO.

Kundin Encyclopædia Britannica ta ce Iceland ba ta da sojoji, amma tana da jami'an tsaron farin kaya domin tsaron harkokin cikin gida. Ta kasance mamba ce a NATO tun a shekarar 1949, sannan harkokin tsaronta na rataya wajen ƙarfafa yarjejeniyar tsaronta da Amurka da NATO wajen tsaronta da ma na sararin samaniyarta.

A shekarar 2006 ne Amurka ta rufe sansanin sojinta da ke birnin Keflavik da ke ƙasar, bayan dogon lokaci.

Da take kare matakinta na rashin soji, ƙasar ta ce harkokin tsaro na cin kuɗi sosai, kuma ƙasar ba ta girma kuma mutanenta kaɗan ne, sannan ta ƙara da cewa yankin da take a North Atlantic ya sa ba ta fuskantar wata babbar barazanar tsaro kai-tsaye.

Ƙasar dai tana cikin ƙasashen da suka fi jin zaman lafiya.

Firaministan Iceland Kristrón Mjöll Fróstadóttir

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Firaministan Iceland Kristrón Mjöll Fróstadóttir
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Akwai kuma ƙasar Vatican City State, ƙasar da aka fi sani da Vatican wadda ita ce ƙasar da ta fi kowace ƙasa rashin yawa a duniya, kuma ba ta da sojoji na kanta a ƙasar.

Maimakon sojin kanta, sai ƙasar da dogara da dakarun Swiss Guard, waɗanda suke da alhakin ba Fafaroma kariya, sannan akwai yarjejeniyar da ƙasar ke da ita da ƙasar Italiya domin samun kariya tun daga shekarar 1929, wadda ake kira da yarjejeniyar Lateran Treaty of 1929.

Rashin sojojin ƙasar ba zai rasa nasaba da kasancewar ƙasar ce hedkwatar ɗarikar Katolika, kuma ba ta da wani buri na tsaro ko siyasar duniya.

A arewacin turai kuma, akwai ƙananan ƙasashe guda huɗu da ba su da sojoji: Monaco da Andorra da Liechtenstein da San Marino.

Monaco na dogaro ne da sojojin Faransa sai kuma ƴansanda na cikin gida, ita kuma Andorra tana dogara ne da Faransa da Sifaniya.

Ita kuma Liechtenstein ta soke sojin ƙasar ne a shekarar 1868 bayan yaƙin Prussia da Austria, sai ta bar ƴansandan cikin gida.

Ita kuma San Marino ta soke sojinta a ƙarni na19 kuma ba da ta wata yarjejeniya da wata ƙasa kan tsaro, sai dai baki ɗayanta tana zagaye ne da Italiya, wanda hakan ya sa take samun tsaro daga ƙasar.

Amurka ta Tsakiya

Kundin Encyclopædia Britannica ta ce ƙasar Costa Rica da ke Amurka ta Tsakiya ta soke aikin soji a shekarar 1949 bayan yaƙin basasa, inda ta sanar da cewa ta koma cikakkiyar ƙasar dimukuraɗiyya mai zaman lafiya, sannan ta rubuta haka a sashe na 12 na kundin tsarin mulkin ƙasar cewa ƙasar babu soja.

Tun daga lokacin, Costa Rica take amfani da ƴansanda domin tsaron cikin gida, sannan take amfani da ƙawayenta na ƙasashen duniya domin tsaronta daga barazanar waje.

Shugaban Panama José Raúl Molino

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Panama José Raúl Molino

A Amurka ta Tsakiya akwai Panama, ƙasar da ta kasance ba tare da sojoji ba tun daga shekarar 1990 bayan Amurka ta kutsa ƙasar tare da kifar da gwamnatin Manuel Noriega.

An soke sojin ƙasar ne a hukumance a kundin tsarin mulkin ƙasar na 1994, sai aka kafa ƴansanda masu tsaron cikin gida da bakin iyakoki.

Ita ma Panama tana dogaro ne da ƙawayenta ƙasashen duniya wajen tsaronta da kare ta daga barazanar tsaro, musamman Amurka wadda ta ba ta amanar tsaro.

Yankin Pacific Ocean

Wasu masu rawar al'ada a ƙasar tsibirin Solomon Islands

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu masu rawar al'ada a ƙasar Tsibirin Solomon

Wasu ƙananan tsibirai da suke yankin sun zaɓi zama ba tare da sojoji ba saboda yarjejeniyar tsaro da suke da ita da Amurka da Australia da New Zealand.

Ƙasar Tsibirin Solomon Islands ta soke aikin soja ne a 2003 bayan wasu rikice-rikice da aka yi a ƙasar, sai ta koma amfani da tsaron haɗin gwiwa da ƙasashen Australia da New Zealand.

Haka Tuvalu da Kiribati duk ba su da sojoji, sai dai kawai ƴansanda masu kula da tsaron cikin gida, sai kuma tsaron da suke samu daga Australia da New Zealand.

Ita ma Nauru ba ta da sojoji, inda take dogaro kan samun tsaro daga sojojin ƙasar Australia.

Sauran ƙasashen nahiyar su ne Micronesia da Palau da Marshall waɗanda dukkansu tsibirai ne da suke dogaro da Amurka domin tsaronsu, sai kuma ƴansanda da suke tsaron cikin ƙasar.

Nahiyar Indian Ocean

Firaministan Mauritus Pravind Kumar Jugnauth

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Firaministan Mauritus Pravind Kumar Jugnauth

Mauritius tsibiri ne da ke nahiyar Indian Ocean, gabas da ƙasar Madagascar, kuma ba ta da sojoji tun lokacin da ta samu ƴanci daga Birtaniya a shekarar 1968.

Tsaron cikin ƙasar na ta'allaƙa ne a kan ƴansanda da sauran jami'an tsaron farin kaya.

Ita ma ƙasar tana dogaro ne da ƙawayenta na ƙasashen duniya domin samun kariya daga barazanar tsaro daga waje.

Yankin Caribbean

A yankin Caribbean, akwai ƙasar Grenada da Amurka ta kutsa a shekarar 1983 bayan an yi juyin mulki a ƙasar, amma yanzu babu sojoji a ƙasar.

Tana dai da rundunar ƴansanda da take kula da harkokin tsaron cikin gida a ƙasar, sannan akwai alaƙar tsaron haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen gabashin yankin da ke kula da duk wata barazanar tsaro da ke fuskantar mambobin ƙasar.

Ita ma ƙasar Dominica ba ta da sojoji sai dai ƴansanda, lamarin da ya faru bayan rikicin siyasa da aka yi a ƙasar a shekarun 1980s, inda gwamnatin ƙasar ta yanke shawarar cewa ƴansanda sun wadatar wajen kula da tsaron cikin ƙasar, sai kuma amfani da tsaron haɗin gwiwa domin fuskantar barazanar tsaro daga waje.

Ita kuma tana cikin ƙungiyar tsaron haɗin gwiwa na ƙungiyar ƙasashen gabashin Caribbean.

Ƙasashen Saint Lucia da Saint Vincent da Grenadines da Saint Kitts da Nevis ba su da sojoji, amma suna da ƴansanda.

Abin da hakan ke nufi

A jawabinsa a Majalisar Ɗinkin Duniya, Shugaban Falasɗinu Mahmoud Abbas ya ce, "ba ma buƙatar ƙsar Falasɗinu mai sojoji."

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A jawabinsa a Majalisar Ɗinkin Duniya, Shugaban Falasɗinu Mahmoud Abbas ya ce, "ba ma buƙatar ƙsar Falasɗinu mai sojoji."

Ya kamata a gane cewa ƙasashen da ba su da sojoji suna yanki ne da babu barazanar tsaro, ko kuma suna da yarjejeniyar tsaro da wasu manyan ƙasashe da suke ba su tsaro.

Wasu sun yi amannar cewa waɗannan ƙasashe suna da tsare-tsare masu kyau wanda hakan ya sa suke sauya akalar kuɗaɗen ƙasashen domin ayyukan more rayuwa.

Sai dai masu suka suna ganin ba daidai ba ne a ce ƙasa ba ta sojoji, saboda suna ganin za a iya samun matsala idan aka samu wata barazanar tsaro ko kuma guguwar siyasar duniya ta canja.

Idan aka samu tsaiko a yarjejeniyar tsaro tsakanin ƙasashen da manyan ƙasashen, za su iya samun kansu a tsaka mai wuya. Don haka tsirar irin ƙasashen na ta'allaƙa ne da zaman lafiyar ƙasashen da suke ba su tsaro.