Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa Faransa ke da sansanonin soji a Afrika?
- Marubuci, Daga Mamadou Faye
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Afrique
Yayin da ake samun yawaitar juyin mulki a tsoffin ƙasashen da Faransa ta yi wa mulkin mallaka a Afrika, Faransar ta ce ba za ta yi wasa da gudunmawar harkar soja ba a nahiyar.
Ana samun ƙaruwar masu yin zanga-zanga kan ci gaba da kasancewar Faransa a Afrika, wuraren da a baya ta girke sojojinta.
A baya-baya, an kori dakarun Faransar a Nijar da Mali, inda wasu ƙasashe ke duba yiwuwar kawo karshen yarjejeniyar da ta janyo shiga tsakanin sojojin Faransa har sau 30 tsakanin 1964 zuwa 1995.
Me ya sa sojojin Faransa suka kasance a Afrika?
Tun bayan samun ƴancin kai, Faransa na son tabbatar da ganin ɗorewar gwamnatoci", in ji Dr Bakary Sambe, darakta a cibiyar Timbuktu.
Faransar na ganin yammacin Afrika da kuma yankin Sahel a matsayin wani yanki da take da hakkin tura dakarunta kuma tana da tasiri", a cewarsa.
Farfesa Bruno Charbonneau, daga kwalejin sojoji ta Saint-Jean a Canada kuma masani kan samar da zaman lafiya da shiga tsakani kan rikice-rikice a Yammacin Afrika, ya amince cewa:
"Kasancewar sojojin Faransa a Afrika ya bai wa Faransa damar shiga tsundum a ɓangaren warware rikice-rikice a ƙasashen Afrika da ke amfani da harshen Faransanci, musamman a Kwamitin Tsaro na MDD," in ji shi.
Ya ƙara da cewa bayar da taimakon soji ga ƙawayenta a Afrika da Faransa ke yi, na nufin cewa za ta iya bijirowa da kare muradunta, da shiga tsakani na soji.
Ma'aikatar tsaron Faransar ta ce muradin da take son cimmawa da aikin soji a Gabon shi ne horar da sojoji a yankin da ƙara musu kwarin gwiwar tunkar ƴan ta'adda, da kare iyakokinta na ƙasa da kuma na ruwa. Wannan ya kunshi aikin wanzar da zaman lafiya, da tattara bayanan sirri da kuma samr da kayayyakin soji.
Ta ce hakan na cikin tsarin shirin ƙarfafa dakarun wanzar da zaman lafiya a Afrika, wani horo da aka kirkiro a shekarun 1990 wanda ya kunshi ƙasashen Faransa, da Birtaniya da kuma Amurka.
A Senagal, Faransa ta ce tana aikin horas da sojoji a faɗin ƙasashe 15 mambobin Ecowas, haɗa da makwabta Mauritania.
Waɗanne ƙasashe ke da sansanonin sojin Faransa har yanzu?
Duk da cewa yawan ƙasashen da ke ɗauke da sansanonin sojin Faransa sun ragu a baya-bayan nan, sai dai har yanzu akwai wasu ƙasashe da dama da dakarun ke ci gaba da zama kamar:
- Chad: Akwai sojojin Faransa kusan 1,000 a ƙasar, waɗanda ake kira (EFT), an ɗora musu alhakin kare muradun Faransa da ƴan ƙasar. Da kuma taimakawa sojojin Chadi da kayayyakin yaƙi da kuma bayanan sirri, suna kuma cikin ɓangaren kakkaɓe ayyukan ƴan ta'dda. Suna da sansanoni a N'Djamena, babban birnin ƙasar, da birnin Abéché da ke gabashi, da wani karamin sansani a Faya da ke arewacin ƙasar.
- Djibouti: Ƙasar ta dogara da taimakon Faransa. A yanzu, akwai sojojin Faransar 1,500 a ƙasar waɗanda aka cimma yarjejeniyar kasancewarsu tun 1997, lokacin da ƙasar ta samu ƴancin kai, da kuma 2014.
- Gabon: An girke sojojin Faransa a ƙasar tun bayan samun ƴancin kai a 1960 da kuma 2014 waɗanda suka kai 350. A cewar ma'aikatar tsaron Faransa, sansanin yana a Libreville, babban birnin ƙasar da wani sansani na sojin sama.
- Ivory Coast: Ta kasance gida ga ayyukan sojin Faransa. An kafa wani sansani a can a 2015 karkashin haɗin gwiwar tsaro da ƙasashe da ke kusa. An tura dakaru 950 a matsayin ɓangare na wani samame mai suna Operation Licorne tsawon shekaru 15 baya. An kafa sojojin wanzar da zaman lafiyar na Faransa ne gabanin ɓarkewar yaƙin basasar ƙasar a 2002.
- Senegal: Ƙasar tana ɗauke da sojoji kusan 400, waɗanda aka tura tun 2011, suna taimakawa a aikin horas da sojoji. Akwai sansanoni biyu a Dakar, babban birnin ƙasar, inda kuma suke amfani da filin jirgin sama na sojojin ƙasar. Sojojin suna kuma da wani gidan rediyo da ke watsa shirye-shirye a birnin Rufisque kusa da Dakar.
A watan da ya gabata, sojoji 1,300-1,500 da aka tura Nijar, haɗe da jiragen sama na yaƙi da kuma na marasa matuki da ke aikin kakkaɓe ƴan ta'adda, suka fara janyewa daga sansanoni uku bayan buƙatar ficewarsu da sojojin da suka yi juyin mulki suka yi.
Me ya sa Faransa ta riƙe bayan gidanta?
Afrika ta bai wa Faransa ikon gaske a idon duniya, a cewar Farfesa Tony Chafer, malami a jami'ar Portsmouth da ke Birtaniya.
"Yayin da ake ƙara samun ƙasashe masu karfin iko da ke gogayya a duniya, Faransa na da muradi na siyasa wajen ganin dakarunta sun ci gaba da zama a yankin Afrika," in ji shi.
Ya ce kasancewar sojojin Faransa a Afrika ya taka rawa wajen tabbatar da kujerarta na dindindin a Kwamitin Tsaro na MDD - Faransa na da babbar rawa da take takawa idan aka yi maganar batun tsaro a Yammaci da kuma Tsakiyar Afrika a MDD ko kuma a al'ummomin ƙasashen waje.
Faransa ta yi taka tsan-tsan a ɓangaren hulɗar tattalin arziki da kuma dangantaka a Afrika. An ga hakan a samar da kuɗin CFA, waɗanda ake kyautata zaton sun bunƙasa baitul-malin Faransa, da kulla alaƙa ta kut-da-kuta da manyan masu mulki.
Me ya sa masu zanga-zanga ke son dakarun Faransa su fice?
"Sojojin Faransa ku tafi. Ku fice mana," kamar yadda wani mawakin raggae ɗan ƙasar Ivory Coast Alpha Blondy ke rerawa a wakarsa a shekarun 1990. An yi wakar ne a lokacin da aka buɗe wani sabon babi na ƴanci a ƙasar.
Duk da ƙaruwar ayyukan masu ikirarin jihadi a Yammacin Afrika, Faransa ta ɗauki buƙatar tura ƙarin dakaru.
Aikin soji na farko shi ne na Operation Serval, wanda aka kaddamar a Mali bayan da masu iƙirarin jihadi suka sake karɓe iko da arewacin ƙasar a 2012. An maye gurbin shi da wani samame mai suna Operation Barkhane, wani shirin yankuna da aka kafa don yaƙi da masu ta da ƙayar baya wanda aka kawo karshensa a watan Nuwamban 2022.
Dr Sambe ya ce dukkansu sun ƙasa samun nasara bayan da ƙungiyoyin ƴan ta'dda suka ninƙa a wannan lokaci.
"Ƙasashe sun fara shakkar muhimmancin kasancewar sojojin Faransa - akidoji da zargin kitsa makarkashiya ya taso da ke nuna cewa suna ɗan jan hankali ko kuma ƙara rura wutar rikicin ta ƴan ta'adda," in ji shi.
Wannan haɗe da kiraye-kirayen "samun ƴanci" da ke fitowa daga matasa na nufin cewa mutane da yawa na son ganin bayan sojojin Faransa.
Juyin mulki da aka samu a baya-bayan nan a ƙasashen Mali, da Burkina Faso, da kuma Nijar - inda sojojin suka yanke shawarar korar sojojin Faransa da shan yabo wurin al'umma - na cikin irin buƙatar da ake da ita na ganin ficewarsu.
Me zai iya biyo baya?
Sojojin Faransa sun janye daga Mali a shekarar da ta gabata bayan umarni da shugabannin mulkin soji suka bayar a Bamako, babban birnin ƙasar, kuma sun faɗa wa dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD su ma su fice.
Yayin da suke ficewa, hakan zai karyawa wasu gwiwa, ko da kuwa yanayin tsaro ya taɓarɓare cikin shekaru goma da suka gabata, in ji Farfesa Chafer.
Tun bayan janyewar, take hakkin bil'adama ya ta'azzara, kuma a halin yanzu 'yan Mali ba su da tsaro, in ji shi.
A halin da ake ciki dai sojojin ƙasar Mali sun koma neman taimakon ƙungiyar wajen sojojin hayar Rasha na Wagner a matsayin wani ɓangare na sabuwar kawance.
Ana zargin ɓangarorin biyu da laifukan cin zarafin bil adama.
Farfesa Chafer ya yi imanin cewa babbar rawar da Wagner ke takawa a ƙasar "ba don inganta tsaron jama'a ba ce, amma don tallafawa gwamnatin sojin Mali".
Da alama kuma ta wargaza yarjejeniyar zaman lafiya da ƙawancen 'yan tawayen kabilar Abzinawa, wanda kuma ta fara kwace yankuna a arewacin ƙasar yayin da dakarun ƙasashen waje suka janye.
Ko akwai madadin hanyar samun tsaro?
Ƴan kwangila, da mayakan sa-kai masu kare kansu da ƙungiyoyin sa-kai, kamar Wagner, ba su ne mafita ba, in ji Dr Sambe, yana mai nuni da ƙasar Mali a matsayin misali.
Yana son ganin haɗakar sojoji daga Ecowas, Tarayyar Afirka da sauran rundunonin tsaro na nahiyar.
"Lokaci ya yi da za a matsa zuwa ga yadda sojojin Afirka za su kasance a Afirka," in ji shi.