Toni Kroos zai koma bugawa Jamus wasanni

fg

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan tsakiyar Real Madrid Toni Kroos zai koma bugawa ƙasarsa Jamus wasa.

Dan wasan ya ce zai bugawa ƙasar wasan gasar Europe 2024.

Kroos mai shekara 34, yana cikin tawagar da ta lashe wa Jamus Kofin Duniya a 2014. Kuma ya ci wasa 106 cikin wasannin da ya buga mata.

Ya yi ritaya a watan Yulin 2021 amma yanzu ya janye matakin da ya ɗauka a baya bayan ya tattauna da kocin Jamus din na yanzu Julian Nagelsmann.

"Zan ci gaba da bugawa Jamus a karo na biyu daga watan Maris. Saboda me? Mai horaswa ne ya nemi na yi hakan, shi ne na amince," kamar yadda Kroos ya wallafa a shafinsa na Instagram.

"Ina da tabbacin tawagar da za ta halarci gasar Europe din za ta taka rawa sama da ta zarce wadda ake tsammani".

A yanzu da yake wasa ya lashe Bundesliga da La Liga sau uku, baya ga lashe gasar Champions sau biyar.

Haka kuma ya samu nasarar lashe kofin duniya, kuma yana cikin tawagar Jamus da ta ƙare gasar duniya a matsayi na uku a 2010 kuma ta je wasan kusa da ƙarshe a 2012.

Sabon kocin ƙungiyar Nagelsmann ya zaɓe shi ya zama cikin tawagar da za ta buga wasan sa da zumunta da Faransa da Netherland.

Jamus za ta fafata da Scotland a filin wasa na Allianz Arena a Munich a matsayin wasan farko na Europe 2024 da za a fara ranar Juma'ar 14 ga watan Yuni.