Man United tana nan ta takwas a teburi duk da cin Newcastle

Manchester United ta doke Newcastle United 3-2 a kwantan wasan Premier League mako na 34 ranar Laraba.

United ta fara cin kwallo ta hannun Kobbie Mainoo a minti na 31 da fara wasa, sai dai Anthony Gordon ne ya farke, bayan da suka koma zagaye na biyu.

Amad Diallo ne ya kara ci wa United kwallo na biyu, sannan Rasmus Hojlund ya kara na uku, saura minti shida a tashi wasan.

Sai dai kuma daf da za a tashi daga karawar United ta farke na biyu ta hannun Lewis Hall.

Da wannan sakamkon United tana matakinta na takwas da maki 57, iri daya da na Newcastle United ta bakwai.

Tuni dai Chelsea ta koma ta shidan teburi da maki 60, bayan da ta yi nasarar cin Brighton 2-1 a kwantan wasan mako na 34.

Ranar 19 ga watan Mayu za a buga wasannin karshe a kakar bana, inda Newcastle United za ta je gidan Brentford.

Ita kuwa United za ta kara da Brighton, yayin da Chelsea za ta karbi bakuncin Bournemouth a Stamford Bridge.

Wasu batutuwan da ya kamata ku sani kafin wasan da suka kara:

Wasa daya Newcastle ta yi nasara a kan Manchester United a Old Trafford a karawa 28 a Premier League shi ne 1-0 a Disambar 2013.

Kungiyar da Eddie Howe ke jan ragama ta yi nasara a wasa uku baya da suka kara a dukkan fafatawa.

Rabon da Newcastle ta yi nasara a kan United gida da waje a Premier League tun bayan 1930-31.

Manchester United

An doke Manchester United wasa 14 a lik a kakar nan, karon farko tun bayan da ta yi rashin nasara 16 a kakar 1989-90.

Wasa daya aka doke ta a gida na karshen da za a rufe gasar Premier League daga 16 shi ne wanda Cardiff City ta yi nasarar 1-0 a 2018-19.

United ta bari kwallo 82 ya shiga ragarta, karon farko da aka dura mata kwallaye da yawa tun bayan 1970-71.

Rasmus Hojlund ya ci kwallo daya a wasa takwas a lik a karawa takwas, bayan da ya zura bakwai a raga a wasa shida baya.

Newcastle United

Newcastle ta ci wasa bakwai a waje a lik, bayan da ta yi nasara daya daga karawa 10 da fara kakar bana da yin canjaras biyu da rashin nasara bakwai.

Newcastle na fatan zama cikin 'yan shidan teburi a Premier League karo na biyu a jere tun bayan da ta yi uku daga 2001-02 zuwa 2003-04 karkashin Sir Bobby Robson.

Newcastle United ta ci kwallo14 da ƴan wasan da suka shiga canji suka ci mata, saura ta kara daya ta kafa tarihi a wannan fannin.

Alexander Isak ya ci kwallo 20 a kakar nan, ɗan wasan Newcastle United na farko tun bayan Alan Shearer da ya zura 22 a 2003-04.