Abu biyar da ya wakana a taron sauyin yanayi na COP29

    • Marubuci, Matt McGrath
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Environment correspondent
  • Lokacin karatu: Minti 6

An kammala taron sauyin yanayi na COP29, inda ƙasashe masu tasowa suka yi ƙorafin cewa dala biliyan 300 da aka ware a shekara domin ba su a 2035 cewa ta yi kaɗan.

Ƙasashe masu arziki da suka halarci taron da aka yi a Azerbaijan sun yi mamakin jin cewa ƙasashe masu tasowa sun ce kuɗin ya yi kaɗan, abin da suke gani a matsayin maƙudan kuɗaɗe.

Sai dai hakan cigaba ne - kan dala biliyan 100 da suke tallafawa da farko a duk shekara.

Sai dai, ƙasashen duniya, waɗanda suka yi hoɓɓasa don ganin an ƙara yawan kuɗin, na da batutuwa da dama da ake son warwarewa da kuɗaɗen.

Ƙara kuɗin cigaba ne, amma har yanzu kawuna a rabe suke

Akwai korafe-korafen cewa kuɗin da aka ware ya yi kaɗan, kuma wasu kamar bashi aka bayar.

Kuma matalautan ƙasashe sun nuna ɓacin-ransu ta yadda suka ce sai da aka kai maƙura kafin ƙasashe masu arziki suka bayyana abin da za su bayar.

"Kuɗin ya yi kaɗan," kamar yadda wakilin Indiya a taron ya faɗa wa sauran wakilai, bayan da aka amince da kuɗaɗen da za a bayar.

"Wannan daftari ya yi kaɗan matuka. Wannan, a ra'ayinmu, ba zai shawo kan matsalolin sauyin yanayin da muke fuskanta ba."

Daga karshe, ƙasashen masu tasowa sun amince su karɓi kuɗin, inda ƙasashe masu arziki da yawa suka yi nuni da batun zuwan Shugaba Donald Trump a shekara mai zuwa, wanda ya kasance yana da tababa kan sauyin yanayi, inda suka ce ba za su samu cimma yarejejeniya da ta kamata ba.

Sai dai an soki wannan tallafi a matsayin cewa babu wani abin kirki da zai haifar.

An ƙalubalanci cewa idan kana son saka duniya ta zauna lafiya daga ƙaruwar sauyin yanayi, to dole ne ƙasashe masu arziki su taimaka wa masu tasowa domin rage gurɓatacciyar iska, saboda nan ne aka fi samun ƙaruwar ɗumamar yanayi a cikin shekaru goma da suka wuce.

Ana sa ran wallafa sabon tsarin yanayi a watan Maris zuwa Yunin shekara mai zuwa domin fito da yadda ƙasashe za su taƙaita fitar da gurɓatacciyar iska cikin shekara goma da ke tafe.

Idan da an samu ƙarin kuɗaɗe da suka fi na yanzu a taron na COP29, to da hakan zai taimaka ainun wajen ƙara ƙoƙari da ake yi a ɓangaren sauyin yanayi.

Kuma a daidai lokacin da ake samun rashin tabbas na siyasa, haɗa kan ƙasashe a kan sauyin yanayi zai zama da wuya.

Saɓani kan kuɗi ya sake kunno kai kan daɗaɗɗiyar matsalar rarrabuwar kai da ake da ita a tsakanin ƙasashe masu arziki da matalauta, tare da ɓacin-rai da kuma gaba da ban taɓa gani ba cikin shekaru.

Taron duniya kan sauyin yanayi (COP)na tsaka-mai -wuya

Janyo hankalin ƙasashe kusan 200 domin su amince da yarjejeniyar tallafi kan sauyin yanayi abu ne mawuyaci.

Amma ga Azerbaijan, mai masaukin baƙi, ƙasar da a tarihi ba ta taɓa shiga wani batu na sauyin yanayi ba, lamarin ya kasance kamar ya fi ƙarfinta.

Shugaban ƙasar, Ilham Aliyev, bai taimaka ba a nasa ɓangare ta hanyar kwatanta mai da iskar gas a matsayin "kyauta daga Allah".

Maganganunsa - ta hanyar zargin "kafafen yaɗa labaran Yamma", ƙungiyoyin agaji da kuma ƴan siyasa da yaɗa labaran ƙarya, sun ƙara dagula al'amura.

Azerbaijan ta bi sahun Masar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a matsayin ƙasa ta uku a jere da ke bin tsarin kama-karya wajen karɓar baƙuncin taron sauyin yanayi na duniya( COP), abin da ya sa tababa kan yadda ake zaɓar ƙasa da za ta karɓi baƙuncin taron.

Azerbaijan, kamar UAE, na da tattalin arziki ne da ta samu daga ɓangaren fitar da mai da iskar gas, wanda ke nuna shakku kan yiwuwar taimaka wa duniya sauyawa daga ɓangaren mai, da iskar gas da kuma gawayi.

Manyan masu shiga tsakani sun nuna ɓacin ransu kan abin da wasu suka ayyana da taron COP mafi muni cikin shekara goma.

Jim kaɗan bayan fara taron ne, shugabannin sauyin yanayi da dama suka rubuta wasiƙa inda suka ce taron COP ba shi da wata manufa tare da neman a kawo sauyi.

Rashin jin muryar China a taron bana

Yayin da rawar da Amurka za ta ka taka a ɓangaren yaƙi da sauyin yanayi a gaba ke cikin ƙila-wa-ƙala saboda zuwan Trump, hankali ya karkata ga wanda zai iya zama jagoran sauyin yanayi idan Amurka ta fice cikin shekaru huɗu masu zuwa.

Ana sa ran cewa China ita za ta zama jagora a ɓangaren.

Ba a ji ɗuriyar ƙasar ba da ke sahun gaba wajen fitar da iska mai ɗumama yanayi (carbon) a taron sauyin yanayi na bana ba, inda kawai wakilinta ya ɗaga hannu kawai don bada cikakken bayani a karon farko kan adadin kuɗaɗen da take bai wa ƙasashe masu tasowa.

Har yanzu Majalisar Ɗinkin Duniya na ɗaukar China a matsayin "ƙasa mai tasowa", abin da ke nufin ba ta da wani hakki a hukumance na kula da rage hayaki mai gurɓata muhalli ko kuma ba da taimakon kudi ga ƙasashe matalauta.

Duk da haka, ƙasar China ta amince a cikin yarjejeniya da aka cimma, inda za ta samu damar kiɗaya gudummawar da ta bayar a cikin asusun bai-ɗaya na ƙasashe masu fama da sauyin yanayi.

Gaba-ɗaya, ana ganin matakin a matsayin mai tasiri.

"China na ƙara fito da gaskiya game da tallafin kuɗi ga ƙasashen kudancin duniya." in ji Li Shuo, na cibiyar nazarin manufofin jama'ar Asiya.

"Wannan ya kamata ya sa ƙasar ta taka rawar gani a nan gaba."

Shakkun Trump kan sauyin yanayi

Duk da cewa babu Trump a taron COP, amma an ji alamun kasancewarsa.

Wani abu da ya ja hankalin masu shiga tsakani a Baku shi ne buƙatar tabbatar da cewa gwamnatin Trump ta biyu ba za ta inganta tattaunawar sauyin yanayi na tsawon shekaru ba.

Don haka ba abin mamaki ba ne ganin cewa ƙasashe masu arziki sun so su ƙuduri aniyar samar da kuɗaɗe nan da shekarar 2035.

Sun yi imanin sanya lokacin zai bai wa Amurka damar sake bayar da gudunmawa da zarar Trump ya bar mulki.

Haka-zalika, yunƙurin haɓaka tushen masu bada gudummawa an yi shi ne da sanya tunanin Trump.

Za a yi amfani da kawo ƙasar China a lamarin, ko da a matsayin wucin-gadi, don nuna cewa ya dace ta shiga tarukan ƙasa da ƙasa kamar COP.

"Ba wanda ke tunanin Trump a Fadar White House zai zama wani abu mai illa da haifar da koma-baya ga tsarin sauyin yanayi," in ji Farfesa Michael Jacobs, wani babban jami'in cibiyar bincike ta ODI Global.

"Amma wannan yarjejeniya ta kasance game da ƙoƙarin takaita ɓarnar yadda ya kamata."

Masu fafutuka sun yi ta eho a taron na duniya

Ɗaya daga cikin abin da aka fi gani a COP29 shi ne matakin da wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu na muhalli da masu fafutuka suka ɗauka.

Ni kaina na ga lokacin da aka kori wakilin Amurka kan sauyin yanayi John Podesta daga wani wurin taro tare da rera waƙoƙin “ka ji kunya” a kunnensa.

Yawancin ƙasashe masu tasowa sun dogara ga waɗannan ƙungiyoyi masu zaman kansu don tallafi domin tunkarar al'amura masu wuya kamar sauyin yanayi - COP.

A yayin tattaunawar, yawancin waɗannan masu fafutukar sun ƙi amincewa da kusan kowace yarjejeniya.

Haka-zalika, a zauren taron na ƙarshe lokacin da dukkan ƙasashe suka amince da kuɗin da za a bayar, an yi ta jin ihu lokacin da masu magana daga ƙasashe da yawa suka yi tir da yarjejeniyar, bayan sanarwar.

Shin gwagwarmayar adawa da muhawara za ta zama sabon al'ada a taron sauyin yanayi na diflomasiyya?

Dole ne mu jira taron COP na gaba domin ganin haka.