Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gwamnatin Tinubu na daukar matakan murkushe 'yan hamayya — Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, ya gargadi gwamnatin kasar da ta guji yin amfani da miyagun matakai don murkushe 'yan hamayyar siyasarta.
Tsohon mataimakin shugaban Najeriyar, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta PDP a zaben shekara ta 2023, ya ce gayyatar da 'yan sanda suka yi wa tsohon gwamnan jihar Kaduna, kuma wani jigo a jam'iyyar hadaka ta ADC, Malam Nasir El-Rufai, da wasu hare - hare da aka kaddamar kan wasu masu banbamcin ra'ayi da gwamnatin kasar, tamkar wani tsararren farmaki ne mai matukar hadari ga 'yan adawa.
Atiku Abubakar, ya bayyana damuwa, game da wasu take-take da yake ganin kamar wani kisan mummuke ko bi-ta-da-kulli ne ake yi wa mutanen da suka yi hannu riga da ra'ayi ko goyon bayan gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
AbdurRashid Shehu Sharada, mataimaki na musamman kan kafafen yada labarai ga tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar, ne ya shaida wa BBC cewa al'ummar Najeriya ko wa na ganin yadda shugaban Najeriya Bola Tinubu, ke ta kokarin ganin cewa a zaben 2027 ba za a samu wata jam'iyyar adawa da zata yi takara ba.
Ya ce," Idan aka duba za a ga cewa a yanzu dukkanin jam'iyyun adawa a Najeriya ba su taba shiga irin yanayin da suke ciki ba saboda jam'iyya mai mulki na amfani da wasu hanyoyin domin ganin cewa an samu rarrabuwar kai da rashin fahimtar juna a cikin wadannan jam'iyyu."
"Idan aka duba irin abin da ya faru da tsohon ministan shari'a na Najeriya wanda aka kai wa hari a jihar Kebbi har aka raunata magoya bayan jam'iyyarmu ta ADC da dama, kowa ya san wannan adawa ce karara." In ji AbdurRashid Shehu Sharada.
Mataimaki na musamman kan kafafen yada labarai ga tsohon Atiku Abubakar, ya ce," Akwai taron dattawa na jihar Katsina wanda aka kira domin a tattauna matsalar tsaro da jihar ke fama dashi bisa jagorancin Usman Bugaje, shi ma a wannan taron an turo 'yan bangar siyasa domin hana wannan zama."
Mai Magana da yawun Atiku Abubukar, ya ce matsalar ba a nan kadai ta tsaya ba domin akwai abin da ya faru wanda muka ga to lallai abin na neman wuce gona da iri.
Ya ce," Abin da ya faru a yayin taron jam'iyyar ADC wanda tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai,ya jagoranta a gaban jami'an tsaro aka turo wasu mutane suka je suka tayar da zaune tsaye amma babu wanda aka kama ko kuma wani mataki da aka dauka amma sai gashi abin kunya wai hukumar 'yan sandan Najeriya ta gayyaci Malam Nasir El-Rufai, da wasu 'yan jam'iyyun adawa domin su amsa tambayoyi."
To sai dai kuma Abdul'Aziz Abdul'Aziz, mai magana da yawun shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya ce bai ga abin korafi ba a nan.
Ya ce," Na farko dai babu wani ko wata ko jami'in gwamnati da zai musgunawa wani a kyale shi, batun gayyatar da 'yan sanda suka yi wa Malam Nasir El Rufa'I, wannan ba abu ne da za a ce an musgunawa mutum ba domin ai an ji kalama da ya yi a yayin wani taro da suka yi a Kaduna, da kuma yadda suke yawo da mutane dauke da makamai wanda dole doka ta yi hukunci akai."
Sannan kuma abubuwan da suka faru a game da harin da aka kai wa tsohon ministan shari'a a Kebbi da taron da aka yi a Katsina, babu hannun gwamnati a ciki, in ji Abdul'Aziz Abdul'Aziz.
Masana harkokin siyasa dai na ganin ya zama wajibi bangaren gwamnati mai ci da na 'yan adawa su rika sara suna duban bakin gatari a takon rawar da suke yi a fagen siyasar Najeriya.