Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙasashen da suka sha da ƙyar zuwa zagayen ƴan 16 a gasar Afcon 2023
A ranar Laraba aka kammala karawa a matakin rukuni na gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta nahiyar Afirka 2023, da ke gudana a ƙasar Ivory Coast.
Karawar ta matakin rukuni ta bayar da mamaki kasancewar wasu daga cikin ƙasashen da ake tunanin za su iya lashe kofin sun gaza taɓuka abin kirki.
Bayan kammala karawar ta rukuni, wasu ƙasashe sun tsallake cikin sauki wasu da ƙyar wasu kuma an ɓaro su.
Akwai waɗanda Allah ya yi wa gyaɗan-dogo sanadiyyar wasu sabbin tsare-tsare da Hukumar kula da ƙwallon ƙafa ta Afirka (Caf) ta ɓullo da su.
Cikin irin waɗannan ƙasashe akwai mai masaukin baƙi Cote d’Ivoire da Guinea da Mauritaniya da kuma Namibiya waɗanda duk da sun zo a matsayi na uku cikin rukuni, sun samu zuwa mataki na gaba.
Ƙasashen huɗu su ne ake kira a turance ‘best losers’.
Ƙasashen da suka tsallaka zuwa zagayen ƴan 16
Ƙasashen su ne:
- Equatorial Guinea
- Nigeria
- Cape Verde
- Egypt
- Senegal
- Cameroon
- Guinea
- Angola
- Burkina Faso
- Mauritania
- Namibia
- DR Congo
- Ivory Coast
- South Africa
- Morocco
- Mali
Yadda ake fafatawa a gasar
Za ku iya duba yadda ƙasashen da suka kai zagayen ƴan 16 za su kara da kuma sakamakon dukkanin wasannin da aka buga a ƙasa.