Me zai faru idan jam'iyyu a Kano suka ƙi cimma yarjejeniyar zaman lafiya a zaɓen 2023?

Abba Kabir Yusuf da Nasiru Gawuna

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto, 'Yan takarar gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf na NNPP (hagu) da Nasiru Gawuna na APC mai mulki sun fara yaƙin neman zaɓensu
    • Marubuci, Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja

An kaɗa gangar siyasa a Najeriya, kuma tuni al’amura suka ɗauki ɗumi kafin babban zaɓe na watan Fabarairun 2023.

Zafafan kalamai da na tunzura mabiya da rura wutar ƙiyayya, na cikin abubuwan da ke damalmala al’amura a Najeriya duk lokacin da zaɓuka suka ƙarato.

Ga mabiya siyasar Najeriya, sun sani cewa Kano - jihar da ta fi yawan al'umma a Najeriya a cewar ƙidaya ta 2006 - na daga cikin jihohin da siyasarsu ta fi zafi da ɗaukar hankali.

Wannan ne ya sa a ƴan shekarun baya-bayan nan aka samar da wani tsari na sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin jam’iyyun ƙasar gabanin zaɓuka.

Sai dai babbar jam'iyyar hamayya ta NNPP a Kano na barazanar ƙaurace wa yarjejeniyar a wannan karon idan hukumomi ba su kama tare da hukunta shugaban jam'iyyar APC Abdullahi Abbas ba, wadda ke mulkin jihar.

Tun a watan Satumba dukkan 'yan takarar shugaban ƙasa suka sanya hannu kan irin wannan yarjejeniya da zummar yin yaƙin neman zaɓe cikin kwanciyar hankali gabanin babban zaɓen.

Akwai irin wannan yunƙuri a jihohi 36 na Najeriya.

'Yadda APC da NNPP ke barazana ga zaman lafiyar Kano'

Shugaban NNPP da na APC

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto, Shugaban APC Abdullahi Abbas (hagu) da na NNPP Haruna Umar Doguwa duka sun yi barazanar cin zaɓe "ko da tsiya ko da tsiya-tsiya"

Wani abu mai kama da ɗumamar yanayi ya kunno kai a siyasar ta Kano sakamakon barazanar da wasu jam'iyyun hamayya suka yi na ƙaurace wa yarjejeniyar zaman lafiya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Jam'iyyar NNPP ta yi barazanar ƙin saka hannu kan yarjejeniyar saboda abin da ta kira "kalaman tayar da fitina" da shugaban APC mai mulkin Kano ya yi cewa sai sun ci zaɓe "ko da tsiya ko da tsiya-tsiya."

"Mu a tsarinmu, ba za mu yarda mu shiga yarjejeniyar da idan aka taɓa mu mun kai maƙurar da ba za mu iya ƙyalewa ba," a cewar Shugaban NNPP na Kano Umar Haruna Doguwa.

Ya ƙara da cewa: "Ba a cizon mutum a rami sau biyu, duk wanda aka ciza a rami sau biyu kuma ya ƙyale ya zama sakarai wanda bai san abin da yake yi ba."

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ba za su kai ƙara kotu ba, sai ya ce "wannan aikin 'yan sanda ne saboda a gabansu ya faɗa."

Shugaban na NNPP na wannan batu ne bayan shi ma ya yi barazanar cewa za su aikata tsiya-tsiyar kamar yadda APC ta ce za ta yi.

"Wannan maganar da na yi ta nuna cewa ni muminin ne kenan, an sare ni sau biyu na ce ban yarda ba," a cewarsa. "In dai wannan hanyar ake bi a yi nasara to mu ma za mu bi ta don mu yi nasara."

______________________

Siyasar Kano a taƙaice:

  • Kano na da adadin masu rajistar zaɓe 5,927,565 - kashi 6.34 ke nan cikin 100 na masu zaɓe a Najeriya.
  • Tun daga 1999 zuwa 2023 Rabiu Kwankwaso da Ibrahim Shekarau da Umar Ganduje ne kawai suka mulki Kano - shekara takwas-takwas kowannensu.
  • Nasiru Gawuna ne ɗan takarar APC mai mulki da ke samun goyon bayan Gwamna Ganduje.
  • Abba Kabir Yusuf ne ɗan takarar NNPP mai samun goyon bayan tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso.
  • Ganduje ne mataimakin Kwankwaso tsawon shekara takwas da suka yi a kan mulki - 1999 zuwa 2003 da kuma 2011 zuwa 2015.
  • A watan Mayun 2022, Ibrahim Shekarau ya koma NNPP daga APC, sannan ya koma PDP a watan Agusta.
  • Abba Kabir Yusuf da Abdullahi Abbas maƙwabtan juna ne a unguwar Ciranci da ke tsakiyar birnin Kano - akwatin zaɓensu ɗaya.
  • INEC ta bayyana Sadiq Wali a matsayin ɗan takarar PDP, kodayake Mohammed Abacha na ƙalubalantar matakin a gaban kotu.
  • Dukkan tsoffin gwamnonin uku sun taɓa yin aiki da juna a jam'iyyun APC da PDP da NNPP kafin su raba gidaje.

______________________

Ko da tsiya, ko me zai faru sai mun ci zaɓe - Shugaban APC

Har yanzu ɓaɓatun da Shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas ya yi ba su daina jan hankalin 'yan ƙasa ba, musamman a shafukan sada zumunta.

"Ko da tsiya ko da tsiya-tsiya, ko ana ha-maza ha-mata, ko me za a yi, ko me zai faru, ko mai ta fanjama fanjam sai mun ci zaɓe," in ji Abdullahi Abbas.

Shugaban jam'iyyar, wanda ake yi wa laƙabi da ɗan sarki - ya yi kalaman ne yayin da suke ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe na takarar gwamna a Ƙaramar Hukumar Gaya.

A bayyane take ciyaman ɗin yana sane da cewa kalaman da yake yi ba su dace ba amma duk da haka sai ya faɗa.

Kafin ya fara ɓaɓatun sai da ya ce: "...ina tabbatar muku cewa wannan alama ce ta cin zaɓe. Wannan karon, duk da cewa an ce na daina faɗa, ko da tsiya..."

Daga baya ciyaman ɗin ya faɗa wa BBC Hausa cewa "kalamai ne na 'yan siyasa kuma ban yi don na tayar da fitina ba."

Da ma Abdullahi Abbas ba baƙo ba ne wajen yin kalamai irin waɗannan, har ma laƙabi ake yi masa da "ko da tsiya" saboda makamantansu da ya yi gabanin babban zaɓen 2019.

Yayin da jam'iyyarsu ta APC ke fuskantar babbar barazana a zaɓen 2019, Abdullahi Abbas ya nemi matasa su tabbatar cewa jam'iyyarsu ta yi nasara, yana mai barazanar korar duk ɗan sandan da ya kama su daga aiki.

"Sai dai ba mu sani ba ko za a iya kai mutum ofishin 'yan sanda, amma ina tabbatar muku ko wane ne za mu sake shi, kuma ba zancen zuwa Bompai (hedikwatar 'yan sanda a Kano), kuma ɗan sandan da ya yi kamun idan bai yi sa'a ba ya bar aiki," kamar yadda ya faɗa wa matasan.

Cikin sowa da yi masa kirari, Abdullahi Abbas ya ci gaba da cewa: "Ina tabbatar muku za mu kare mutuncinku. Zaɓen nan ko da tsiya-tsiya sai mun ci shi."

Me kalmar tsiya-tsiya ke nufi?

Abba Kabir Yusuf
Bayanan hoto, Abba Kabir Yusuf na PDP (na biyu daga hagu) tare da Gwamna Ganduje (na biyu daga dama) yayin saka hannu kan yarjejeniyar gudanar da kamfe cikin kwanciyar hankali a zaɓen 2019

Asalin kalmar "tsiya" a harshen Hausa na nufin rashi, a cewar Farfesa Aliyu Muhammad Bunza na Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto. "Wato rashin abin yi, ko rashin aikin yi," in ji shi.

"Idan kuma aka yi amfani da kalmar a ɓangaren 'yan siyasa ko 'yan banga, ana nufin za su ƙwace akwatin zaɓe ko ƙarin ƙuri'a ko yin maguɗi duka domin su ci zaɓe ta kowace hanya," kamar yadda masanin harshen ya bayyana.

"Ita tsiya-tsiya da kalmar tsiya aka samo ta, kuma tana nufin duk wani abu da ba na arziki ba," a cewar wani masanin harshen Hausa a Jihar Kano da muka ɓoye sunansa saboda tsaro.

"Ma'ana mutum zai bi wata hanya da ta haɗa da ta arziki ko kuma ta rashin kyautawa wajen cimma wani burinsa.

"Kalmar tsiya-tsiya kuma na nufin duk hanyar da ba ta dace ba ma ita zai bi wajen samun abin da yake nema, ba a saka arzikin ba ma a ciki.

"Ana yin amfani da karan ɗori a haɗa kalma biyu a Hausa don nuna jam'in abu. Misali, "tsiya-tsiya" na nufin kwarzanta tsiya da kuma yadda tsiyar ta kai matuƙa gaya".

A taƙaice dai, in ji Farfesa Bunza, kalmar "tsiya" ba ta da wata ma'ana fiye da tashin hankali ko fitina a wannan janibin.

Ta banjama-banjam kuma fa?

Kazalika, an ji Abdullahi Abbas na cewa "komai banjama-banjam" lokacin da yake bayyana hanyoyin da za su bi don su ci zaɓe.

Farfesa Bunza ya ce: "Idan aka kwatanta mutum da 'ta banjama' ana nufin mutum wanda ba ya jin kunyar a gan shi yana aikata assha [abin-ƙi].

"Idan aka ce tabanjama-banjam kuma, wato ana nufin abin za a aikata abin da ake nufi kenan - za a aikata tabanjama abin da ke nufin duk wani aikin da bai dace ba."

Tuni abin da ake gudu ya fara faruwa

Bayanan da BBC ta tattara sun nuna cewa bayan Abdullahi Abbas ya yi waɗancan kalamai a ranar Laraba, 23 ga watan Nuwamba, magoya bayan jam'iyyarsu ta APC sun yi maci tare da yayyaga wasu hotunan ɗan takarar NNPP Abba Kabir Yusuf.

A wani harin ramuwar gayya, su ma magoya bayan NNPP ɗin sun kai hare-hare a lokon su Abdullahi Abbas, inda su ma suka tayar da hankali tare da yayyaga hotunan takarar Gawuna da Garo.

Titi ɗaya ne kawai ya raba tsakanin unguwar Ciranci da Abdullahi Abbas ke zaune da kuma unguwar Tudun Wuzirci ta Abba Kabir Yusuf a Ƙaramar Hukumar Birni ta Kano Municipal.

Tazarar da ke tsakanin gidan mahaifin shugaban APC ɗin da kuma ɗan takarar NNPP ba ta wuce mita 500 ba. Hasali ma, a akwati ɗaya suke jefa ƙuri'a.

Bayanai sun nuna cewa da ma ba a jefa ƙuri'a a wannan rumfar zaɓen ba tare da cikakken tsaro ba na 'yan sanda saboda gudun rikici tsakanin magoya bayan gidan siyasar biyu.

A wannan karon ma, sai da Kwamashinan 'Yan Sandan a Kano, Abubakar Lawan ya shiga tsakanin ɓangarorin biyu da kansa kafin a yayyafa wa wutar rikicin ruwa.

Tashin hankalin da zaɓen ƙarashe ya jefa al'ummar Gama a 2019

Akwai wata rikita-rikita da ta faru a zaɓen gwamnan Kano na 2019 da har ta sa 'yan sanda kama mataimakin gwamna a lokacin kuma ɗan takarar APC a yanzu, Nasiru Yusuf Gawuna, da abokin takararsa kuma kwamashina a lokacin, Murtala Sule Garo, saboda zargin sun yaga takardar sakamakon zaɓe a mazaɓar Gama a ƙaramar hukumar Nassarawa.

Bidiyon da aka ga Murtala Garo na zuba Turanci a ofishin 'yan sanda jim kaɗan bayan kama su shi da mataimakin gwamna, na cikin abubuwan da ma'abota shafukan zumunta ba za su manta da su ba.

Haka nan, akwai hotunan da aka dinga yaɗawa na Murtalan wandonsa na ƙoƙarin sauka daga ƙugunsa daidai lokacin da 'yan sanda suka kama shi.

An zarge su da yunƙurin damalmala sakamakon zaɓen saboda fargabar jam'iyyarsu ta APC na gab da faɗuwa.

Bayanan bidiyo, Korafin da wata mata mazauniyar unguwar Gama ta yi a lokcain zaben karashe na Gama na 2019

Wannan lamari na daga cikin abin da ya sa zaɓen ya zama ɗaya daga cikin mafiya zafi da aka yi a tarihin siyasar jihar, da har aka kai ga zagaye na biyu tsakanin PDP da APC kafin hukumar zaɓe INEC ta bayyana Ganduje a matsayin wanda ya lashe shi a wa'adi na biyu.

An shiga zagaye na biyun ne sakamakon soke ƙuri'u masu yawa da INEC ta ce an kaɗa ba bisa ƙa'ida ba a unguwar Gama da ke cikin Ƙaramar Hukumar Nassarawa, waɗanda INEC ta ce sun zarta yawan tazarar da ke tsakanin Abba Kabir Yusuf na PDP da Gwamna Abdullahi Ganduje na APC.

PDP ce kan gaba zagayen farko da ratar ƙuri'a 26,655, kafin daga bisani INEC ta bayyana APC a matsayin wadda ta lashe zagaye na biyun da tazarar kuri'a 8,982 jumilla.

'Yan daba ɗauke da manyan makamai sun ci zarafin masu kaɗa ƙuri'a da ma'aikatan hukumar zaɓe ta INEC a zaɓen na Gama.

Tawagar BBC Hausa ma ba ta tsira ba daga tashin hankalin, inda matasa ɗauke da makamai suka fatattaki 'yan jaridar sannan suka tilasta wa masu jefa ƙuri'a.

Tawagar ta ga yadda aka tuɓe wa wata mace kaya kawai saboda ta ƙi yarda ta zaɓi ɗan takarar da ƴan dabar suka tursasa mata a lokacin.

Kazalika, wasu matasa sun fatattaki ƴan jaridar gidan talabijin na TVC tare da barzanar cinna wuta a motar TVC mai ɗaukar bidiyo da bayanan tataɓurzar da ake yi a wajen don hana su watsa shi kai tsaye ga ƴan ƙasar.

Sai dai ɓangarorin biyu sun zargi juna da amfani da matasa don tayar da fitina.

Masu sa-ido na gida da waje sun yi Allah-wadai da yadda ƙarshen zaɓen ya gudana, inda suka ce an yi amfani da 'yan daba da jami'an tsaro wurin muzgunawa da hana 'yan adawa kaɗa ƙuri'a, da kuma aringizon kuri'a, zargin da APC da INEC da 'yan sanda suka musanta.

Ku latsa nan don karanta labarin da BBC ta wallafa a wancan lokacin kan batun zaben.

Hukuncin da doka ta tanada kan kalaman ta da fitina

Sashe na 92 zuwa 96 na Dokar Zaɓe ta 2022 a Najeriya ne suka yi magana kan yaƙin neman zaɓe da kuma hukunce-hukunce kan laifuka, cikinsu har da na kalaman tayar da fitina a lokutan yaƙin neman zaɓen.

Sashe na 93 (1) na dokar ya ce: "Haramun ne jam'iyya ko ɗan takara ko wani mutum ko rukunin mutane su yi wa wani barazana ba ta hanyar yin amfani da ƙarfi ko tashin hankali yayin yaƙin neman zaɓe don tilasta wa mutumin ko wani daban wajen goyon bayansu ko kuma ya daina goyon bayan wata jam'iyya ko wani ɗan takara."

"(2) Duk jam'iyya ko ɗan takara ko mai neman takara ko wani rukunin mutane da suka saɓa wa tanadin wannan sashe ya aikata laifi kuma za a hukunta shi da:

"(a) Idan ɗan takara ne ko mai neman takara ko wani mutum ko rukunin wasu mutane, tarar abin da bai wuce naira N,1,00,000 ko kuma ɗaurin wata 12.

"(b) Idan kuma jam'iyya ce, tarar naira N2,000,000 a karon farko, da kuma naira N500,000 idan ta sake yin laifin a gaba."

Kauce wa Facebook
Ya kamata a bar bayanan Facebook?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Facebook suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Facebook da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook

Wannan bidiyon na nuna lokacin da ƴan daba suka fafari mutane daga layin zaɓe, ciki har da ƴan jarida na BBC da na wasu kakafen inda suka ruga don neman mafaka

'Idan ba a ɗauki mataki ba lamarin zai haifar da fitina'

Jim kaɗan bayan shugaban APC, Abdullahi Abbas ya yi waɗancan kalamai sai jagororin jam'iyyar da magoya baya suka ɓarke da sowa da ƙyaƙyata dariya, cikinsu har da Gwamna Ganduje.

"Yadda ake fatan a kammala zaɓe lafiya, idan kuma aka fara irin waɗannan kalamai to kamar ana tunzuro sauran mutane ne su ma su dinga yin hakan," in ji masanin kimiyyar siyasa a Kano Malam Kabiru Sufi.

Masu sharhi kan al'amuran siyasa na kallon kalaman a matsayin na tunzuri, waɗanda idan ba a ɗauki mataki ba zai haifar da matsala.

"'Yan siyasa na cewa kowa na da ikon tayar da fitina, idan wani ya nuna cewa tashin hankali ne makaminsa to yana bai wa wani dama ne shi ma ya yi," a cewar Sufi."

"Wannan dalilin ne ya sa ya kamata a kauce wa irin waɗannan kalaman don a samu tsaftatacciyar siyasa, a ja hankalin masu yin su don kar a ɗumama siyasar baki ɗaya."

Tuni ma'abota shafukan sada zumunta suka laƙaba wa Abdullahi Abbas sunan "tsiya-tsiya" tare da mayar da abin raha da muhawara da sauran hirarrakinsu na yau da kullum.

Hakan yana alamta cewa ko dai masu zaɓe - waɗanda ake yin abin don su - ba su fahimci girman matsalar ba, ko kuma ba su ɗauki abin da muhimmanci ba.

Sai dai Sufi na ganin suna yin hakan ne don su rage zafin abin tun da hukumomi ba su yi magana ba.

"Sun fahimci girman matsalar, wataƙila sun jira ne su ga ko za a samu tsawatarwa, rashin samun tsawatarwar kuma sai suka mayar da shi raha, kuma akwai hikima cikin hakan."

Tarihi ya nuna cewa siyasar Kano ta gaji kalaman tayar da hankali duk lokacin da 'yan siyasa suka hau duro, sai dai kalaman kan fi zafi idan shugabanni na yi wa junansu barazana da tashin hankali.