Kotu ta kama ɓarawon yara da laifi a Kenya

Kotu ta kama wani ma'aikacin asibiti da laifin safarar mutune bayan BBC ta ɗauki bidiyonsa lokacin da yake yunƙurin sayar da jariri a kasuwar bayan fage.

Fred Leparan da ke aiki a asibitin Mama Lucy Kibaki, an ɗauki bidiyonsa yana karɓar kuɗi dala 2,050 (kwatankwacin naira miliyan 1.5) don sayar da jaririn da ke ƙarƙashin kulawar asibitin.

An kama shi a 2020 bayan wani binciken ƙwaƙwaf na sashen BBC Africa Eye.

An tuhumi Leparan tare da wani ma'aikacin daga wani asibitin daban, Selina Awour, da zargin satar yaro.

An samu Awour da aikata laifuka uku da suka shafi wofintar da yara, amma an wanke shi daga zargin safarar yaran.

Za a yanke wa mutanen biyu hukunci a ranar 26 ga watan Satumba.

Tun da fari wakiliyar sashen Africa Eye ta tunkari Leparan ne a matsayin mai sayen jariri bayan ta samu labarin cewa babban ma'aikacin yana safarar yara a asibitin gwamnati.

An shirya ganawa a asibitin, inda Leparan ya nemi wakiliyar, wadda ta ce ita da mijinta sun gaza ɗaukar ciki, ya tambayi wasu abubuwa kafin a ƙulla yarjejeniyar sayen jaririn.

A ranar da ya kamata a tura jaririn zuwa wata cibiyar kula da jarirai ta gwamnati, tare da wasu yaran biyu, an ɗauki Leparan yana sauya bayanai a jikin takardu don ya nuna cewa yara biyu za a kawo maimakon uku.

BBC ta tabbatar da cewa an kai dukkan yaran uku zuwa gidan kula da su kai-tsaye, amma an ɗauki bidiyon Leparan yana sauya bayanan yana mai faɗa musu cewa yanzu jaririn ya zama nasu kuma suna iya tafiya da shi.

Duk da hujjar da ake da ita a kansa, shari'ar ta ɗauki sama da shekara biyu.

Leparan ya samu damar ɗaukar ƙwararrun lauyoyi a Kenya, amma kuma babban shaidan da yake kare shi bai iya bayar da cikakken bayani ba.

Duk da cewa dolensa ya amince da cewa shi ne a cikin bidiyon, amma ya yi yunƙurin musanta cewa muryarsa ce, inda ya ce ta wani ce daban duk da cewa motsin bakinsa ya yi daidai da kalaman. Daga baya ya amince cewa wasu daga cikin kalaman nasa ne.

Leparan ya kuma yi iƙirarin cewa bai fahimci wasu ɓangarori ba na asibitin da ya shafe shekara uku yana aiki a cikinsa, yayin da aka nuna wa kotun bidiyon Leparan yana tsara yadda za a sace da kuma fitar da jaririn.

Haka nan, binciken BBC ya gano yadda aka dinga sayar da yara a asibitin Mama Lucy, amma wani ma'aikacin asibitin da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce ya san wasu jarirai 12 da suka ɓata cikin wata biyu kacal.

"Mutane da dama na karɓar cin hanci. Da zarar an ba su wani abu sai su rufe bakinsu gum kuma ba za su sake cewa komai a kai ba," a cewarsa, yana nufin cin hancin da ake bai wa ma'aikatan asibitin.

Ana yawan samun buƙatar sayen yaran da aka sato a Kenya, wadda ke ƙaruwa sakamakon ƙyama saboda gaza ɗaukar ciki da kuma yunƙurin ɗaukar riƙon yara, abin da ke da wahala a hukumance.

Abin da Leparan ya aikata kaɗan ne daga cikin matsalolin da ke tattare da wannan lamari.

Africa Eye ya kuma ga yadda masu safara ke shirya saye da sayar da jarirai a wasu asibitocin sha-ka-tafi, da kuma satar yaran daga wajen iyaye matan da ba su da matsuguni da ke yawo a kan titunan birnin.

Mary Auma, wadda ke da wani asibitin da take karɓar haihuwa daga mata marasa ƙarfi kuma su sayar mata da su don ta sayar wa wasu don neman riba, ta ɓace ɓat bayan wani wakilinmu da ya ɓatar da kama ya ɗauki bidiyonta.

Da muka sake komawa birnin Nairobi a baya-bayan nan, ba mu ga alamar Auma ba, kuma an lalata asibitin nata.

Amma fa har yanzu ana ci gaba da sace yara a Nairobi. A kusa da asibitin da aka lalata, wata mata ta tunkaro mu ɗauke da kwali da aka manna hoton jikarta mai shekara biyar mai suna Chelsea Akinye.

Shekara ɗaya ke nan da kwana shida bayan sace Chelsea a lokacin, a cewar kakar tata, Rosemary. Ta ce ta yi ta neman Chelsea a kullum tun daga ranar ta hanyar liƙa hotonta a faɗin unguwar da sauran sassa.

Alƙaluman hukuma da ake da su kan yaran da ake safara a Kenya ba su da yawa.

A cewar sakatariyar kula da walwalar yara, Florence Bore, an bayar da rahoton ɓatan yara 6,841 tsakanin watan Yulin 2022 da Mayun 2023. Yara 1,296 kawai aka yi nasarar ganowa.

Mueni Mutisya, daga sashen binciken laifuka na hukumar, ta faɗa wa BBC cewa suna samun rahoton satar yara biyar a kowane mako a lissafi na tsakatsaki.

Kwana ɗaya bayan mun wallafa rahoton binckenmu a 2020, ministan kula da walwalar jama'a da aikin yi na lokacin, Simon Chelugui, ya ci alwashin ɗaukar tsattsauran mataki don daƙile satar yara.

Ms Mueni ta ce akwai buƙatar a ƙara zage damtse, tana mai kira da ƙara kafa dokokin da za su tilasta wa jama'ar gari kai rahoton duk wani zargi da suke yi na satar yara ko kuma cin zarafinsu.

"Ya kamata mu samu manufa ɗaya wajen kare yara," a cewarta.

Yaran da suka fi shiga haɗari su ne na talakawa, kamar yadda Maryana Munyendo, shugabar ƙungiyar 'Missing Child Kenya', ta bayyana.

Ƙungiyar na da layin waya da ake kira a kyauta don bayar da rahoton garkuwa da yara.

"A Nairobi, har yanzu muna yawan samun rahotanni daga unguwannin talakawa," in ji Ms Munyendo. Ta ce a lissafi na tsakatsaki, har yanzu ana tura mata rahoton ɓatan yara sau uku a kullum ta layin wayarta.