Me ya sa yara ke aikin ƙarfi a ƙasa mai arziƙi kamar Amurka?

Ga yarinya 'yar shekara 14 mai suna B, zaman ta a aji ba tare da ta yi gyangyaɗi ba abu ne mai matuƙar wahala.

Yawanci takan kasance ba ta je makaranta ba tsawon kwanaki.

Tana karatu ne a wata makarantar gwamnati da ke tsibirin Grand Island, wani karamin gari ne a jihar Nebraska da ke Amurka.

To amma rashin zuwan ta makaranta ba yana nufin tana aikata wani mugun laifi ba ne.

Yawanci B, wadda iyayenta 'yan asalin Guatemala ne, takan gaji ne sosai bayan ta yi aiki daga karfe 11 na yamma zuwa 5 na safe a tsawon kwanaki shida a mako.

Tana aikin wanke injinan da ake amfani da su wajen sassara kasusuwan dabbobin da aka yanka a masana'antar da ake sarrafa nama.

Wani lokacin ma takan fasa zuwa makaranta ne saboda jinyar ƙonewar da ta samu a lokacin da take aiki.

A cewar wani kundi da wata kotu ke da shi, B, na daya daga cikin yara 31 da gwamnatin tarayya ta gano a bara cewa suna aikin dare wajen tsaftace masana'antar ba bisa ka'ida ba.

Wata kungiyar tabbatar da tsaftar yadda ake sarrafa nama wato PSSI ce ke daukar su haya don yin wannan aiki.

Masu sanya ido daga gwamnatin tarayyar da suka je masana'antar sun bayyana cewa," Yawancin ma'aikatan da suka tattauna da su na cikin tsoro kuma sukan rinka kallon wadanda suka dauke su aiki a lokacin da ake musu tamboyi."

A karshe dai an zargi kungiyar PSSI da daukar yara kanana 102 a jihohi 8 da laifin aiki.

A watan Fabarairun da ya wuce ƙungiyar ta PSSI, ta biya tarar dala miliyan 1.5, bayan da gwamnati ta gano cewa ana sanya yara ayyuka masu hadari saboda ta'ammali da wasu sinadarai da suke a ko da yaushe.

Masu bincike daga gwamnatin kasar ta Amurka, sun fahimci cewa akalla yara uku da ke aiki a wannan masana'anta sun samu raunuka a yayin aiki.

To amma a bangaren B, abin ya sha bamban.

Amurka na daya daga cikin kasashen da ke da arziki a duniya, to amma tana fama da matsalar sanya yara aikatau ba bisa ka'ida ba.

A 2022, kusan yara 4000, masu bincike na gwamnatin tarayya suka gano suna irin wannan aiki.

Bautar da yara na jan hankalin ma'aikata, doka a wasu jihohin ta bayar da damar a rinka biyan yara rabin albashin manya, abin da ya sanya sauran jihohin kasar ke duba yiwuwar daukar irin wannan mataki.

Gaba daya an sake dokar bautar da kananan yara a jihar Iowa a watan Yuli, inda aka fadada ayyuka da sa'oin aiki da ya kamata yara 'yan shekaru goma sha su rinka yi.

Jihar Iowa, ita ce jiha ta baya-bayan nan da ta zartar da dokoki a kan bautar da kananan yara kamar irin na gwamnatin tarayyar kasar, to amma wani bincike da wata cibiya ta yi a watan Mayu, ya gano cewa akalla jihohi 14 cikin 50 na Amurka na duba yiwuwar amfani da dokar gwamnatin tarayya ta rage irin yadda ake bautar da kananan yara, kuma tuni jihohi takwas suka amince da irin wadannan dokoki.

Yara 'yan shekara 16 zuwa sama a wasu jihohin yanzu za su iya aikin karfi ko mai hadari kamar rushe gini ko aiki a masana'antar sarrafa nama.

Za kuma su iya aiki a gidajen shan barasa kamar raba barasar ga masu bukata to amma ba za su iya saya ba har sai sun kai shekara 21.

To amma wannan mataki ya ci karo da dokokin kasa inda aka amince cewa yara 'yan shekaru 14 da 15 za su yi aiki ne na tsawon sa'o'i uku a rana kuma kada lokacin ya shafi lokacin zuwa makaranta, sannan kuma kada su yi aiki bayan karfe bakwai na yamma.

'Wannan ba matsala ce ta ƙarni na 19 ba'

Babu wanda zai ce ya san girman wannan matsala, tun da babu wata kididdiga ta yaran da ba sa aiki a kasar.

A shekarun 1970 ne Amurka ta daina karbar kididdiga a kan yara 'yan kasa da shekara 16 da ba sa aiki - in ji Farfesa Edmonds.

To amma duk da haka masu duba kamfanoni a kasar za su iya ba mu kididdiga a kan wannan batu.

Bayan samun rahoton, an samu karuwa da kashi 69 cikin 100 a kan bautar da yara a bara idan aka kwatanta da 2018.

A watan Fabrariru a cikin wata shari'a, an gano cewa an samu yara ƴan kasa da shekara 13 da suke aiki ba bisa ka'ida ba, kuma yawancinsu na aiki ne a mayanka.

Wannan matsala ce ta yanzu ba wai ta karni 19 ba, kuma matsala ce da ta kamata a kawo karshenta, in ji Marty Walsh a cikin wata makala da ya wallafa a ranar 27 ga watan Fabrairun 2023.

Karancin ma'aikata

Karuwar da ake samu ta bautar da yara a Amurka na da abubuwan da ke janyo ta musamman ga yara marasa karfi.

Wuraren aiki a Amurka na masu matukar wuya su cike gibin da suke da shi na ma'aikatan da suke bukata kuma albashin kasar ya karu saboda matsalar hauhawar farashin kayayyakin da aka fuskanta a kasar a bara.

Dukkan wadannan abubuwa na nuna cewa akwai karancin ma'aikata a kasar kuma matsala ce da take taimaka wa bakin haure shiga kasar don neman guraben aiki musamman mutanen da suka fito daga kasashen da ke makwabtaka da kasar kamar Mexico.

A sakamakon wannan, adadin yara bakin haure da suka tsallaka zuwa Amurka ya karu.

An saki yara tsakanin kashi 12 cikin 100 da kashi 14 cikin 100 a 2021 da 2022 inda aka mika su ga wadanda za su dauki nauyin su don kula da su.

Wani lauya a kan kaurar yara ya shaida wa BBC cewa, a hakikanin gaskiya, gwamnatin Amurka ba ta san abin da ke faruwa ga wadannan yara ba idan ta sake su ko kuma ta damka su a hannun masu kula da su.

Ya ce, " Mun san cewa wadannan yara yawanci an hada su ne da iyalai marassa karfi wadanda kuma ke da yara da yawa, gashi ba su da cikakkun takardu. Ba zan yi mamaki ba idan aka ce kashi biyu bisa ukunsu na aikin karfi."

Gwamnati ba ta ce komai ba kan waɗannan kalamai na lauya.

Yaran da ake nema don su yi aiki

Kwararrun da BBC ta yi hira da su sun ce irin wadannan yara na zama wadanda ake nema a masana'antu musamman inda ke neman ma'aikata.

A nasa bangaren, Farfesa Nana, ja ya yi, ya ce bai ga dalilin da zai sa a samu karuwar irin wadannan yara a wuraren da ake neman ma'aikata ba.