Newcastle ta kammala ɗaukar Sandro Tonali daga AC Milan

Newcastle ta ɗauki ɗan wasan tsakiyar AC Milan da Italiya Sandro Tonali.

Ɗan shekara 23 ya sanya hannu tsakaninsa da ƙungiyar na tsawon shekara biyar, ya kuma zama ɗan wasa na farko da Eddie Howe ya ɗauka a bana lokacin da ƙungiyarsa ke shirin tunkarar Champions.

Newcastle ta ɗauki Tonali kan kuɗi fan miliyan 55, wanda hakan ya sa ya zama ɗan wasan Italiya mafi tsada.

Tonali ya taimaka wa AC Milan ta lashe Serie A na 2021-2022 kuma yana cikin tawagar da ta je wasan kusa da na ƙarshe na gasar Zakarun Turai a bara.

Yana cikin tawagar Italiya da take buga wasan Zakarun Turai na 'yan ƙasa da shekara 21.

A wani bayaninsa da aka wallafa a shafin ƙungiyar, Tonali ya ce " Ina son bai wa maras ɗa kunya a tsakiyar filin wasa, zan yi duk abin da zan iya a ko da yau she, ina jin wani irin daɗi cewa zan yi wasa a filin wasa na St James Park zan so na ji yadda magoya baya za su nuna mana ƙauna."

Kocin ƙungiyar Howe ya ce Tonali, " Ɗan wasa ne na musamman da ke da bai wa, kuma zai taimakawa kulob ɗinmu ta ko ina.

"Yana ɗan shekara 23 amma ya zama ɗaya daga cikin manyan 'yan wasa masu muhimmanci a ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin kwallon kafa na Turai a gasar Champions da yadda yake taka rawa a ƙasarsa."

Tonali ya koma AC Milan ne daga Brescia a 2020, a shekarar da ta biyo baya, ya ci kwallo biyar cikin wasa 36 da ya buga lokacin da Milan ta ci lig a 2022.

Ya ci kwallo biyu a wasanni 34 da ya buga a Serie A a kakar da ta wuce da suka kammala a matsayi na hudu.

Ya buga wasa 12 a gasar Zakarun Turai gabanin a kora ƙungiyar gida a matsakin kusa da ƙarshe na gasar.