Shirye-shiryen Kirsimati da yawon buɗe ido a kan raƙumi cikin hotunan Afirka

Lokacin karatu: Minti 3

Wasu daga cikin zaɓaɓɓun hotuna daga Afrika da na ƴan nahiyar a wasu sassan duniya

Ɗan wasan ninƙayar Afirka ta Kudu, Mthobisi Mlambo, sanye da kayan Santa a ƙarƙashin teku a ranar Laraba,18 ga watan Disamban 2024.

Asalin hoton, Rajesh Jantilal / AFP

Bayanan hoto, Ɗan wasan ninƙayar Afirka ta Kudu, Mthobisi Mlambo, sanye da kayan Santa a wani wasa da aka yi a Durban.
Wata mai sayar da kayyaki a Abidjan ta baje kolin kayan Santa a gefen titi a ranar Alhamis 19 ga watan Dismanban 2024

Asalin hoton, Legnan Koula / EPA

Bayanan hoto, A kasuwannin Abidjan na Ivory Coast ana ci gaba da sayar da kaya masu alaƙa da bikukuwan kirsimati, gabanin shagulgulan ranar bikin da ke tafe.
Wasu masu wasan tsere biyu a yayin gasar Marakez a ranar Asabar 14 ga watan Disamban 2024.

Asalin hoton, Mohamed Elshahed / Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Asabar ƴan wasan tsere daga sassan duniya sun fafata a gasar Marakez, a Giza na ƙasar Masar.
Mai yawon buɗe ido a kan raƙumi a Giza, na ƙasar Masar.

Asalin hoton, Sayed Hassan / Getty Images

Bayanan hoto, Wani mai yawon buɗe ido a kan raƙumi a wajen tseren na Masar.
Wani ma'aikaci yana tara tubali domin gina abin da aka yi wa laƙabi da farin tsauni, kusa da birnin Minya - a ranar Asabar 14 ga watanDisamban 2024.

Asalin hoton, Mahmoud Elkhwas / Getty Images

Bayanan hoto, Duk dai a ranar wani ma'aikaci yana tara tubali domin gina abin da aka yi wa laƙabi da farin tsauni, kusa da birnin Minya da ke kudancin Masar.
Masu wasannin hawa sama sun ƙayatar da jama'a a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu - a ranar Litinin 16 ga watan Disamban 2024.

Asalin hoton, Kim Ludbrook / EPA

Bayanan hoto, A ranar Litinin masu wasannin hawa sama sun ƙayatar da jama'a a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu.
Wata mai tallar kayan ƙawa sanye da kayanta da aka ɗinka su da haɗakar farantai da cokula, a wajen bikin baje kolin al'adu na kudancin Sudan karo na 11, a Nairobi babban birnin ƙasar Kenya a ranar Laraba 18 ga watan Disamban 2024.

Asalin hoton, Daniel Irungu / EPA

Bayanan hoto, Wata mai tallar kayan ƙawa sanye da kayanta da aka ɗinka su da haɗakar farantai da cokula, a wajen bikin baje kolin al'adu na kudancin Sudan karo na 11, a Nairobi babban birnin ƙasar Kenya a ranar Laraba.
Ƴanmatan ƙabilar Maasai sun sha kwalliya a wajen buɗe wasanni Olympics a Kajiado na ƙasar a ranar Asabar 14 ga watan Disamban 2024.

Asalin hoton, Daniel Irungu / EPA

Bayanan hoto, Ƴanmatan ƙabilar Maasai sun sha kwalliya a wajen buɗe wasanni Olympics a Kajiado na ƙasar.
Zakarun gasar riƙe da kofin da suka lashe a ranar Asabar 14 ga watan Disamban 2024

Asalin hoton, Daniel Irungu / EPA

Bayanan hoto, Ƙauyen Mbirikani Manyatta ya karɓi kofin wasannin Olympics na Maasai, na bana.