Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mene ne shirin nukiliya na Iran kuma me Amurka ke so ta yi?
- Marubuci, Raffi Berg
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 5
Amurka da Iran na shirin fara tattaunawa a ranar Asabar karon farko cikin tsawon shekaru da zimmar ƙulla sabuwar yarjejeniya kan shirin nukiliyar Iran ɗin.
Shugaba Donald Trump ne ya cire Amurka daga yarjejeniyar da suka ƙulla tsakanin Iran da ƙasashen duniya a 2018, kuma ya saka mata takunkumai, abin da ya harzuƙa Iran.
Trump ya yi barazanar ɗaukar kai hare-hare kan Iran idan aka gaza cim ma yarjejeniya.
Me ya sa aka hana Iran mallakar nukiliya?
Iran ta ce shirin nukiliyarta ba na ƙera makami ba ne, na samar da makamashi ne kawai.
Ta nanata cewa ba neman haɗa bam ɗin nukiliya take yi ba, amma wasu ƙasashe - da kuma hukumar kula da makaman nukiliya ta duniya International Atomic Energy Agency (IAEA) - ba su yarda ba.
An fara zargin Iran ne game da shirin nata bayan an gano wasu ɓoyayyun wuraren binciken nukiliya a 2002.
Hakan ya jawo karyewar wata yarjejeniya da ake kira Nuclear Non-Proliferation Treaty (NPT), wadda Iran ta ƙulla da wasu ƙasashe, wadda ta ke hana yaɗuwar makaman nukiliya a duniya.
NPT kan bai wa ƙasashe damar yin amfani da fasahar nukiliya wajen ayyukan lafiya, da noma ban da haɗa makamin nukiliya.
Yaya cigaban shirin nukiliyar Iran yake?
Tun bayan ficewar Amurka daga yarjejeniyar da aka kira Joint Comprehensive Plan of Action or JCPOA a 2018, Iran ta karya ƙa'idojinta a matsayin martani, wanda ya sa aka sake ƙaƙaba mata takunkumai.
Ta ƙara zuba dubban na'urorin tace ma'adanin Uranium wanda yarjejeniyar JPCOA ta haramta.
Haɗa makamin nukiliya na buƙatar a inganta ma'adanin uranium zuwa kashi 90 cikin 100. A ƙarƙashin yarjejeniyar, an bai wa Iran damar inganta kashi 3.67 ne kawai ko kuma zuwa nauyin 300kg - wanda zai iya ba da damar ayyukan bincike amma bai kai na haɗa makami ba.
Amma zuwa watan Maris na 2024, hukumar IAEA ta ce Iran na da uranium kusan 275kg da ta inganta zuwa kashi 60 cikin 100. Hakan zai iya ba ta damar haɗa bam kamar shida idan ta ƙara inganta shi.
Jami'ai a Amurka sun ce sun yi imanin Iran za ta iya mayar da shi zuwa makami ɗaya a cikin mako ɗaya. Amma kuma sun ce Iran sai ta yi kamar shekara ɗaya zuwa wata 18 kafin ta iya samar da cikakken makamin nukiliya.
Amma wasu ƙwararru na cewa za a iya gina ƙaramin makamin cikin wata shida ko ƙasa da haka.
Me ya sa Trump ya cire Amurka daga yarjejeniyar?
Amurka da Majalisar Ɗinkin Duniya da Tarayyar Turai sun saka wa Iran takunkuman tattalin arziki daga 2010 saboda zargin cewa tana shrin haɗa nukiliya.
Sun hana Iran sayar da man fetur ɗinta a kasuwar duniya da kuma hana ta taɓa kuɗinta dala biliyan 100 da ke ƙasashen waje. Tattalin arzikinta ya karye, kuma darajar kuɗinta ya yi ta karyewa, wanda ya jawo hauhawar farashi.
A 2015, Iran da manyan ƙasashen duniya shida - Amurka, Faransa, Rasha, Jamus, Birtaniya - suka ƙulla yarjejeniyar JCPOA.
Ƙasashen sun amince su ɗage wa Iran takunkumai bisa sharuɗɗan yarjejeniyar.
An tsara yarjejeniyar za ta yi aiki tsawon shekara 15.
Lokacin da Donald Trump ya kama mulki ya fitar da Amurka daga yarjejeniyar a 2018, wadda babbar dirka ce a cikinta.
Ya ce yarjejeniyar ba ta da kyau saboda ba mai ɗorewa ba ce kuma ba ta yi magana kan shirin Iran na makamai masu linzami ba. Ya ƙara wa Iran takunkumai saboda ta dawo kan teburin tattaunawa.
Isra'ila ta yi iƙirarin cewa Iran ta ci gaba da neman haɗa nukiliya a ɓoye kuma za ta yi amfani da kuɗin da ta samu bayan cire tukunkumi wajen ƙarfafa rundunar sojinta.
Me Amurka da Isra'ila ke so yanzu?
Da alama sanarwar da Trump ya bayar ta neman fara tattaunawa da Iran ta bai wa Isra'ila mamaki. Ya daɗe yana cewa zai iya ƙulla yarjejeniya mafi kyawu sama da JCPOA, amma har yanzu Iran ta yi watsi da buƙatar.
Trump ya yi gargaɗi cewa idan Iran ba ta yarda da sabuwar yarjejeniya ba "zai kai musu hari".
Mai bai shi shawara kan harkokin tsaro Mike Waltz ya ce Trump na son Iran ta "lalata baki ɗayan" shirin nukilyar tata, yana cewa: "Kamar ingantawa, ko haɗa makami, wato shirinta na makamai masu linzami."
Duk da cewa Trump ya ce tattaunawar ta gaba da gaba ce, ministan harkokin Iran Abbas Araghchi ya ce tattaunawar da za a yi a Oman ba ta gaba da gaba ba ce. Ya ce a shirye suke su tattauna amma dole sai Trump ya amince cewa "babu maganar hari".
Bayan sanarwar da Trump ya yi, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce yarjejeniya ɗaya da za su amince da ita ita ce wadda Iran za ta yarda da haƙura da shirin nukiliya gaba ɗaya.
Ya ce hakan na nufin: "Mu shiga mu tarwatsa masana'antun, mu lalata komai bisa sa ido da jagorancin Amurka."
Abin da Isra'ila ke fargaba shi ne Trump zai iya yarda da wani abu ƙasa da lalata shirin na Iran gaba ɗaya da zai yi kurin cim mawa a matsayin nasarar difilomasiyya.
Isra'ila da ba ta shiga yarjejeniyar NPT ba, ana ganin tana da makaman nukiliya, abin da ba ta taɓa amsawa ko ƙaryatawa ba.
Isra'ila na ganin idan Iran ta samu nukiliya barazana ce a gare ta saboda har yanzu ba ta amince da 'yancin Isra'ilar ba a matsayin ƙasa.
Amurka za ta iya kai wa Iran hari?
Amurka da Isra'ila na da ƙarfin sojin da za su iya kai wa masana'antun nukiliyar Iran hare-hare, amma hakan zai zo da wahala da kuma kasada, har ma da rashin tabbas.
Manyan masana'antun na ƙarƙashin ƙasa, abin da ke nufin mafi munin bamabaman da ke iya fasa gidan ƙasa ne kawai za su iya kaiwa ga wurin. Yayin da Amurka ke da waɗannan bamabaman, ba a san ko Isra'ila na da su ba.
Tabbas Iran za ta kare kan ta, wanda zai iya haɗawa da kai wa kadarorin Amurka hari a yankin Gabas ta Tsakiya, da kuma harba wa Isra'ila makamai masu linzami.
Idan hakan za ta faru, akwai yiwuwar sai Amurka ta yi amfani da sansanoninta da ke ƙasashen yankin Gulf na Larabawa, da kuma jiragen ruwa masu dakon jiragen yaƙi.
Amma kuma ƙasashe kamar Qatar da take da sansanin sojin sama na Amurka mafi girma, ba lallai ta yarda a yi hakan ba saboda tsoron ramuwar gayya.