Za a fara shari'ar matar da ake zargi da kashe kishiyarta da taɓarya a Bauchi

CP Umar Mamman Sanda

Asalin hoton, Bauchi Police Command

Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi arewa maso gabashin Najeriya ta ce za ta gurfanar da wata matar aure a gaban kotu, da aka yi zargin ta buga wa kishiyarta taɓarya a kai, lamarin da ya yi sanadin mutuwar ta daga bisani a asibiti.

Za a gurfanar da matar ne a gaban kotun a ranar Talatar nan 29 ga watan Nuwamban 2022.

'Yan sanda sun ce a makon da ya wuce ne, mijin matan Ibrahim Sambo a ƙauyen Gar cikin ƙaramar hukumar Alƙaleri, ya kai ƙorafin amaryarsa Maryam Ibrahim bisa zargin ta buga wa uwargidansa Hafsat Ibrahim taɓarya.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Bauchi SP Ahmed Muhammed Wakil ya shaida wa BBC cewa a bincien da suka yi Maryam ta tabbatar musu da cewa ta yi amfani da taɓarya ta kashe Hafsat.

Ya ce “abin da ya faru akwai ɗan marigayiyar mai suna Abdul’aziz da mahaifiyarsa ta aike shi ya kai wa Maryam din tsire, to tana kammala cin tsiren sai ta fara amai.

“To dama akwai faccalarsu a gidan, sai Maryam ta ba ta labari, sai ita faccalar ta ce ai kamar cutar olsa ce ta jawo mata hakan, amma sai Maryam ba ta yarda da batun ba.

“Kawai sai ta je kicin ta ɗauko taɓarya ta je ta samu uwagidan nata Hafsat a kwance sai ta doka mata taɓaryar,” in ji shi.SP Wakil ya ƙara da cewa bayanin Maryam ya nuna musu cewa zargin Hafsat take yi da aiken tsire da ta yi mata.

Tun daga lokacin da lamarin ya faru Maryam ke garƙame a hannun ƴan sanda a birnin Bauchi inda aka ci gaba da faɗaɗa bincike.

“Amma za mu gurfanar da ita a gaban kotu a yanke mata hukuncin da ya dace da ita,” a cewar SP Wakil.

Bayanai sun ce a lokacin da Maryam ta buga wa Hafsat taɓarya sai aka garzaya da ita cibiyar lafiya a matakin farko da ke garin na Gar, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarta.

Matsalar kashe-kashe tsakanin kishiyoyi ba baƙon abu ba ne a Najeriya, sai dai abin na neman zarta hankali, duba da yadda ake samun ƙaruwar hare-haren da kishiyoyi ke kai wa juna.