Yadda aka kashe wasu 'yan Nijar a Kudancin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni daga jihar Anambra da ke kudancin Najeriya na cewa 'yan Jamhuriyar Nijar biyu ne mahara suka kashe a karamar hukumar Aguata ranar Asabar da daddare, yayin da na ukun ke can kwance a asibiti yanzu haka yana jinya.
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake zargin sace wasu 'yan Nijar kimanin 10 duk dai a jihar ta Anambra.
Kawo yanzu ba a san wadanda suka kai harin ba, sai dai yankin ya dade yana fama da hare-haren mayakan kungiyar IPOB da ke son ballewa daga Najeriya.
BBC ta fahimci cewa an yi jana'izar waɗanda suka mutu, kuma sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da wasu yan bindiga a cikin mota suka same su a bakin shagon da suke sana'a suka bude musu wuta.
Wani abu da BBC ta gano shi ne cewa duka mutanen biyu da kuma daya da aka jikkata 'ya'yan mutum daya ne.
Mahaifin nasu ya shaida wa wakilinmu cewa 'ya'yan nasa "suna zaune ne kusan karfe tara sai aka bude musu wuta, kuma tuni muka rufe biyun, daya kuma na nan na karbar magani."
Ya kara da cewa garin Aguata na jihar Anambra na daya daga cikin garuruwa mafiya hadari saboda yawaitar hare-hare.
"Ko da rana duk abin da ake so za a yi maka a Aguata. Babu jami'an tsaro, ba inda za ka kai kukanka a bi maka hakkin ka. Babu shi sai dai Allah," in ji shi.
Saboda haka ya bukaci hukumomi da su tashi tsaye su kawo karshen hare-haren da ake kai wa al'umma a jihar Anambra musamman baki.
Alhaji Abdullahi Sa'idu shi ne mataimakin shugaban 'yan Jamhuriyar Nijar mazauna kasashen waje reshen Najeriya, ya kuma tabbatar wa BBC faruwar lamarin.
Ya bukaci jami'an tsaron Najeriya su rika kare wadannan baki da suka zo makwabciyar kasarsu neman abinci.
Duk da shugabannin kungiyar sun bayyana cewa 'yan sanda sun zo sun dauki hoton gawawwakin matasan da aka kashe, ba su samu wani gamsasshen bayani kan cewa za a dauki wani mataki ba.
Wakilcin kungiyar ya za su rubuta wa ofishin jakadancin Nijar da ke Abuja takarda domin bayar da bayani dalla-dalla na abin da ya faru a Aguata.
BBC ta yi kokarin jin ta bakin rundunar 'yan sanda a jihar Anambra, sai dai yunkurin bai yi nasara ba.
Babu wasu bayanai da suka nuna cewa hukumomin tsaron Najeriyar sun nuna dan yatsa ga wani ko wata kungiya da suke zargi da kai wannan hari ga bakin, amma a baya bayannan kungiyoyin 'yan bindiga sun zafafa hare a kudancin kasar.
Ko a makon da ya gabata jami'an tsaro sun gano wani sansanin yan bindiga a jihar Imo makare da gawawwakin, da kuma gasassun sassan jikin mutane.
Hakama ana kai wa sarakunan gargajiya hare-hare da ta kai ga cewa yanzu haka wasunsu sun shiga buya domin tsira da rayuwarsu.










