Abu 10 kan sabon Alkalin Alkalan Najeriya

Asalin hoton, State House
An rantsar da Mai Shari’a Olukayode Arwoola a matsayin muƙaddashin babban jojin kasar, bayan murabus din da Mai Shari’a Ibrahim Tanko Muhammad ya yi.
Mai shari’a Tankon ya yi murabus ne bisa dalili na rashin lafiya.
Mai Shari’a Olukayode Ariwoola shi ne ke bi wa babban jojin Najeriya Mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad baya.
An wayi gari da labarin murabus din babban jojin Najeriyar, Mai Shari’a Ibrahim Tanko Muhammad, musamman ma yadda ya mamaye kafafen yada labaran kasar da dama.
Mai taimaka masa a kan harkokin yada labarai Isa Ahuraka, ya tabbatar wa manema labarai, cewa tun a ranar Lahadi Mai shari’ar ya ajiye aikin nasa.
Wane ne sabon babban jojin?

Asalin hoton, State House
- Mai Shari'a Olukayode Ariwoola shi ne alkali mafi girman mukami bayan murabus din Mai Shari'a Ibrahim Tanko Muhammad.
- An haife shi ne a watan Agustan shekarar 1954, kuma ya yi alkalanci a Kotun Daukaka Kara ta Najeriya, kafin ya samu daukaka zuwa Kotun Kolin kasar.
- Ariwoola Musulmi ne ɗan asalin jihar Oyo, kuma ya shafe kusan shekara 11 a matsayin ɗaya daga cikin manyan alƙalan Kotun Ƙolin, bayan shigarsa cikinta a watan Nuwamban 2011.
- Babban Jojin ya fara karatunsa ne a ƙaramar hukumar Iseyin ta jihar Oyo daga 1959 zuwa 1967.
- Ariwoola ya kammala digirinsa a fannin Shari’a a Jami’ar Ife wacce ta zama Jami’ar Obafemi Awolowo a Ile Ife da ke Jihar Osun a 1980.
- Kafin ya zama alƙalin Kotun Ƙoli dai yana Kotun Ɗaukaka Ƙara ne a matsayin ɗaya daga cikin alƙalanta, sakamakon ƙarin girma da ya samu daga Babbar Kotun Jihar Oyon
- A yanzu bayan rantsar da shi, ya zama baban jojin Najeriya na 18, kuma ga alama shi ne zai ja ragamar yanke hukuncin shari’ar zaɓen shugaban ƙasa na 2023 idan har an samu ƙorafi bayan zaɓen.
- Mai Shari’a Ariwoola na ɗaya daga cin alkalai bakwai na Kotun Ƙoli da suka yanke hukunci kan ƙarar zaɓen shugaban ƙasa na 2019 da suka tabbatar da Shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar a karo na biyu.
- Sannan ya riƙe amtsayin alkali a Kotunan Ɗaukaka Ƙara na Kaduna da Enugu da kuma Lagos.
- Mai shari’a Ariwoola ya yi ƙarin karatuttuka da kuma kwasa-kwasai a ƙasashe daban-daban bayan Najeriya da suka haɗa da Birtaniya da Faransa da Amurka da Birtraniya da UAE.
End of Wasu labaran da za ku so ku karanta
Rashin lafiyar mai murabus

Asalin hoton, Supreme Court
An tabbatar da cewa babban Jojin mai murabus ya yanke shawarar sauka daga mukamin nasa ne sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita.
Babu dai wata sanarwa dangane da rashin lafiyar alkalin alkalan Najeriyar da aka fitar a baya, amma bayanin da ke fitowa daga kotun kolin na nuna cewa ya dan kwana biyu yana jinya.
Murabus din Mai shari’a Ibrahim Tanko ya zo bagatatan ne ko ba zato ba tsammani, kasancewar sai a watan Disamban badi ne zai cika shekarunsa na ritaya, wato shekara 70 da haihuwa.
Ko da yake a ƴan makwannin da suka wuce wasu majiyoyi a kotun kolin sun bayyana cewa an yi zaman tsama tsakanin babban jojin da wasu alkalan kotun kolin, wadanda suke zargin cewa ba a kyauta musu.
Wato ma’ana suna fuskantar nakasu ta fannin walwala. Amma Mai shari’a Ibrahim Tanko ya kare kansa - yana cewa aljihun kotun kolin ne ba shi da nauyi sosai.










