Gargaɗin da Najeriya ta yi wa 'yan kasarta kan shiga yaƙe-yaƙe a ƙasashen waje

Lokacin karatu: Minti 3

Najeriya ta gargadi 'yan ƙasarta a kan shiga yake-yake a wasu kasashen bayan wani rahoto da ya fito da ke cewa an yaudari wasu 'yan kasar inda suka shiga yakin da Rasha ta ke yi a Ukraine.

Cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta fitar, ta bayyana matukar damuwarta a kan yadda ake kara samun 'yan Najeriya da ake dauka aiki ba bisa ka'ida ba domin su je su yi yaƙi a wasu kasashen.

Rahoton wanda aka wallafa a makon da ya gabata wanda wasu masu bincike suka gudanar kan sojojin haya na Rasha, ya ce rundunar sojin Rasha ta dauki 'yan Najerya akalla 36 aiki domin su yi yaki a Ukraine inda aka kashe mutum biyar daga cikinsu.

Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta ce,"Yawancin 'yan Najeriyar da aka dauka irin wannan aiki an tura su fagen daga bayan an yaudaresu da cewa za a ba su aiki a rundunar sojin Rasha."

A makon daya gabata wani bincike da kamfanin dillancin labarai na AFP ya yi ya gano wasu 'yan kasar Kenya da dama da ke yaki a Ukraine bayan da aka yi musu alkawarin za a biya su makudan kudade.

Sun je Rasha inda aka tursasa musu sanya hannu a kan wata kwantiragi da ba su fahimci abin da ta kunsa ba daga nan kuma aka tura su fagen daga.

A makon daya wuce ne, shugaban kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya tattauna da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a kan batun dawowar wasu 'yan Afirka ta Kudu da ke yaki a Ukraine gida.

Wasu bayanai da aka samo daga Uganda wadda aminiyar Rasha ce, sun nuna yadda kasar ba ta son a soki Rasha.

A watan Nuwambar 2025, Ukraine ta ce ta gano 'yan kasar Afirka akalla 1,436 da ke yi wa Rasha yaki.

Jakadan Rasha a Najeriya Andrey Podyolyshev ya musanta cewa Moscow na daukar ƴan Najeriya aiki domin shiga cikin jerin mayaƙan da ke taimaka wa Rasha a yaƙinta da Ukraine.

Ya ce ba shi da masaniya kan duk wani shirin gwamnati na ɗaukar ƴan Najeriya aiki domin yaƙi a Ukraine, ya kuma ƙara da cewa idan har haka na faruwa, Rasha ba ta da hannu a ciki.

Sai dai sanarwar da rundunar sojin Ukraine ta fitar ta bayar da cikakken bayani kan ƴan Najeriya da suka mutu a fagen yaƙi da kuma yadda suka shiga rundunar sojin Rasha.