Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me nasarar Najeriya a Rwanda ke nufi a neman zuwa gasar Kofin Duniya?
A ranar Juma'a ne tawagar Super Eagles ta Najeriya ta doke Rwanda d2-0 a birnin Kigali a wasannin neman gurbin shiga gasar cin Kofin Duniya.
Ɗan wasan Najeriya Victor Osimhen ne ya zura duka ƙwallayen biyu gabanin hutun rabin lokaci.
Hakan na nufin yanzu Najeriya na matsayi na huɗu a cikin ƙasashe shida da ke Rukunin C bayan wasanni biyar-biyar.
A wasan Najeriya na gaba, za ta fafata ne da ƙasar Zimbabwe a fiin wasa na Godswill Akpabio da ke jihar Oyo a kudancin Najeriya a ranar Talata mai zuwa.
Bayan doke tawagar ƙasar Lesotho da Afirka ta Kudu ta yi ranar Juma'ar, yanzu ta ƙara tsawaita jagorancin rukunin da take yi zuwa maki 10. Sai Benin da ke ta biyu da maki takwas, Rwanda ta uku da maki bakwai, sai kuma Najeriya mai maki shida.
Wasanni huɗu suka rage wa Najeriya yanzu, waɗanda a cikinsu ne za ta nemi ɗarewa saman teburin. Amma za ta buƙaci doke Afirka ta Kudu da Benin kafin ta yi hakan.
Ƙasar da ta zama ta farko a kowane rukuni daga cikin rukunai tara na ƙasashen Afirka ne ke da tabbacin shiga gasar kofin na duniya, wanda a karon farko aka faɗaɗa zuwa ƙasashe 48.
Sai kuma za a zaɓi ƙasashe huɗu da suka fi ƙoƙari daga cikin waɗanda suka zama na biyu, sai su fafata wasan kifa-ɗaya-ƙwala na neman cike gurbi, inda waɗanda suka samu nasara za su iya samun damar shiga gasar.
Yanzu Najeriya na da sauran wasa biyar, duk da wanda za ta fafata da Zimbabwe a mako mai zuwa.
Sauran wasannin su ne:
- 1 ga Satumba: Nigeria da Rwanda
- 8 ga Satumba: Afirka ta Kudu da Najeriya
- 6 ga Oktoba: Lesotho da Najeriya
- 13 ga Oktoba: Najeriya da Benin