Mai tallan ruwa a filin wasa ta zama lafari a Najeriya

A da Gbemisola Yusuf na sayar da kayan sanyi ne a filayen kallon wasa a jihar Legas

Asalin hoton, Gbemisola Yusuf

Bayanan hoto, A da Gbemisola Yusuf na sayar da kayan sanyi ne a filayen kallon wasa a jihar Legas
    • Marubuci, Emmanuel Akindubuwa
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Gbemisola Yusuf mace ce mai hanƙoron jan ragamar rayuwarta da kanta.

Tun tana shekara 21 da haihuwa ta fara alƙalancin wasa a Najeriya.

"Jagorantar 'yanwasa 22 a cikin fili abu ne mai ban sha'awa," kamar yadda ta shaida wa BBC Sport Africa a filin wasa na Maracana da ke Legas.

Wannan ba ƙaramin abin alfahari ba ne saboda tana cikin alƙalan wasa mata ƙalilan a Najeriya.

Duk da cewa an samu ƙaruwar alƙalan wasa mata a Afirka a 'yan shekarun nan, har yanzu mata ba su da yawa a harkar alƙalancin wasa a Afirka da duniya baki ɗaya.

Zuwa 2023, mata 53 ne kawai ke cikin alƙalan wasa na hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya. Jerin ya ƙunshi mataimaka alƙalin wasa, da alƙalan wasan ƙwallon daɓe (futsal), amma hakan ma an samu ƙaruwa duk da haka idan aka kwatanta da shekarun baya.

Afirka ta Kudu da Moroko ne suka fi yawan alƙalan wasa mata da ke busa wasanni a babban mataki.

Alƙalan wasa mata kan fuskanci ƙalubale mai yawa a Najeriya da Afirka saboda al'adu da addinai.

Da ma can al'adu kan hana matan shiga wasanni musamman ma ƙwallon ƙafa.

Yusuf ta haɗu da Janny Sikazwe, wanda ya busa wasa a gasar Kofin Ƙasashen Afirka da ta Kofin Duniya a shekarar nan

Asalin hoton, Gbemisola Yusuf

Bayanan hoto, Gbemisola ta haɗu da Janny Sikazwe ɗan ƙasar Zimbabwe, wanda ya busa wasa a gasar Kofin Ƙasashen Afirka da ta Kofin Duniya a shekarar nan

Matashiyar da aka haifa a yankin Agege na jihar Legas, filin wasan da ke yankin muhimmin abu ne a rayuwarta da ma danginta.

Lokacin da take yarinya, takan je filin wasan tare da mahaifiyarta. Takan sayar da ruwa da lemo ga 'yanwasa, da kociyoyi, da ma 'yankallo.

A wannan lokacin ne sha'awar ƙwallon ƙafa ta shiga rayuwarta.

Bayan ta fara a matsayin 'yarwasa, Gbemisola ta koma alƙlancin wasa.

Wani mai gidanta mai suna Dele Atoun, tsohon lafari kuma sakataren majalisar alƙalan wasa ta Legas, kan tuna lokacin da ta fara wasa.

"Ta gina ƙwarin gwiwa a ranta duk da yadda take ganin ana kai wa alƙalan wasa hari, ana jifan su - amma kuma ta ga yadda suka yi nasara," in ji shi.

Cin zarafi

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Gbemisola ta fara alƙalancin wasa lokacin da take shekara 14 da haihuwa bayan ta shiga wani shrii da hukumar ƙwallon ƙafar Afirka Caf ta shirya domin zaƙulowa da kuma ba da horo ga matasa a alƙalancin wasa.

Sai dai hanyar da ta bi ba mai sauƙi ba ce musamman a Najeriya, saboda cin zarafi ta hanyar kalamai da ma yadda magoya baya kan kai wa alƙalan wasa da 'yanwasan hari.

Wani bincike da ƙungiyar alƙalan wasa ta Najeriya NRA ta gudanar ya nuna cewa kashi 80 na mutanen da suka ba da amsa sun ce sun fuskanci wani nau'i na cin zarafi a lokacin da suke alƙalancin wasa.

Gbemisola ta fuskanci irin wannan yanayin amma kuma hakan bai sanyaya mata gwiwa ba.

"Zan iya cewa alƙalancin wasa ne aiki mafi wahala a duniya," a cewarta.

"Za ka yanke hukunci a cikin 'yan daƙiƙoƙi, ko da kuwa ka yi daidai ko akasin haka."

Muhimmiyar damar da Gbemisola ta samu ita ce lokacin wani wasa a Legas tana 'yar shekara 18.

Alƙalan wasan ba su zo ba. 'Yan mintuna kafin lokacin take wasan, sai aka nemi Gbemisola - da ke taimaka wa mahaifiyarta sayar da ruwa a filin wasan - ta jagoranci wasan.

"Kusan ta yi komai daidai a wasan nan, kuma hakan ya ja hankalin mutane da yawa," in ji Atoun.

Dan da nan Gbemisola ta ɗaukaka, inda har ta yi busa a gasar firimiyar Najeriya ta mata.

Kaiwa wannan mataki ma na da nasa ƙalubalen, musamman ga mata.

Hari kan alƙalan wasa a Najeriya ba sabon abu ba ne, kuma yakan haɗa da zagi da ma kai hari.

A 2021, wasu 'yankallo sun kori wata alƙaliyar wasa yayin wani wasan hamayya, lamarin da ya jawo tir daga hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya da kuma kiraye-kirayen tsaurara tsaro yayin wasanni musamman kan mata alƙalan wasa.

Ya zuwa 2023, babu wata gasa a Najeriya da ta fara amfani da na'urar VAR mai taimaka wa alƙalin wasa. Hakan ya sa alƙalan wasan Najeriya ba su iya busa wasanni a wasannin duniya saboda na'urar.

Gbemisola ta ce idan har ta dage da ƙoƙari a aikinta, ba ta da wata fargaba.

"Nakan yi bakin ƙoƙarina kawai na bar wa Allah sauran," a cewarta.

'Mayyar filin wasa'

Gbemisola (ta uku daga dama) ta fara ne a matsayin 'yarwasa kafin ta zama alƙaliyar wasa

Asalin hoton, Gbemisola Yusuf

Bayanan hoto, Gbemisola (ta uku daga dama) ta fara ne a matsayin 'yarwasa kafin ta zama alƙaliyar wasa

A wajen Gbemisola, filin wasa na Agege ba wuri ba ne kawai, wata alama ce ta mafarin sana'arta.

Duk da cewa yanzu ta daina sayar da ruwa saboda Jami'ar Legas da take zuwa karatu, ba ta manta da wannan lokaci ba.

"Komai na rayuwata ya ta'allaƙa ne da filin wasa na Agege," in ji ta.

"A nan na samu ƙwarin gwiwar shiga aikin lafari, kuma yankin gaba ɗayansa ya taimaka sosai."

Tana cikin alƙalan wasan da suka busa gasar makarantu ta Afirka, inda ta shiga wasannin neman gurbi da kuma gasar kanta a Tanzania.

"Burina ne ya cika. Na ji daɗin yin hakan," kamar yadda ta bayyana.

"Zuwa ƙasashe da kuma tattaunawa da alƙalai daban-daban, da kuma koyon harsuna abubuwa ne da suka taimaka mani."

Iya magana da harsuna daban-daban kan taimaka wa alƙalin wasa wajen ƙarfafa ikonsa a cikin fili.

"Abu ne mai muhimmanci sosai saboda ban taɓa tsammanin zan haɗu da mutanen da na gani ba."

Shi ma mai gidanta Atou ya ce: "Ina alfahari da nasarorinta. "Labarinta mai ƙarfafa gwiwa ne da jajircewa."