Yanayin da Gaza za ta kasance bayan yaƙi

    • Marubuci, Catherine Heathwood
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 5

Shugaban Amurka Donald Trump ne ya tabbatar da kawo ƙarshen yaƙin Hamas da Isra'ila bayan amincewa da tsare-tsarensa guda 20.

Yarjejeniyar wadda aka sanar a ranar Alhamis za ta fara aiki ne da sako dukkan Isra'ilawa da Hamas ta yi garkuwa da su.

Za dai a yi musayar su da ɗaruruwan Falasɗinawa da ke gidajen yarin Isra'ila, sannan a janye sojojin Isra'ila da kuma isar da kayan agaji zuwa Zirin.

Sai dai har yanzu akwai wasu bayanai kan yadda za a gudanar da tsare-tsaren da ma jadawalin yadda za a aiwatar.

A ranar Talata ne aka yi shekara biyu cur da harin Hamas na ranar 7 ga Oktoban 2023 a Isra'ila, wanda ya yi ajalin mutum 1,200, sannan Hamas ta yi garkuwa da mutum 251.

Yanzu ne dai aka fara ɗabbaƙa somin-taɓin yarjejeniyar, kuma halin da Zirin Gaza za ta kasance a gaba na buƙatar ƙarin haske.

Wa zai jagoranci Gaza a ƙarƙashin tsare-tsaren Trump?

A tsare-tsaren Trump, za a kafa gwamnatin wucin-gadi da za ta ƙunshi wasu mutane da za a zaɓo daga Falasɗinawa, a ƙarƙashin kulawar kwamitin amintattu wanda Trump zai shugabanta, sannan kuma a ciki akwai tsohon Firaministan Birtaniya Tony Blair.

Daga bisani za a miƙa mulkin zuwa ga gwamnatin Falasɗinu bayan kwamitin ya kammala "gyare-gyarensa," kamar yaddaTrump ya nuna.

Haka kuma Hamas ba za ta kasance cikin masu ruwa da tsaki a gwamnatin Gaza ta kowane hali ba, a cewar yarjejeniyar.

Sannan tsare-tsaren sun nuna cewa za a yi wa ƴan Hamas afuwa idan sun miƙa wuya, ko kuma a ba su damar ficewa zuwa wata ƙasar da suke so.

A wane yanayi mutanen Gaza za su kasance?

Yarjejeniyar za ta fara aiki ne a cikin awa 24 bayan majalisar zartarwar Isra'ila ta amince, kamar yadda kakakin gwamnatin ƙasar ya bayyana a ranar Alhamis.

Hugh Lovatt, babban mai bincike ne a cibiyar nazarin diflomasiyyar ƙasashen waje ta Turai wato 'European Council on Foreign Relations' (ECFR) da ke Landan, ya ce a taƙaice yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin na "nufin ƴan Gaza sun daina fargabar rasa rayukansu."

"Abubuwa uku ne - su daina fargabar kisa da tursasa musu barin garuruwansu da ma fargabar faɗawa cikin yunwa. Waɗannan su ne abubuwa da suka fi muhimmanci a wajen mutanen Gaza," in ji shi a tattaunawarsa da BBC.

"Bayan sun koma gidajensu kuma sun tabbatar da tsaronsu, lokacin za su fara tunanin yadda za su inganta rayuwarsu," in ji Lovatt says.

Lallai mutanen Gaza suna cike da farin cikin samun labarin tsagaita yaƙin.

Jumaa Ramadan Abu Ammo, mazaunin Gaza ya bayyana wa BBC cewa, "abin da zan fara yi shi ne kwashe baraguzan da suka rufe gidanmu domin nemo gawarwakin kakannina biyu.

"Bayan nan sai mu fara yunƙurin sake gina gidan, da yardar Allah sai mun sake gina dukkan Gaza kuma za mu ci gaba da rayuwa sama da yadda muka yi a baya'', in ji shi.

Martanin sojojin Isra'ila bayan harin na 7 ga Oktoban a Gaza ya yi sanadiyar ɗaiɗaita gine-gien Gaza da tarwatsa ababen more rayuwarsu.

Yaƙin ya yi ajalin sama da Falasɗinawa 67,000, mafi yawansu fararen hula - ciki har da ƙananan yara sama da 18,000 kamar yadda ma'aikatar lafiyar Gaza ta bayyana.

Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran hukumomin duniya na amincewa da alƙaluman da ma'aikatar ta fitar.

Yaya batun kayan agaji?

Daga cikin tsare-tsaren Trump guda 20 akwai bayar da dama a shigar da agaji zuwa Gaza, Zirin da masana da suke da alaƙa da Majalisar Ɗinkin Duniya suka tabbatar akwai yunwa a watan Agusta.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito daga wani jami'in Isra'ila cewa za a ria shigar da manyan motocin kayan agaji 600 a kowace rana.

Haka kuka kafar ta ruwaito wata majiya daga Falasɗinu na cewa za a fara kai manyan motoci aƙalla 400 ne a kowace rana, sannan a riƙa ƙarawa a hankali a hankali.

Amma Mr Lovaty ya nanata cewa dole a samu walwalar da ƙungiyoyn agaji na duniya da za su samu sukunin shigar a agajin zuwa Gaza ba tare a fargaba ba.

Amma a cikin yarjejeniyar ta Trump, ba a ce komai ba kan gidauniyar agajin Gaza ta Gaza Humanitarian Foundation (GHF) mai cike da taƙaddama, wadda ta maye gurbin tsare-tsaren Majalisar Ɗinkin Duniya wajen rabon abinci.

Lovatt ya bayyana wa BBC cewa, "ya kamata a fayyace komai game da tsaron Zirin saboda yadda aka riƙa samun matsalar tsaro a kusa da cibiyoyin agaji bayan yarjejeniyar baya ta karye."

Shin yarjejeniyar za ta ɗore?

Wannan yarjejeniyar na cikin abubuwan farin ciki da aka gani tun farkon yaƙin a shekara biyu da suka gabata.

Amma tsare-tsaren Trump guda 20 daftari ne kawai na wasu ƴan shafuka, kamar yadda wakilin BBC a Jerusalem Tom Bennett ya bayyana.

Ya ce har yanzu akwai wasu abubuwa da suke buƙatar ƙarin bayani daga kowane ɓangare.

Daga ciki akwai buƙatar Isra'ila cewa dole a raba Hamas da makami, da kuma inda sojojin Isra'ila za su koma bayan janyewa da ma batun mulkin Gaza.

Mr Lovatt ya bayyana wa BBC cewa za a iya ɗabbaƙa tsarin na Trump, amma abin da zai biyo baya kuwa babu tabbas.

"Netanyahu ya ce sojojin Isra'ila ba za su janye baki ɗaya daga Gaza ba, kuma ba za a samar da ƴantacciyar ƙasar Falasɗinu ba, kamar yadda na nanata har a bayaninsa a fadar gwamnatin Amurka," in ji shi.

"Waɗannan wasu matsaloli ne guda biyu manya da za su yi wahalar samun cikakkiyar amincewar Falasɗinawa idan Isra'ila ba ta janye sojojinta daga Gaza ba," in ji shi.

Wace rawa Trump ya taka?

Babban abin da ya ja hankali a wannan yarjejeniyar shi ne rawar da Trump ya taka wajen matsa wa Hamas da Isra'ila su amince da yarjejeniyar, kamar yadda wakilin BBC a Jerusalem Hugo Bachega ya bayyana.

Idan har wannan yarjejeniyar ta tabbata, za ta zama babbar nasarar da Trump ya samu a harkokinsa na sanya baki a diflomasiyya a ƙasashen waje zuwa yanzu.

Ya sha bayyanawa a zahiri cewa yana da burin lashe kambun gwarzon zaman lafiya na duniya wato Nobel Peace Prize wadda ake bayarwa kowace ranar 10 ga Oktoba.

Mr Lovatt ya ce "Amurka ta kasance tana da rawar takawa game da diflomasiyar Isra'ia da Gabas ta Tsakiya musamman diflomasiyyar Isra'ila da Falasɗinu, sannan tana da iko - ko da ƙarami ne - wajen tanƙwara Israila."

Ana sa ran Trump zai isa Masar nan da wasu kwanaki domin ganawa da masu shiga tsakanin da ke aikin tsara yarjejeniya.