Bajintar Messi da mai yiwuwa ba za a taɓa kamo shi ba

Asalin hoton, Getty Images
Gwarzon ɗan ƙwallon duniya
Kyautar da ya lashe a baya-bayan nan, ta kasance batun bambance-bambancen ra'ayoyi, amma ba za a iya jayayya a kan cewa Lionel Messi na cikin manyan 'yan ƙwallon da tarihi da zai manta da su ba.
Ɗan wasan mai shekara 36, ya lashe kyautar Ballon d'Or karo na takwas - inda ya shiga gaban duk wani ɗan wasa da yawan guda uku - a ranar Litinin kuma ya ci gaba da kafa tarihin da ba za a taɓa kamo shi ba.
Messi ya jagoranci Argentina zuwa gasar Kofin Duniya a Qatar cikin watan Disamba, kafin ya kawo ƙarshen shekara 20 yana buga ƙwallon ƙafa a Turai, tare da Barcelona inda ya koma Inter Miami ta Amurka a watan Yuli.
Yayin da tauraronsa ke ci gaba da haskakawa - a kulob da kuma ƙasarsa - mun duba wasu daga cikin bajintar tarihi da Messi ya kafa a tsawon shekaru.
Mafi cin kyautar Ballon d'Or - takwas
Ba abin mamaki ba ne lokacin da aka bayyana Messi a matsayin wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or ta maza, kyautar gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafa a duniya na kakar 2022-23.
Babban rawar da ya taka wajen taimakawa Argentina ta lashe gasar cin kofin duniya a karon farko tun 1986, kusan ya ba da tabbacin zai tsawaita tarihin lashe kyautar zuwa takwas - duk da ƙoƙarin da ɗan wasan Manchester City Erling Haaland ya yi.
Cristiano Ronaldo, wanda yanzu haka yake buga wasa a Saudiyya, shi ne abokin hamayyar Messi na kusa inda yake da guda biyar, amma yana da shekara 38 kuma ba a tantance shi ba a cikin ‘yan wasa 30 da za su iya lashe kyautar a bana.
Da wuya ne ɗan wasan na kasar Portugal ya iya kalubalantar tarihin da Messi ya kafa.
Haka ne irin nasarar da Messi da Ronaldo suka yi a Ballon d'Or, sauran 'yan wasa biyun da suka ci kyautar a baya wadanda har yanzu suna buga kwallo su ne Luka Modric na Croatia da Karim Benzema na Faransa.
Yayin da dukansu sun kai shekara 30, ba su da damar isa ko kusa da yawan lambobin Messi.
Erling Haaland da ɗan wasan tsakiya na Real Madrid da Ingila Jude Bellingham da ɗan wasan Real daga kasar Brazil Vinicius Jr har ma da ɗan wasan Bayern Munich da Ingila Harry Kane za su yi sha'awar samun damar kasancewa zakaru a nan gaba.
Ko da yake , za a daɗe kafin a samu wanda zai kama kafar Messi.
Mafi ƙwallaye a La Liga - 50
Ba zai yiwu a faɗi lokacin da za a iya zarce wannan gagarumar bajinta zura ƙwallo a raga ba, amma tarihi ya nuna cewa ana iya ɗaukan tsawon lokaci.
Kwallo 50 da Messi ya ci a Barcelona a wasa 37 da ya buga a 2011-12 ba tarihin La Liga kaɗai ba ne, shi ne mafi yawa a kakar wasa guda, a ɗaya daga cikin manyan gasannin lig-lig guda biyar na Turai tun lokacin da aka kafa gasar Premier a 1992-93.
Shekarar da aka fara buga gasar La Liga a 1929, 'yan wasa uku ne kawai suka ci ƙwallo 40.
Messi da Cristiano Ronaldo sun yi hakan sau biyu, kuma Luis Suarez ya yi haka shekara bakwai a baya - karo na ƙarshe da aka kai wannan matakin.
Mafi cin ƙwallaye a duk gasar kakar wasa - 73
Wannan adadi ne wanda da alama ba za a iya kamo Messi ba.
A kakar wasa ta 2011-12, Messi ya ci wa Barcelona ƙwallaye 73, adadi mafi yawa a duk wata gasa kuma babu wanda ya samu ko kusa da yin haka tun daga lokacin.
Haaland ya karya kowane irin tarihi a kakar wasansa ta farko a Premier bara, amma, duk da yana zura ƙwallo a kowane mako, ya kammala kakar wasan da ƙwallo 52 - 21 ƙasa da ƙasaitacciyar bajintar Messi.
Ko shahararren ɗan wasan Everton Dixie Dean ya gaza da ƙwallo 10, inda ya zura ƙwallo 63, abu mai ban mamaki a kakar wasan 1927-28 - tarihin gasar Ingila wanda ya kasance na tsawon shekara 95.
Mafi yawan ƙwallaye a Champions league a kulob ɗaya - 120
Messi ya ɗan gaza a tarihin ɗan wasan da ya fi zura ƙwallaye a gasar zakarun Turai.
Shi ne a matsayi na biyu – da ƙwallo 11, bayan Cristiano Ronaldo wanda ya ci ƙwallo 140 – kuma dukkansu biyu sun buga wasansu na ƙarshe a gasar.
Sai dai ƙwallo 120 da Messi ya ci wa Barcelona, ta sanya shi zama ɗan wasa mafi yawan zura ƙwallaye a kulob ɗaya na gasar.
Ronaldo ya ci wa Real Madrid ƙwallo 105 a matsayi na biyu, yayin da Karim Benzema ya ci wa Real ƙwallo 78, a matsayi na uku.
Da yake abu ne mai matuƙar wahala, 'yan wasa su kasance masu alƙawari ga kulob ɗaya a zamanin nan, da wuya a ga wanda zai iya kwatanta abin da Messi ya yi nan da shekaru masu zuwa.
Mafi yawan ƙwallaye a Argentina - 106
Messi ne ɗan wasan Argentina da ya kafa tarihin zura ƙwallaye a raga ga ƙasar Argentina - kuma yana ci gaba da tafiya.
A tarihin wasansa a Argentina da ya fara a 2005, ya zura ƙwallo 48 fiye da Gabriel Batistuta, a matsayi na biyu, ya kuma fi wanda ke mataki na uku Sergio Aguero da ƙwallo 63
Yayin da har yanzu Messi yake ci gaba da cin ƙwallaye ga ƙasar, kuma ganin cewa abokan hamayyarsa biyu sun yi ritaya, zai ɗauki lokaci mai tsawo kafin wani ya kama ƙafar tarihin Messi a Argentina.











