Chelsea za ta dauki Potter domin maye gurbin Tuchel

Chelsea za ta tattauna da kociyan Brighton, Graham Potter domin ya maye gurbin Thomas Tuchel.

Ranar Laraba Chelsea ta kori Tuchel, wanda ya lashe kofi uku a wata 20 a Stamford Bridge.

Tuni Brighton ta bai wa Potter mai shekara 47, tsohon kociyan Swansea da Ostersunds izinin tattaunawa da Chelsea ko za su iya kulla yarjejeniya.

An kori Tuchel bayan da ya kasa samun kwarin gwiwa daga ‘yan wasan Chelsea da sabon shugaban kungiyar, wanda ya mallaka a watan Mayu.

Potter, wanda ake hangin zai karbi aikin horar da tawagar Ingila nan gaba, na jan ragamar Brighton wadda ke mataki na hudu a teburin bana.

Kociyan ya yi nasara a wasa hudu da canjaras daya a wasa shida a Premier League ta kakar nan.

An nada Potter mai horar da Brighton a cikin watan Mayun 2019, ya kuma kai kungiyar mataki na 15 da na 16 da na tara a kaka ukun da ya horar da ita.

Sai dai salon wasan da yake horarwa da yadda kungiya ke kai hare-hare da taka-leda mai ban sha’awa ya sa kungiyoyi da dama ke ganin zai zama fitatce nan gaba.

Sabon wanda ya sayi Chelsea ya kasha £255.3m wajen sayo yan kwallo takwas a bana.

Kungiyar Stamford Bridge tana ta shida a teburin Premier League da cin kwallo uku da canjaras da rashin nasara a karawa biyu a lokacin da aka kori Tuchel.

Ranar Talata Chelsea ta yi rashin nasara a gidan Dinamo Zagreb da ci 1-0 a wasan farko a Champions League karawar cikin rukuni da ta buga.