Nau'o'in cutar kansa da yadda take yaɗuwa a jikin ɗan'adam

Josephine Namwanjje (R), 28, checks the legs of his brother Jonathan Luzige, a colon cancer patient, at their home in Nabbingo, on June 26, 2025. Hospice Africa Uganda (HAU),

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Dr. Dilip Nikam
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Oncologist, Bombay Hospital, Mumbai
  • Lokacin karatu: Minti 4

Da zarar mutum ya ji sunan kansa, abin da ke faruwa zuwa zuciya shi ne fargaba ba ga masu ɗauke da cutar da yan uwansu kaɗai ba, har ma ga likitoci da masu bincike.

An fara ambato batun kansa ne tun zamanin rubuce-rubucen Girka da kuma takardun Romawa.

Bayan gwaje-gwaje da masu bincike suka yi a lokacin, sun gano cewa masu cutar na ɗauke da kumburi a jikinsu kuma tana yaɗuwa daga sassa zuwa sassa na jiki. Sun ce raɗaɗin da masu ciwon ke ji ba ya misaltuwa.

Akwai dalilai da dama da masana suka bayyana cewa suna haifar da cuttukan kansa a sassan jikin ɗan'adam, da suka hada da shan taba sigari, cin abinci maras kyau, har ma da rashin motsa jiki.

Amma kuma sun ce yakan dauki shekaru da dama kafin wadannan abubuwa su haifar da cutar ta kansa.

Ta yaya kansa ke yaɗuwa a jiki?

Kansa.

Asalin hoton, Getty Images

Kansa dai na yaɗuwa ne daga sassa zuwa sassa na jiki, a cewar masana.

Jikin ɗan'adam yana ɗauke da biliyoyin ƙwayan halitta. Jijiyoyi da dama ne suka haɗu suka samar da sasan jiki.

Ƙwayoyin kansa ba sa mutuwa da wuri, suna ƙauracewa garkuwar jiki sannan su yaɗu daga sassa zuwa sassa. A can ne suke yi wa ƙwayoyin halitta lahani da kuma jiki. Abu ne mawuyaci a ƙauce wa hakan.

Sai dai, ba kowane kumburi a jiki ne yake da alaƙa da kansa ba. Wasu lokuta, ana samun kumburi haka nan.

Waɗanne irin nau'ukan yaɗuwar kansa muke da shi?

Cutar kansa.

Asalin hoton, Getty Images

Akewai na'u'oin yaɗuwar kansa da muke da shu guda uku. Sun haɗa da:

Yaɗuwar kai-tsaye: Ƙwayoyin kansa na yaɗuwa kai-tsaye inda suke cin ƙarfin ƙwayoyin halitta da kuma sassan jiki.

Yaɗuwa ta hanyar kumburi: Ƙwayoyin cutar kansa na shiga cikin jiki, inda suke riƙiɗewa su zama kumburi sannan su yi jiki illa.

Yaɗuwa ta hanyar jini: Kansa na yaɗuwa ta hanyar jijiyoyin jini zuwa huhu, sannan ya zarce zuwa ƙasusuwa da hanta da kuma ƙwakwalwa.

Zanen mutum.

Asalin hoton, Getty Images

Nau'o'in cutar kansa

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kansar bakin mahaifa: Kansar bakin mahaifa kan tsiro ne a bakin mahifar mata. Kuma takan fi shafar matan da ke kan ganiyarsu, wato daga shekara 30 zuwa 45. Masana sun ce yawancin matsalolin cutar kansar bakin mahaifa na faruwa ne sakamkon kamuwa da nau'in kwayar cutar da ake kira HPV, wacce galibi kan yadu ta hanyar ko wace irin mu'amalar jima'i tsakanin mace da namiji. Amma kuma akwai irin nau'ukan wannan kwayar cuta ta HPv guda 100 da akasari ba su da hadari. Sai dai wasu nau'ukan sukan haddasa wasu sauye-sauye a cikin kwayoyin halittar bakin mahaifar da ka iya haifar da cutar kansar.

Kansar mama: Galibi an fi samun cutar kansar mama a tsakanin mata kamar yadda bincike ya nuna, kuma an fi samu galibi daga matan da shekarunsu suka kama daga 50 zuwa sama.

Amma kuma akwai yiwuwar warkewa idan aka gano cutar da wuri, in ji kwararru.

Don haka yake da matukar muhimmaci mata su rika zuwa ganin likita akai-akai ana duba lafiyarsu don gano idan akwai wasu sauye-sauye a jikin maman nasu.

Akan samu cutar kansar mama a tsakanin maza, amma ba kasafai ba.

Kansar huhu: Cutar kasar huhu nau'in kansa ce da aka fi yawan samu a fadin duniya.

A Amurka kansar huhun ita ce kan gaba wajen haddasa asarar rayuka.

An kuma fi danganta shan taba sigari wajen haifar da cutar, amma kuma za ta iya kama wadanda ba sa shan taba sigarin.

Kansar kwakwalwa: Kansar kwakwalwa kan faru ne a lokacin da kwayoyin halittar kansar suka yadu fiye da kima ta yadda ba za a iya dakatar da su ba.

Nau'ukan irin wannan cuta sun danganta ne ga yanayin yadda suke sake saurin yaduwa bayan yi wa wanda ya kamu magani.

Don haka akwai nau'uka masu saurin yaduwa da kuma wadanda ba su da karfin saurin yaduwar.

Kansar kwakwalwa kan shafi ko wadanne mutane- babu babba babu yaro, duk da cewa an fi samu a tsakanin wadanda suka manyanta.

Kansar mafitsara: Masana sun bayyana cewa galibi wadanda suka fi shiga hadarin kamuwa da cutar kansar mafitsara maza ne.

Akan kuma samu namiji daya cikin tara da ke kamuwa da cutar, amma kuma mutum daya kadai cikin 39 kan mutu da cutar.

Kusan kashi 80 bisa dari na mazan da suka kai shekara 80 na da kwayoyin halittar kansar a mafitsararsu.

Bayan kasancewa maza, akwai wasu dalilai da kan haifatr da cutar ta kansar mafitsara.

Akwai dalilai kamar na shekaru, da yanayin abinci, da kiba da tarihin cutar daga cikin dangi, da kuma yadda mutum yake tafiyar da rayuwarsa.