'Na yi nadamar shiga aikin ɗansanda'

Retired police officers dey protest
Lokacin karatu: Minti 4

Ƴansanda da suka yi ritaya na gudanar da zanga-zanga a Abuja babban birnin Najeriya kan yadda suka ce ana ba su abin da bai taka kara ya karya ba a matsayin fansho da kuma giratuti.

Tsoffin ƴansandan daga sassa daban-daban na Najeriya na gudanar da zanga-zangar ne a Abuja, buƙatarsu ita ce a tsame su daga tsarin fansho na 'karo-karo."

"Idan da gaske ne tsarin na da kyau, me ya sa sufetan ƴansanda da mataimakansa da kwamishinonin ƴansanda ba sa ciki? In ji Iliyasu Aliyu, ɗaya daga cikin jagororin masu zanga-zangar.

Iyasu ya ƙara da cewa ya yi ritaya bayan kwashe shekara 35 yana bauta wa ƙasa amma a ƙarshe naira miliyan 2.5 kacal aka biya shi a matsayin giratuti, sannan ake ba shi naira 40,000 duk wata a matsayin fansho.

"Mene ne wannan kudin zai wa mutum?" In ji Ilyasu.

 Ilyasu Yahaya Aliyu
Bayanan hoto, Ilyasu Yahaya Aliyu, ya shaida wa BBC cewa ya yi ritaya yana da shekara 35 amma naira miliyan 2.5 kawai aka biya shi giratuti

BBC tattauna da masu zanga-zangar da dama, ciki har da wata mata da ta yi ritaya a matsayin Sufeta, wadda ta kwashe sama da shekara biyu bayan yin ritaya kafin aka biya ta giratuti naira miliyan 1.4. Daga nan kuma sai aka riƙa biyan ta fansho naira 22,000 a kowane wata.

"Na yi da na sanin shiga aikin ɗansanda," kamar yadda ta shaida wa ƴan jarida.

"Na yi nadamar kwashe shekara 35 na rayuwata ina bauta wa wannan ƙasar. Kalle ni a yanzu, wane aiki zan iya yi?"

Matar, wadda ta ce yanzu ta haura shekara 60 a duniya kuma mijinta ya rasu, ta ce ita kaɗai take kula da yaransu, inda yanzu ƴar autarta take karatu a wata jami'ar jiha.

"Kuɗin gidan da take zama a kowace shekara naira 200,000 ne, shekara nawa zan kwashe ina tara kuɗin da ake biyana kafin na iya biya mata haya?" In ji ta.

Kalli abubuwan da ke faruwa
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon zanga-zangar tsofaffain ƴansanda a Abuja ranar 21 ga watan Yulin 2025

Masu zanga-zangar sun fara ne daga ƙofar shiga Majalisar Dokokin Tarayya da ke Abuja inda suke neman ƴan majalisar su amince da dokar da za ta cire su daga tsarin fansho na karo-karo, sai dai babu wani jami'in majalisar da ya fito domin jin ƙorafinsu.

Daga bisani, ɗan gwagwarwamayr nan na Najeriya, Omoyele Sowore ya jagoranci masu zanga-zangar zuwa babban ofishin ƴansandan Najeriya da ke Abuja.

Masu zanga-zangar na ɗauke da kwalaye ɗauke da rubuce-rubuce kamar: "Sufeta Janar ka biya ƴansanda, Tinubu ka biya ƴansanda".

Sai dai an jibge tarin jami'an ƴansanda a kan titi cikin shirin ko-ta-kwana, amma ba su far wa kowa ba.

Sai dai ƴansandan sun riƙa nuna wa masu zanga-zangar yadda za su yi jerin-gwanon ta yadda ba za su haifar da cunkoson ababen hawa ba.

Retired police officers dey protest

Ɗaya daga cikin lauyoyin masu zanga-zangar, Deji Adeyanju ya shaida wa ƴan jarida cewa ya kamata a mutunta jami'an ƴansandan da suka shafe shekara 35 suna hidimta wa ƙasa a maimakon ba su giratutin naira miliyan biyu da fanshon naira 30,000 wata-wata.

"Ƴan majalisa waɗanda ke aiki na shekara huɗu kacal na karbar miliyoyin kuɗaɗe a lokacin da suke majalisa sannan kuma idan za su tafi a ba su abin da ya fi haka. To me zai sa a riƙa bai wa ƴansandan da suka yi ritaya abin da bai taka kara ya karya ba?"

"Ko shugaban ƙasa da ya rasu kwanan-nan, Najeriya ce ke kula da shi har ya mutu, me ya sa za a riƙa yin watsi da jami'an ƴansanda? Me hakan ke nunawa ga waɗanda ke cikin aiki a yanzu?" In ji Adeyanju.

'Na shiga aikin ina jin daɗi amma kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba'

DSP Godwin Tom
Bayanan hoto, Godwin Tom, ya yi ritaya a matsayin mataimakin Sufetan Ƴansanda (DSP)

Godwin Tom, wanda ya yi ritaya a matsayin mataimakin sufuritandan ƴansanda (DSP) ya bayyana yadda ya shiga aikin ɗansanda cikin karsashi da ƙuruciyarsa.

"Lokacin na kammala karatuna nan digiri ke nan a jami'ar Ado Ekiti da sakamako mai kyau. Shekaruna 19 a lokacin," in ji shi.

"Ina jin dadi a lokacin, kuma na yi amfani da duk ƙarfina wajen yi wa Najeriya aiki. Tarihin aikina da na yi babu gazawa, duk wani horo da na je a gaba nake."

Sai dai ya ce a aikin da ya yi wa ƙasa, kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba.

"Bai kamata ma na ajiye aiki a matsayin DSP ba. Na yi shekara 11 a muƙami ɗaya - saje, sai kuma na ƙara yin shekara shida a muƙamin sufeta. Duk kuwa da kyawun takarduna na karatu," in ji shi.