Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan APC ne kan gaba wajen neman tsige shugaban kasa a majalisa, in ji Shekarau
Tsohon gwamnan Kano kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Sanata Ibrahim Shekarau, ya ce ɓangaren rinjaye a majalisar dattijan Najeriya ce ta soma gabatar da batun neman a tsige shugaban kasa, Muhammadu Buhari, muddin bai ɗau matakin kawo ƙarshen matsalolin tsaro ba.
Sanata Shekarau wanda mamba ne a kwamitin tsaro na majalisar dattijan Najeriya ya shaida hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da BBC.
Sanatan ya ce a lokacin zaman da majalisar ta yi kan halin da Najeriya ke ciki na taɓarɓarewar tsaro an shafe sama da sa’a uku ana dambarwa, kowa na tsokaci da kawo nasa ra’ayi, har aka kai ga matsayin neman a tura takardar tsigewa zuwa ga shugaba, Muhammadu Buhari bayan ba shi wa’adi.
Wannan batu na tsige Buhari kan matsalar taɓarɓarewar tsaro ya jawo yamutsi a zauren majalisar dattawan sakamakon zazzafar muhawarar da 'yan majalisar suka yi a tsakaninsu.
End of Wasu labaran da za ku so karantawa
‘Batun Tsigewa daga Wajen ɗan APC ya fito’
Malam Ibrahim Shekaru ya ce ba zai ambaci suna ba, amma dai mutum na farko da ya soma gabatar da wannan batu na neman tsige shugaba Buhari a majalisa ɗan APC ne, haka zalika mutum na biyu da ya goyi-bayansa kafin sauran mutane shi ma ɗan APCn ne.
Ya ce “Ba zan soma kama sunan kowa ba amma wallahi ina tabbatar ma ka cewa wanda ya soma tashi ya ce a rubutawa shugaban ƙasa takardar tsigewa wallahi ɗan APC ne, wanda ya goyi-bayansa ma wallahi ɗan APC.
“Wannan zama ne na ɗaki da zama ne na zauren majalisa da kowa ya shaida, har da ‘yan jarida. Ina son mutane su san cewa maganar kalmar a tsige shugaban ƙasa daga wajen APC ta fito ba ɓangaren masu hamayya ba, su suka faɗi abin su.”
Abin da ya sa ɓangaren hamayya ficewa daga majalisa
Sanata Ibrahim Shekarau ya ce tunda ba kuri’a aka jefa ba, shugaban majalisa na da damar aunawa ya ga wani ra’ayi ne yafi rinjaye kafin a yanke hukunci, to bayan zaman ne shugaban majalisa ya shaidawa al’umma abubuwan da aka tattauna.
Sai dai a cewar Shekarau, a wajen bayyani sai shugaban majalisa ya shaida matsayin bai wa shugaba Buhari wa’adin mako shida, amma kuma bai kara wani abu ba.
To hakan ne ya sa shi kuma shugaban marasa rinjaye ya mike, ya shaida cewa shugaban majalisa ya yi ƙwange domin akwai abin da bai ambato ba.
Wannan dalili ne a cewar Shekarau, ya sa shugaban marasa rinjaye ya nunawa shugaban majalisa cewa ya saɓa doka saboda bai faɗamasa abin da zai faɗa ba, nan take kuma ya ja hankalin sauran marasa rinjaye suka fice daga zaman.
“Bangaren marassa rinjaye sun ce ya kamata a sanya batun tsige shugaban kasar a cikin kudirin, amma shugaban majalisar bai yi haka ba. Wannan ne ya sa suka fice daga zauren a fusace”, in ji Shekarau.
Sanata Shekarau ya ce dama dimokuradiya ta gaji kalubale, don haka shi a ganinsa bai kamata mutum ya tsaya yana surutai kan tada kura ko rigima ba, domin neman gyara ba wai ya na nufin a yi rigima ba ne.
‘Tsaron Najeriya ya taɓarɓare fa’
Sanata Shekarau ya ce kuskure ne ma a ce mutum ya ce shugaban kasa ba ya hoɓɓasa, sai dai har yanzu akwai jan aiki da gyara wanda dole ba za a kau da kai ba.
Saboda harkar tsaro a Najeriya ta taɓarɓare kuma abu ne da kowa ya shaida.
Ya ce a zamansa na shekara uku a majalisa kowa ya shaida cewa kullum ana cikin zaman jajantawa, amma abubuwa sun gaggara sauki, in ji Shekarau.
“Saboda a zamana na shekaru uku a majalisa duk abin da aka bukata wanda ke da alaƙa da kuɗi an bayar, don haka babu batun rashin kuɗi ko wani ƙwange”.
Mal Shekarau ya ce kullum magana guda ake yi, ga shi hukumar tsaro ta DSS ta fitar da bayanan sirri cewa mutane su sake lura saboda Abuja na cikin fargaba.
“Kafin wannan lokaci an kai hari Kuje, an kuma budewa rundunar fadar shugaban kasa wuta a Bwari.
Wadanan su ne abubuwan da suka sa aka yi zama a ranar Larabar da ta gabata, sama da mutum 50 ne suka magantu, ana neman mafita da kawo shawarwari.
Har aka kai ga matsayar rubuta kudiri ga shugaban kasa na tuni kan shawarwari tsaro da aka yi a 2020, sannan kowa ya yi amannar cewa babu shaidar cewa an yi amfani da wannan kudiri da shawara ta majalisa."
"Sannan wasu ‘yan majalisa na cewa wannan ba zai wadatar ba, don haka a ba da wa’adi, anan ne aka tsayar da sati shida bayan dogon muhawara.
Sai dai wasu sun zo da shawarar cewa bayan wata shida inda babu wata gamsashiyar shaida a kasa to a aike takardar tsigewa ko kuma a ce zaa dau mataki, in ji Shekarau.