Ba a ɗauka ta da muhimmanci duk da ƙwallayen da nake ci - Harry Kane

Harry Kane

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Kane ya ci wa Ingila ƙwallaye 69 da kuma 76 a Bayern Munich
Lokacin karatu: Minti 1

Kyaftin ɗin Ingila Harry Kane ya ce yana ganin kamar "ba a ɗaukar sa da muhimmanci" kuma ma mutane sun fara gajiya da yawan kafa tarihi da yake yi a cin ƙwallaye.

Ɗanƙwallon na Bayern Munich mai shekara 31, shi ne kan gaba a yawan ci wa Ingila ƙwallaye kuma yana sa ran ƙarawa kan 69 da ya ci jimilla a ranar Juma'a yayin wasa da Albania.

Sai dai duk da yawan ƙwallayen nasa a Ingila, Kane na shan suka daga wasu kafofin yaɗa labarai na Jamus game da salon wasansa a Bayern ɗin, inda ya ci ƙwallo 76 a wasa 82.

"Kamar lokacin da Ronaldo da Messi ke cin ƙwallaye na fitar hankali, za su ci 50 a wata kaka sai kuma su ci 40 a kaka ta gaba amma sai a ce ba su yi ƙoƙari ba," in ji Kane.

"Mutane ba su ɗaukar abin da muhimmanci har a nan Ingila. Na ci ƙwallaye 69, amma idan na ci Albania ko Latvia sai mutane su dinga nuna kamar da ma sun san hakan za ta faru, sai ka ga ba a maganar waɗannan wasannin.

"Da a ce shekarata 25 kuma nake yin abin da nake yi a yanzu, da murnar da mutane za su dinga nunawa ta sha bamban. Matsalar ƙwallon ƙafa kenan. Na ga abin da ya faru da wasu 'yanwasan bayan sun haura shekara 30.

"Ƙila mutane kan gaji da abin da kake yi, amma tabbas ni ban gaji ba. Ina farin ciki da irin waɗannan wasannin da wasu ma masu zuwa."