Manyan hafsoshin sojin Ecowas za su gana don tsara shirin tunkarar Nijar

Manyan hafsoshin sojin Afirka ta Yamma za su gudanar da taro a 'yan kwanaki masu zuwa don tsara shirye-shirye kan yiwuwar amfani da ƙarfin soja, yayin da ƙasashen duniya ke ƙara nuna fargaba game da yanayin da ake tsare da hamɓararren Shugaba Bazoum Mohamed.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce taron manyan hafsoshin sojin na nuna cewa ƙasashen Afirka ta Yamma suna gaggauta shirye-shiryen tura sojoji da yiwuwar ɗaukar matakin kawar da masu juyin mulki a Nijar.

"Ana tsara yin wani (taron) a makon gobe," Reuters ya ambato wani mai magana da yawun Ecowas yana cewa.

Wani jami'in gwamnatin Najeriya da kuma wata majiyar sojojin Kwatdebuwa sun ce za a yi taron ne ranar Asabar a Ghana.

Zuwa yanzu babu masaniya ƙarara kan yadda girman rundunar zai kasance, da tsawon lokacin da za a shafe kafin a iya tattaro dakarun, da kuma idan haƙiƙa rundunar za ta auka don yin mamaye.

Ƙungiyar Ecowas dai ta ce har yanzu duk ƙofofi a buɗe suke kuma tana fatan za a iya cimma masalaha cikin lumana. Masu sharhi kan al'amuran tsaro kuma sun ce dakarun Ecowas na iya kwashe tsawon makonni ko fiye da haka, kafin su haɗu, abin da mai yiwuwa zai ba da dama ga ƙoƙarin tattaunawa.

Kwatdebuwa ce kaɗai ƙasar da ya zuwa yanzu ta bayyana adadin dakarun da za ta aika. Shugaba Alassane Ouattara ya yi alƙawari a ranar Alhamis cewa ƙasarsa za ta aika wata bataliyar sojoji da ta kai yawan mutum 850 - 1,100.

Hamɓarar da gwamnatin Mohamed Bazoum ya kasance juyin mulki na bakwai a Yammaci da Tsakiyar Afirka cikin shekara uku, abin da kuma ya ƙara jefa yankin cikin tunzuri, baya ga hare-haren masu iƙirarin jihadi da yake fama da su tsawon lokaci.

Ana nuna ƙarin damuwa ga halin da Bazoum ke ciki

Kungiyar Tarayyar Afrika a ranar Juma'a ta nuna damuwa kan rahotanni game da halin da ake tsare da Shugaba Bazoum, inda ta ce ba za ta lamunci ci gaba da tsarewar da sojoji ke yi masa ba.

"Ci gaba da tsare zaɓaɓɓen shugaban ƙasa wanda aka zaɓa ta hanyar doka, abu ne da ba za mu amince da shi ba," cewar wata sanarwa da shugaban Hukumar Tarayyar Afirka, Moussa Faki Mahamat ya fitar.

Da yake zantawa da manema labarai ranar Alhamis, Shugaba Alassane Ouattara ya ce "Tsare Bazoum tamkar ta'addanci ne, kuma na yi alƙawarin bayar da gudunmawar dakaru".

Kungiyar Kare Hakkin Ɗan'adam ta Human Rights Watch, ta ce ta zanta da Shugaba Bazoum a wannan mako, kuma yana ci gaba da kasancewa a tsare tare da matarsa da kuma ɗansa, ya ce kuma lafiyar iyalinsa tana cikin garari.

"Ɗana ba shi da lafiya, yana fama da ciwon zuciya, kuma yana buƙatar ganin likita," Kamar yadda ƙungiyar ta ruwaito Bazoum yana cewa. "Sun ƙi barinsa ya samu ganin likita ko magani."

Ya kuma faɗa wa ƙungiyar cewa rabon sa da wutar lantarki tun ranar 2 ga watan Agusta, kuma an ƙi bari ya ga iyalansa da abokansa waɗansa ke son kawo masa taimako.

Ita ma, Tarayyar Turai ta ce halin da ake tsare da Bazoum Mohamed na ci gaba da taɓarɓarewa, kuma ta yi kira saki hamɓararren shugaban cikin gaggawa.

Wata sanarwa da jami'in EU kan manufofin hulɗa da ƙasashen waje, Josep Borrell ya fitar, ta ce ita da Majalisar Ɗinkin Duniya sun damu matuƙa a kan halin da Bazoum ke ciki bayan tattaunawa da shi ta wayar tarho ranar Laraba.

"Mun damu game da halin lafiyar Bazoum da kuma ta iyalansa. Ba mu da tabbaci a kan irin tsaron da aka ba su," in ji EU.

Hamɓararren shugaban ƙasar dai na tsare a gidansa da ke fadar shugaban ƙasa cikin Yamai, babban birnin Nijar tun bayan kifar da shi daga kan mulki.

Amurka da Faransa na goyon baya ga Ecowas

Faransa da Amurka dai sun bayyana goyon bayansu ga dukkan shawarwari da taron Ecowas na ranar Alhamis ya cimma, wanda ya amince da buƙatar tura sojoji zuwa Nijar.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter, ma'aikatar harkokin wajen Faransa, ta ƙara nanata adawa da juyin mulki a Nijar da kuma tsare Shugaba Bazoum.

Ita ma Amurka ta bakin Sakataren Wajenta, Anthony Blinken, ta ce "Gwamnatin Washington na goyon bayan duk wani mataki da Ecowas za ta ɗauka don ganin an dawo da tsarin dimokraɗiyya Nijar".

Ta kuma ce za ta ɗora alhakin duk abin da ya faru ga lafiyar Bazoum da kuma iyalansa a kan sojojin.

Nijar, na ɗaya daga cikin ƙasashe mafi talauci a duniya, kuma ba ta kusa da teku. Girmanta ya kai misalin faɗin Faransa biyu, ita ce ƙasa ta bakwai a duniya da ke samar da makamashin uranium, wani muhimmin sinadari da ake amfani da shi wajen sarrafa makamashin nukiliya da kuma haɗa magungunan cutar daji ko kansa.

Kafin juyin mulkin, Nijar ta kasance abokiyar ƙawance ga Ƙasashen Yamma, amma yanzu ta juya wa uwargijiyarta Faransa baya inda take yunƙurin ƙulla alaƙa da Rasha.

Akwai dakarun Amurka da Faransa da Jamus da kuma na Italiya a Nijar, a matsayin wani ɓangare na yaƙi da masu iƙirarin jihadi da ya bazu a faɗin yanki Sahel.